💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕💕
💕💕💕💕💕
💕💕💕💕
💕💕💕
💕💕
💕
United Arab Emirate
Kwana biyu kenan da zuwansu umma dubai babu abinda suke sai siyayya,ayanxu haka sun hada akwati biyar,saura biyu shima sai gobe don sun gaji dayawa.
Suna isa hotel din da suka sauka suka yi ordering abinci kafin suka wuce daki,suna isa suka yi wanka kafin suka fito don yi lunch mintina bai wuce goma ba aka kawo musu abinda suka bukata,umma na gani ta karba ta ajiye a center table,bude nata tayi ta fara ci ko kallon mukhtar bata yi ba,dariya yayi sannan shima ya sauko ya fara cin nashi,sai da ta kusa koshi sannan ta dago kai,ta kalli mukhtar sannan tace amma abincin nan da dadi fah,dariya mukhtar yayi sannan yace yunwar neh haka,turo baki tayi sannan tacigaba da cin abincinta,dariya ya kuma yi sannan yace wai haushi kika ji,girgiza kanta tayi kawai bata dago ba,better don gani nayi gaskiya na fada saboda nigerian jollof kike ci ba wani hamshakin abinci bane,ana cikin haka saleem ya shigo tare da rushd suna dariya sannan suka yi sallama,mukhtar nai kadai ya iya amsawa,ita umma sha jinin jikinta tayi da ta gansa,don da tasan tare zasu shigo da ta bar falon,tun jiya take avoiding dinshi,tana jin lokacin da yake ce ma ya mukhtar da agidansu suka sauka amma yace kar ya damu akwai next time,karfin halin sai saita kanta tayi kokarin yi,daga nan ta daga kai suka hada ido,farko haduwarsu kenan face to face,kare mai kallo tayi,fari neh tas,kana ganinsa kaga balarabe,gashin kanshi baki wuluk neh,yana da yalwataccen gashin gira da ido dogaye,bakinshi jajur kamar ya sanya jan baki,hancinsa pointed neh am ba sosai ba,yana da built up body,fatar jikin shi ya nuna alamon hutu atattare da shi, farin jallabiyace jikinsa,bazaka taba tsamanin yana da hadi da yan nigeria ba,murmushi ya sakar mata wanda ya sa ta kusa rikicewa amma dayeke kar ta san kar ne,ita ma murmushi ta mayar me sannan ta mike tana tattara kayan da suka yi amfani dashi don saka shi cikin waste bin,kallo ya bita da shi sannan ya raya azuciyarsa,wai daman haka take,gaskiya camera akwai karya,she is so sexy n cute ya fada axuciyarsa.Match suka kunna na gulf wanda ake bugawa,fitowa daga kicin tayi zata wuce daki ta hango suna kallon match din gulf and bazata iya missing dinshi ba domin best game dinta kenan,karasowa falon tayi ta zauna kujerar da saleem yake zaune shi da mukhtar,tsakiyarsu ta zauna sannan ta mika hannu ta dauki remote da soda din dake saman table din,kara volumn tayi sannan ta kura ma tv ido,kallonta saleem da rushd suka yi suna mamakinta,mukhtar da ya lura da hakan murmushi yayi kawai sannan ya mayar da kallonsa gidan talibijin din,minti kadan sai red ninjas suka ci,ihu mukhtar da umma suka yi suna yafa hannu,saleem was shock don sun tsorata shi,kallonsa umma tayi sannan tace dont blame me am afreak for sport channels,and am behind d reds,red rocks,so go red ta fada tare da zama,murmushi saleem yayi yace red yau are just lucky neh kawai,dariya umma tayi sannan tace losers,sannan tayi mai.Dariya mukhtar yayi sannan yace she is alwayx like dat when it comes to match,yah yah wateva,just shiiiiiiii zanyi kallo,haka suka rinka kallo tana yi tana tsalle shi kuma rushd yana binta da ido don duk abinda tayi burgesa take gashi ya ji dadin company dinta yau dinnan,amma bai san yadda zai tunkareta ba don yana ganin ya fada sonta mai tsanani,and she is being her self around him,juyar da kansa yayi ya cigaba da kallon match din,yana tunanin mafita,don shi sonta yake amma bai san ko zata yafe masa abinda yayi mata ba.........ABUJA NAIJA.........
One week before dubai
A abuja kuma su magabatan ismail sun zo sun tambayi auren umma kuma an bashi ita,nan da wata shida za'a daura aurenta,abin yayi ma mamy da momy dadi,da har yola momy tace suje saboda kawu umar dake yola tunda shine madaurin aurenta idan ba babanta,but sai yace tunda sunzo abuja ai kawai Dady yayi maganar kawai ba sai yana nan ba
da wata uku aka so sakawa amma dady yace ai gwanda asaka lokacin hutu sai sa ya Kai lokacin hutun first semester saboda kar stress yayi ma amarya yawa......
