🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻🌻
🌻🌻🌻
🌻🌻
🌻
Na sani na sani,amma kar ki yanka ni tukun ki tsaya kiji abinda ya faru,umma ta fada tana son dariya don yadda amaren suka tasa ta gaba,daga gira sukayi atare alaman tayi explaining,dariyar da take rikewa tayi sannan tace kinsan akwai traffic sannan kuma na tsaya muna magana da ammy neh wallahi sai sa,am sorry ta fada tare da hade hannayenta,murmushi suka yi sannan suka ce apology accepted,so what going on,an gama decor din neh,eh an gama cewar elham, kawai event din zamu fara okay toh bari na sa kaya sai na sauko nazo,cewa sukayi toh sannan suka wuce don daman su ake jira kawai.
Umma na gama shirinta cikin royal blue gown da black turban cap,tayi light makeup dinta,ta sako flat shoe dinta sannan ta dau wayarta ta fito,tana fitowa ta hango marwan da musty tare da bobby zaune a garden opposite BQ,gabanta neh ya fadi amma sai ta dake,marwan neh ya fara hango ta,daga mata hannu yayi alamar tazo,karasawa tayi ta zauna spare kujerar dake wajan tana facing din ya musty,koh kallansa bata karayi ba bayan gaisuwar da tayi mai,marwan yace haba umma kawai tunda kika dawo baki tani sai ta yan uwanki koh,dariya umma tayi sannan tace ji yadda kake magana kamar da budurwarka kake,dariya yayi sannan yace,ai na kusa fita sahun budurwa da saurayi,nema zanje nextlevel, dariya umma tayi sannan tace nima ai nextlevel din zanje tunda na zama yaya ta fada tana mai gwalo,dariya bobby yayi sannan yace,haka neh fa marwan yaya zaka rinka ce mata tunda zaka auri kanwarta,kai na manta mah har ni ma yaya zaka ce min,kai nawa nextlevel din dayawa yake,dariya umma da bobby suka sa sannan sukayi highfive,kallonsu mustapha kawai keyi amma bai ce musu komai ba,girgiza kai marwan yayi sannan yace wato taron dangi zakuyi min koh,toh guduwa zanyi yanxu daman,dariya umma tayi sannan tace idan ma baka gudu ba yanxu zan hada ka da su little cousin dinmu su dameka,dariya suka yi dukkamsu amma banda musty,kallonsa marwan yayi domin yaga alamar baya kusa,taba shi yayi sanan yace duk tunanin amaryar neh haka,murmushi yayi kawai tare da girgiza kansa.Tashi umma tayi sannan tace bari na kara naji anfara sa kidi na je na kwaso shoki,dariya marwan yayi sannan yace toh ayi rawa lafiya,insha Allah kanina ta fada tana kashe mai ido,dariya yayi yana tuna old dayx a shinkafi investment.Tana shiga taga amaren na rawa,shiga tayi suka rinka chashewa,bayan sun gawa rawarsu suka dau hotuna tare da cin snack da drinks din,karfe shida suka gama sannan suka fito,ganin angwayen suka yi a parking lot,ita kuma nainah Abubakar yazo daukanta,kallon umma tayi sannan tace yanxu bazaki rakani ba kenan,nop bazan rakaki ba cewar umma,wannan grumpy husband dinki tab,koh dariya bayayi,am avoiding siting n breathing the same air as him,sai ya ta mah mutum kallon uku saura kwata kamar grumpy a cindrella cartoon,dariya nainah tayi tana girgiza kai sannan tayi hugging dinta,see you tomorrow sis love,okay bye ta daga mata hannu,ita kuma ta karasa wajan mijinta.Tana zuwa yayi hugging dinta ko kunyar jama'ar gidan ma bai ji,murmushi tayi mai sannan tace wai mai sa baka shiri da umma neh ta fada baya sun shiga cikin mota,kallonta yayi cike da mamaki sannan yace dole ne sai nayi shiri da ita neh,ai ba muharramata bace,but ai yar'uwatace sannan kuma ina sonta,kai baka son abinda nake so na lura,ajiyar zuciya yayi sannan ya fada azuciyar,baki san na fi son haka ba,sannan yace mata waya ce miki bana son abinda kike so,gashi baka son yar uwata,ita din ne ta fiya iyayi,mamaki neh karara afuskar junainah,shiko tukinsa yake abinsa ko kallonta bai sake ba haka itama bata kara cewa komai ba.
Allah ya baku ikon gama soyewar kenan cewar umma,dariya suka yi sannan suka zauna saman gadon,sai murmushi suke kamar wasu wawaye,kallonsu umma tayi,sannan tayi murmushi sannan ta cigaba da shan ice cream dinta tana karanta novel a wattpad.
