Chapter Twenty-six

66 3 3
                                    

💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋💋
💋💋💋💋💋
💋💋💋💋
💋💋💋
💋💋
💋
Sai da tayi kusan miti biyar kafin ta nemo natsuwata ta koma daki,duk ta rikice abun da take gani a film da ji alittafai yau ta gani da idonta,ajiyar zuciya ta rinka ajiye wa kamar wanda tayi gudu,tashi tayi ta shiga bathoom tayi brush tayi alwala sannan ta fito ta hau gado ta kwanta don ita kam ta fasa shan ruwan.

Da kyar ta samu tayi barci don tana kulle ido abinda keh zuwa mata kenan,har ta kusa mantawa batayi addua ba saboda rikicewa.

washe gari da safe wayar noor neh ya tada ta abarci,bayan sun gama waya da noor take gaya mata cewa mamy tace wai bata san idan ta ajiye karamar wayar ba don bata ganshi ba,sai cewa tayi kawai ta barshi daman number victoria zata dauka aciki amma tayi mata magana a whatsApp jiya,ashe itama neman layin take bata samu ba shine ta kira batool,ita kuma ta bata wannan,okay toh shi kenan sai na iso,aha.Kwanciya ta kuma yi.

Ke na iso fa Noor ta gaya bayan da umma ta dau wayar,kina ina neh ta sake tambaya,ina gidan ya musty shiryawa nake zan fito in the next one hour,okay ni kuma yanxu na shiga compound dinsu basma ki same ni anan okay no pee,amma ya na ganki da wuri,ke dai bari ina zuwa na samu secretary dina tayi min aikin kawai sai na nayi sending mah chairman din sannan na tattaro inawa inawa na yo kano,dariya umma tayi sannan tace okay sai na iso toh,aha.

Shiryawa ta fara yi da sauri da sauri don tana son ta fita agidan nan as soon as possible,bata son mah ta hadu da daya daga cikinsu,domin she will feel more awkward around them,duk da su basu ganta ba,amma ita kunyar abin ma take ji sai sa tun safe bata bude kofarta ba,tana jin ya musty yana tambayar fareeda koh ta fito lokacin da zai fita take cemai a'a.

Atamfarta ta saka blue mai design din white and yellow flower asamansa,tayi kyau sosai acikin kayan kamar don ita aka zabo ankon,straight gown neh mai tsagu abayansa sannan gaban asamata zip ta wurin boost dinta kamar wata mai shayarwa,mayafi yellow ta dauka tare da yellow purse sannan ta saka black shoe mai rastsin yellow design.Arabian perfs ta fesa sannan ta unpulging wayarta ta fito falo,Tayi kyau sosai duk da ba wani makeup bane a fuskarta,daga powder sai lip balm da kwalli,curve dinta ya fito sosai ainun.

Tana fitowa ta hango fareeda zaune saman sofa tana kallon wani series,dago kai tayi suka hada ido, hararanta tayi sannan ta mike ta tako ida take sannan ta kalleta daga kasa har sama kafin tace agaskiya ya kamata ki daina saka irin wannan kayan ta fada tana ya tsine fuska kaman taga kashi,don bazai yiyu katuwa dake kuma baki da miji ki rinka dressing cikin gidana haka ba,don mamaki kasa magana umma tayi tana kallonta,ita kuma ta cigaba da cewa,sannan kuma gani nayi ke ba muhar.........Katse ta umma tayi da cewa ya isa haka,ke ba don girman ya musty da nake gani ba har kin isa ki tsaya kina gaya min magana ban mammare ki ba,ni sa'arki ce? ko kani na ba sa'anki bane balle ma ke sa'ar husna fa,husna ma ta girmeki da shekara daya, toh wallahi ko husna bata isa ta gaya min magana haka ba amma saboda rashin ta ido shine zaki kalli idona ki gaya min magana don kinga kina matan yayana. Toh wallahi tallahi ko da wasa kika kara tara ta da maganar bazan wallahi sai na miki rashin mutuncin da tunda kika zo duniya ba'a taba miki ba,banzan jahila mara tunani da tarbiya kawai........
Tana kai nan bata bar fareeda da tuntuni take kokarin katse mata hanzari don tayi magana ba, ta fice ta bar mata gidan,ita ko don zafin umma bata barta itama ta gaya mata na ranta ba ya sata kuka,kuka ta rinka yi kamar wanda aka daka,gaskiya idan bata rama ba anshata banza,da kyar ta samu ta lalashi kanta tayi shiru amma idonta yayi bulu bulu yayi jawur dan kuka.

Mafarkinsa Nake 💞💞💞Where stories live. Discover now