Saboda irin jin dadin da mamy da momy suke yi neh yasa suka kira umma right away suna shaida mata,lokacin tana lagos, sai da gabanta yafadi,murmushi tayi sannan tace uhmmmmm momy kenan duk zumudin bikin neh haka,gidanku momy tace tana dariya,mamy kuma take cewa ai tayi sauri ta dawo daga tafiyar da tayi saboda su san ta inda zasu fara,dariya ta rinka musu tana cewa tarewa za tayi wajan ammy kawai,da haka har suka yi sallama.
su noor mah haka suka kiranta suna tayata murna,husna har da cewa finally zasu sha chasu domin sai anyi event din zo agani da sai yan gari abuja sun san dashi,dariya kawai umma tayi bata ce komai ba saboda yanxu tana cewa baza suyi event ba zasu fara sabon bayani,akan cewa wedding din da suke jira kenan so ba zasu yarda ta bata musu show ba,da haka suka yi sallama daga conference call din da suka hada,girgiza kai kaiwa tayi sannan ta juye ta kalli su zaynab dake kallonta,dariya tayi sannan take gaya musu abinda ya faru,murmushi aysha tayi sannan tace finally we are attending nigerian wedding,dariya umma tayi sannan take tambayansu daman basu taba zuwa bikin yan nigeria ba,zaynab tace ai wannan neh zuwansu na biyu naija,shima da kyar abbi ya barsu don yaga mijin Aysha ya rasu and she need a change of environment sai sa,kallonsu tayi da mamaki sannan tace mai sa abbi bai son kuzo naija sannan kuma daman aysha ta taba aure,murmush zaynab tayi wanda yafi kuka ciwo tana kallon aysha,sannan ta kuma kallon inda umma take zaune sannan tace kinsan ammy ba ita ta haife mu ba koh,and rushd baby broda din nah neh,aysha ta fada tana murmushi,dariya umma tayi sannan tace sannan kuma kunyi kama da kannensa ba,shi yayi girma kamar kazar agric,dariya suka yi dukkansu sannan aysha ta daura da cewa back den i was a very naughty child,lokacin da ummana ta rasu ina da shekara shida sannan zaynab kuma ba'a haife ta ba,muna xaune cikin jin dadi da annashuwa duk da ummana bata da rai,babu abinda nake nema na rasa,duk abinda nake so sai anyi min musamman abbi na,kwatsam sai abbi yayi tafiya amma da zai dawo sai ya dawo da mata,anan nen komai ya chanza,i was young and stupied ta fada hawaye na zubo mata,anty siyama kanwar umma like my abbi toh sai ta dinga gaya min cewa ammy is very evil wai ta auri abbi na neh don ta raba ni dashi,don farko ina son ammy sosai,itama ammy tana sona,don ita take min wanka ta ban abinci naci,tana pampering dina sosai,sai dai abinda yasa na fara yarda da batun anty siyama shi ne idan nayi abinda bai dace ba ammy kwaba ta take,sannan kuma tace punishment dina shine,no ice cream for me n chocolate for awhole week,kuma tasan yadda nake sonshi,daga haka abin ya fara ban haushi,kinga tunda daman banajin magana,kuma duk abinda nayi ba'a kwaba min,yanxu kuma na samu mai kwaba min sai nake ganinsa amatsayin mugunta neh kuma ba'a sona,kuma abbi na baya supporting dina,duk lokacin da nayi abinda ba dai dai ba sai ta min wannan punishment din,ina da shekara bakwai ta haifi rushd,daga nan abbi ya daura so akan rushd ta fada tana matse hawaye,sai abin ya kara min yawa,gashi ana hure min kunne, gashi abbi ya daina yin abinda nake so sai abinda ammy tace,daga nan na fara ma ammy rashin kunya da hada mata turzoma yadda abbi zai kore ta daga gidan,ina yar shekara takwas babu makircin da ban koya ba wajan anty siyama,da haka duk yan uwan abbi suka fara nuna ma ammy tsana,har aka ce ammy asiri tayi mai sai sa baya jin maganar kowa sai ita,haka ba karamin tada ma ammy hankali yayi ba,ranan taci kuka da kyar abbi ya lalashe ta,ana haka kuma anty siyama ta samu abinda take so,don jaddy yace sai dai abbi ya auri anty siyama,da farko kin yarda yayi ya tirje,sai da ammy ta roke shi sannan ya yarda,nan kowa ya kara gasgata maganar anty siyama na cewar wai asiri tayi ma abbi,lokacin rushd na da shekara biyu aka auri anty siyama,alokacin neh na fara gane mai ke faruwa don lokacin na fara wayau,gashi ya hadu da anyi groming dina akan hanyar makirci,duk abinda ke faruwa tsakanin abbi da ammy anty siyama zata turani na jiyo mata shi,sai na zama munafukar atskaninsu,duk abinda suka yi tare sai abbi ya ji shi abakin anty siyama,hakan yasa suka fara samun matsala da abbi,duk wannan badakalar da ake ammy bata chaza min ba,duk da rashin kunyar da nake mata,idan ta zaunar dani sai tayi min nasiha,amma bata sani ba,ko tayi min nasiha idan naje wajan anty siyama sai ta kara min nata asama haka rayuwata ta cigaba da tafiya,ina da shekara sha daya aka turani boarding school,lokacin rushd na da shekara hudu,ita kuma daman anty siyama ta haifa yarta zaynab kuma tana da shekara daya