Wayarta ne ya fara kara,ajiye robar ice cream din tayi da wayar hannunta sannan ta mika hannunta ta ja purse dinta ta ciro karamar wayarta wanda ya fara kara kuma,amsawa tayi tare da yin sallama,bayan minti biyu tace uhmmmm dadi na da kai kajen hakuri,naji kawai kayi moving kayan zuwa daya dakin mana ko kawai ayi using wannan kafin nayi setling sannan zanzo na duba important thing dake ciki sauran kuma abayar kyauta kawai,sai da safe don ka katse min abinda nake,kai ya umma ni wallahi yanxu baki sona,dariya umma tayi sannan tace ammar grow up jare,sannan ta kashe wayar bata jira wani korafin nasa ba.yauwa kun gama day dreaming din naku neh ko ya,dariya sukayi sannan husna tace ya ammar neh abi,eh fah duk rikata min kwakwalwata yake son yi wallahi.Dariya husna tayi sannan tace ya ammar kenan akwai rudewa wani lokacin.aifa kam,ya umma kinga yadda kike rawa dazu cewar elham,murmushi umma tayi,batool tace wallahi nema bansan cewa ya umma kin iya rawa haka ba,dariya umma tayi kuma sannan tace,na dai taka amma wannan ba rawa bane kenan haka suka rinka fira kafin tace bari ta basu wani shawarwari.
Gyaran murya umma tayi sannan ta fara magana,nasan banyi aure ba amma from d little i know and from what i have read zan iya fadan abu kadan,shi dai aure ba abun wasa bane kuma ya wuce soyayyar da ake yi awaje,wani sabon alamari neh,akwai ups and down dayawa,sai kun rinka hakuri da juna,zai bata miki rai zaki bata mai rai,but abu daya shi neh alokacin da daya ya hau ya kamata ki sassauta naki fushin domin idan ku biyu kuka taru kuka yi fushi akwai matsala,especially ke husna duk wannan zafin zuciyar taki daga gobe idan za'a fitar dake daga gidan nan ki ajiye shi abakin gate,shiru dukkaninsu suka yi suna jinta idon su cike da hawaye,kafin dai ta gama basu shawarwari dai sun bude famfonsu hawayensu yana zubowa,noor neh ta shigo tana tambayar meke faruwa,murmushi umma tayi sannan tace daga musu magana shine suke son sani kuka ni kuma nakiyi she ne na barsu su nayi,dariya noor tayi sannan tace mai sa ni ba'a bari ina nan akayi ba ai dana karu,ai ke yayata ce sai dai ki ban shawara nima,dariya noor tayi sannan tace kanne ma na ba yayyi shawara ai,sannan tazarar wata biyu neh kawai fah amma kina yi kamar wasu shekaru neh,dariya suka yi sun biyu.Washe garin dauri aure,duk su tashi har sunyi wanka dukkansu mai makeup din da aka dauka tana nan tana ma fuskarsu aiki,umma dai tace babu mai fainta mata fuska,kaya ta saka tayi light makeup din data saba domin ita bata fiye son kwaliya ba. Yanxu ya umma bazaki bari amiki kwaliya ba kenan cewar elham,rabani dan Allah duk awahalar maka da wuya,dariya noor tayi wanda yanxu aka gama mata kwaliya,kaya suka saka su runka hotuna abinsu ko dar dar din da amare kiji su basa ji,wai nace amaren zamani kenan.
Angwaye kuwa sun yi wanka sun sha farar shaddarsu sun daura malum malum da hulunarsu,sunyi kyau sosai.Suna isa daman su ake jira aka fara daurin aure. Nah mustapha Ahmad shinkafi da fareeda suleiman.Sannan aka daura na Mujaheed mukhtar alfasary da maryam Ahmad shinkafi (noor),sannan Muhammad (ammar) Aliyu lamido da fatima (batool) umar lamido,sai Marwan salisu lamido da Aisha elham Ahmad shinkafi,sannan Aliyu (bobby)Ahmad shinkafi da Asmau Aliyu lamido akan sadaki naira dubu sittin sittin.Bayan daurin auren neh aka rinka taya angwayen murna da fatan alkhairi,sai da suka samu aka ragu tukun suka kira amarensu suna gaya musu they are official dia wives.Daga baya suka je gidan akayi hotuna
Dadare kuma aka shirya aka garzaya pinacle hall akayi grand dinner wanda ya kayatar da kowa,awajan akayi barin kudi masu manna dollar nayi masu manna naira nayi,abunka da bikin masu dashi,karfe goma aka tashi taro,aka watse kowa ya koma gida.Washa gari aka kai ko wacce gidanta,batool da noor gidanjensu a abuja yake while husna na kaduna and elham da fareeda na kano. Kuka sosai husna tayi wanda ta saka umma kukan da bata yi niyyar yi ba,kukan husna ya dawo ma umma da memories dayawa,da kyar aka samu aka babbare su daga jikin juna abin gwanin ban tausayi donmin sai da wasu suka zubda hawaye suma. Amare dai kowanne an kaita gidanta, yanzu sai dai ayi masu fatan alkhairi sannan kuma ayi musu adu'ar Allah ya tona asirin amarya da ango.
Pls vote,comment and share
Tankx love you xoxoxox m
💋💋💋💋💋💋💋💋
YOU ARE READING
Mafarkinsa Nake 💞💞💞
RomanceNi wallahi kullum sai nayi mafarkinsa amma bana ganin fuskarsa, kullum ce min yake ni yake so amma yaki nuna min fuskarsa na gani wai sai rannan da nace ina sonsa kafin zai bayyana min kansa. Ni kuma tsoro nake kar nje na gaya ma aljani ina sonsa n...