Part 15 Of Qaddara ce sila

332 28 0
                                    

Qaddara ce sila
QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!

*'Yan uwa muna matuqar buqatar addu'o'in ku bisa ga kidnapping na d'an uwa gare mu wato Abu Afnan da akayi tun cikin watan ramadan don Allah asa Abu Afnan a addu'a Allah ya bayyana shi cikin aminci tare da duk wad'anda akayi garkuwa dasu amin.*

Hajaaratu AKA Queen Hazy wannan page d'in naki ne ina matuqar godiya da qaunar ki ga book dinnan da kuma ga Innar Ansaar da Ansaar sunce sun gode ana mugun Manne😍😉

                    _Page15_
Suna zaune falon su gabad'ayan su Abbu,Momma da twins gefe Maimunatu da Hajaarah da taje musu ne suma hira sosai ake a falon ana tuntsira dariya sosai suka shagala da hirar tasu abun gwanin ban sha'awa kusan Hamdiyyah ce kad'ai ke gefe bata cikin karafniyar yaran da fitinar su.

Mommah ce ta lura da yanda ta takure kanta sosai hakan ya sata kallon ta tace "Yaya Hamdy ya akayi ne?"

D'an ta6e d'an qaramin bakin ta tayi tana kallon twins tace "Mommah dubi yanda suke ta dambe ni bana son fad'a bana son su duke ni a cikina."

Duk suka yi dariya don ganin yanda ta marairaice kamar wadda suka doka d'in Areep ne yace "Hmm ai daman mata basa shiga wasan maza ko Abbu?" Ya qarasa da kallon mahaifin nasu.

Kai ya d'aga yana dariya yace "Haka yake yarona wasan mata daban na maza daban amma ko a wasan mazan ba a son na dambe da kokawa ai ko?"

D'an shiru yayi lokacin da Hameed ke shigowa falon yana fad'in "Haba Ya Bash ai wasan manyan yara kenan a dinga raba raini kawai ana zage qwanji a dinga banbance yarana da mata koba haka ba yarana?"

Da gudu suka yi inda yake suna masa oyoyo kafin Areep yace "Uncle yaushe kazo."

Yana shafa kansa yace "Zuwa na kenan my son."

Aseep da sai yanzu yayi magana yace "Uncle tsarabar mu fa?"

D'an zaro ido yayi kamar gaske yace "Lalala ai na manta kun bani sautun tsaraba,ku tuna min me ma kuka ce in siyo muku?"

Da sauri Areep yace "Gun."

Aseep ya tare shi da "And guitar."

D'an waro ido yayi yace "OMG!Like seriously i forgot yanzu menene abun yi."

Areep rigimamme sai ya ta6e fuska yana shirin sanya kuka,shikam Aseep cikin gentleness nashi sai yayi murmushi yace "Mafi miskila Uncle in ka koma ka siyo mana."

Dariya duka falon akayi kafin Hameed yace "Oh yau kam larabci ake ji gashi bani ji nikam sai turanci."

Areep jin anyi zancen yare yasa shi fasa kukan yayi karaf yace "Nima Uncle nafi son turanci."

Hamdiyyah ta ta6e baki tace "Ba mu'allim yace larabci yafi turanci ba domin shine yaren alqur'ani kuma shine yaren Annabi Muhammad (saw) kuma shine yaren 'yan aljanna ba."

Cike da kulawa Alh.Basheer ya shafa kanta yace "Da kyau Baby na Allah yayi miki albarka."

Ta washe baki tana dariya shikam Areep sai ya koma wajen Hameed yana fad'in "Uncle yaushe zaka kawo mana."

Dariya yayi yana janyo jakarsa yace "Supriseeeee." Ya zaro ya raba musu ya bawa Hamdiyyah nata set d'in na er tsana har da set na kayanta da yawa da su wardrobe da madubi.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now