Part 23 Qaddara ce sila

286 17 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!



_Page26-27_
•••Biki ya rage saura kwana hud'u amarya da tawagar su Innah Jumah daga rugar su inda ta tafi gyaran amare suka yo ayari guda suka taho Gumel saboda shagulgulan bikin,haka suma su Mommah ayarin nata guda zuga guda maqota da 'yan uwan su na kano duk tare suka taho.

Shi kansa Hameed abokan sa na karatu wasu na nesa har sun fara isowa gida fa sai ya soma d'aukar harami dole dai Mommah ta kwashe gayyar ta zuwa gidanta na cikin Gumel.

Sosai ake ta tanadi da shirin soma bikin a washe gari inda bikin zai somu da wasannin fulani daga bisani sauran shagulgula su biyo baya.

Amarya fa tayi shar da ita gwanin sha'awa ga wani qyalli da take kamar jaririya fatar nan sai sheqi take tasha gyaran madara irin na fulani usul tayi mulmul da ita kuma duk da haka basu qyale taba kullum cikin d'irka mata madara suke sabuwar tatsa da zafin ta daga tatsa sai cikinta.

✨✨✨
A washegari dasuka ga jikin nata yayi sauqi sosai tun kafin Mallam Marwaan yazo ma suka bata sallama suka ce in yazo tana iya tafiya.

Tana harabar asabitin ita da Ansaar zaune tana kallon zirga zirgar mutane wasu da walwala wasu akasin hakan wasu kuka ma suke.

A hankali ta riqa nazartar rayuwar da yanayin mutanen dake karafniya a gabanta wad'anda ko kusa akasarin su basu nuna sunsan da zaman ta a wajen ba kad'an ne ma suke kallon inda suke d'in wanda bawai don wani abu bane saidai dole ne ka kalli abinda baka zata ba kamar yanda itama take kallonsu.

Rayuwar ta burge ta duk da ba birni bane garin kuma shima kamar qauyen sune akasari kowa yasan kowa ne saidai su kam zaiyi wahala akwai tsamgwama da tashin hankali irin na garinsu.

Jitai gara ta zauna a garin yafi mata sauqi baza ta iya komawa cikin wannan uqubar ba musamman data tuna Iya Rammah da a yanzun ta kasa gane menene dalilin masifaffen tsoron ta da take ji ne gashi dai a bayan idon ta tana lissafin abinda take mata kuma tana jin zafi har ma tana ji a ranta tabbas zata iya maida martanin duk abinda ya sake biyo baya amma daga ta tsinci kanta a gabanta sai labari yasha banban...

Kiran sunan ta da akayi da qarfi shiya sata d'agowa a hanzarce tana kallonsa tare da had'e wani abun daya tokae mata maqoshi.

Kallo ya bita dashi ita kuma ta sunkwi da kai cike da girmamawa ta gaishe shi.

Yana murmushi mai kyau yace bayan amsa gaisuwar ta "Tunanin me kike Maman Ansaar har na zo na dad'e akanki baki sani ba."

Kauda kanta tayi idon ta na tara ruwa tace "Bakomai." Cikin sarqaqqiyar muryar ta.

Kai ya girgiza don ya lura bata son damuwa koma ba haka ba yanda ta tashi daga ciwo ya kamata ace hutu ta samu don haka kawai sai yace "Tashi mu tafi to."

Kai ta girgiza alamun "Aa."

Da mamaki yace "Aa kuma?"

Kai ta sake d'agawa alamun tabbatarwa.

Sai yayi murmushi yace "To kina da inda zaki cikin garin nan na raka ki?"

Kai ta sake girgizawa alamun Aa shima.

Saida ya zauna yana kallon ta da mamaki kafin yace "To me kike nufi nace mu tafi kice Aa na tambaye ki inda akwai inda kike son zuwa babu zaki zauna a asibiti ne bayan Ansaar yace an sallame ki?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now