naji haushin kaini boarding da akayi,duk ganina ammy neh ta saka hakan ta faru,sai na kara daukan karan tsana na daura mata,daga nan bana sanin abinda yake faruwa sai na dawo hutu,lokacin dana yi shekara uku amakaranta, na dawo hutun term neh na tarar anata daru agida,wai ashe ammy drugs take sha don karta kara haihuwa da abbi,abin ya bani mamaki,lokacin na fara tunani toh idan har ammy na son abbi sosai idan anty siyama ta fada kuma tana son kwace abbi ai haihuwa za tayi don idan ya mutu ta samu gado mai yawa,tunda anty siyama tace saboda kudi ammy ta auri abbi,wannan tunanin neh yasa nasan akwai wata akasa,ace karamar yarinya kamata ina da kaifin tunani awannan dan shekaruna ai dole atambayi idan na koya lamarin gidan aure ashekara sha uku,ana haka ban samu nayi bincike ba na koma school,dana dawo hutu naga duk ammy tayi baki ta rame saboda damuwa,ranar na shiga dakinta sai naga diary dinta,lekawa nayi nagan tana down stair afalo da baki,sai kawai na fara karantawa,wallahi sai da nayi kuka,alokacin shekarata sha biyar anan naga irin rayuwar da ammy tayi tun kafin ta auri abbi da kuma irin kashin da take ci yanxu agidansa,ita aganinta daman son karya ake mata tun farko zuwanta sai sa aka juya mata baya,bata san gadan zare aka hada mata ba,kuma da hannuna aciki ba, domin nice musabbabi faruwar komai, da ni akayi amfani aka dana ma ammy tarko kuma ta fada ciki.Ban gaya wa kowa komai ba sannan ban sa ammy ta gane abinda na gani a diary dinta ba,sai dai kawai na chaza na daina mata rashin kunya ina mata biyayya,bana bari tayi kuka,don idan na sameta tana cikin damuwa nan zan zauna nayi ta bata labari ina sakata dariya don ta manta abinda ya faru,haka hutuna ya kare har na koma makaranta,lokacin da na gama makaranta ina da shekara sha bakwai,saura collage shi kuma rushd na da shekara tara lokacin abbi ya kai shi boarding school don daman shi ya shiga makaranta da sauri,ita kuma zaynab na da shekara shida,alokacin neh ammy tace ita zata koma nigeria baza ta iya zaman dubai ba,gwanda ta je nigeria idan yanuwanta suke,da farko abbi yaki amma basan yadda akayi ya yarda ba,nayi nayi na bita amma abbi ya hana,alokacin neh na san babancin mugunta da gyara,anty siyama haka za tayi ta musguna min,shi kuma abbi daman ba fiye zama yayi ba balle ya san abinda ke faruwa,haka dai sai dai na zauna na sha kukata,zaynab ke zuwa tana bani hakuri,shima idan anty siyama ta kamata tayi mata duka, ana haka na samu admission a cyprus,na tafi shine na samu sassauci,tunda na tafi sai da nayi shekara biyu kafin na dawo,shima dana dawo gidan jaddy na sauka naki sauka gidanmu,lokacin neh muka bi abbi nigeria wajan ammy,ammy tayi farincikin ganinmu,har sai da tayi hawaye,amma ni nafi kowa jin dadin ganinta ayadda take don ta mayar da jikinta tayi kyau sosai masha Allah,ammy treating dinmu take iri daya ba ka gane cewa mu ba ya'yanta bane don duk friend dinta sun zata dukkanmu yaranta neh,wani lokacin mah sai ka zata rushd neh bare,don miskilancinsa tun yana karami yake dashi,gwanda idan yana tare da ni da zaynab yana maganar kusan fifteen minti but bayan haka baya karawa.Da hutunmu ya kare muka koma dubai
YOU ARE READING
Mafarkinsa Nake 💞💞💞
RomanceNi wallahi kullum sai nayi mafarkinsa amma bana ganin fuskarsa, kullum ce min yake ni yake so amma yaki nuna min fuskarsa na gani wai sai rannan da nace ina sonsa kafin zai bayyana min kansa. Ni kuma tsoro nake kar nje na gaya ma aljani ina sonsa n...