Part 49

259 20 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel



P6️⃣8️⃣-6️⃣9️⃣
Kwanci tashi asarar mai rai inji masu iya magana wata d'aya kacal ya ragewa su Hamdiyyah su gama karatun su sai kuma thesis kenan (project kamar yanda masu degree suke kiransa.)

Sabeer ganin wannan lokacin yayi ya soma matsantawa mahaifinsa akan a tura gidan su Hamdiyyah don a tabbatar da magana suna dawowa kawai ayi tunda ragowa ne ya rage musu.

Mahaifinsa ya amince da hakan kuma babu wani jimawa da maganar yasa yayansa,qaninsa da kuma babban amininsa sukaje gidan su Hamdiyyah neman aurenta.

Abun mamaki ma sai suka ga ashe qaninsa coursemate d'in Abbuh ne a makaranta da sukayi a germany don haka take ma babu wani 6ata lokaci aka gama komai har rana suka saka watanni 6 masu zuwa.

ASALIN SABEER.
Sabeer isma'il Elridwan shine cikakken sunansa mahaifinsa Alhaji Isma'il Elridwan haifaffen garin Safana ne jihar katsina haka mahaifiyarsa Haj.Amina Elridwan auren zumunci ne ma tsakaninsu domin kakaninsu d'aya.

Alh.Isma'il cikakken d'an boko ne don mahaifinsa Sambo Elridwan shima haka yake kuma irin masu kud'in nan ne nada wanda Allah ya horewa albarka.

Qannen sa hud'u yayyensa biyu shine na uku Alh.Hamisu shine babba sai Alh.Sulaiman sai shi Alh.Isma'il sai Alh.Salisu sai Alawiyya sai Aziza sai kuma autan su Karima.

Dukkan su sun taso cikin kulawa da soyayyar iyaye fiye da qima yawancin su ma a qasar waje sukayi karatunsu matan ne kawai sukayi anan saboda su mata ne kuma a wancen lokacin ba kowa ke iya tura 'yar sa mace qasar waje ba.

Isma'il yayi karatunsa har masters a Petrochemical engineering yana gamawa ya kama aiki a NNPC wanda shine silar arziqinsa saidai bai wani jima ba ya juya ya koma engineer mai zaman kansa yana kuma kasuwancin da yaga bazai cinye masa lokaci ba sosai.

Yayi aure da shekarun sa 35 a duniya ya auri abokiyar wasansa Amina 'yar qanin mahaifinsu inda ta haifa masa yara 5 Anisa itace babba sai Sabeer sai Isma'il wanda suke kira junior sai Fatima sai autar su mace Fadwa.

Suma yaran sun tashi cikin gata da soyayya da kuma tarbiyya da kulawa suna fara yin degree ne anan kafin ka zabi duk qasar da kake so ka tafi kaje kayi masters.

Anisa ta gama nata har tayi aure da d'anta namiji Muhammad Noor sai shi Sabeer da yake yin nasa Junior yana ajin qarshene a secondary yayin da Fatima da Fadwa suke a junior classes na secondary school.

Wannan kenan.

Cigaban labarin.
Bayan ansa bikin ne Mommah ta roqi Abbuhn tace tunda dai har abin ya samu na Maimuna kawai a bawa gidan su saurayin nata haquri a had'a ayi lokaci guda tunda ba dad'ewa bane sai su had'a wahalar su waje guda.

Yayi murmushi yace "Kinga ikon Allah ko?inda kin barta tayi da tuni itama ta had'a masters d'inta kika dage yanzu gashi zasuyi auren su lokaci d'aya.

Murmushi tayi tace "komai rabo ne idan tana dashi sai tayi a gidan mijinta ai."

Gyad'a kai yayi yace "Hakane Allah ya taimaka mana,zan kuma musu magana inshaAllahu su taimaka mana d'in."

Haka suka cigaba da tattauna yanda lamuran zasu kaya har wani lokaci.

💧💧💧
Cikin dare ta farka da wani irin azababben ciwon baya da mara wanda ya sata nishin da bata san tana yi ba.

Cikin bacci ya ji nishin ta ya miqe ya laluba sai yaji bata wajen kwanciyar ta don haka ya miqe ya fice falon daya fi jin nishin ta ya same ta a durqushe dake da duhu cakumar ta kawai yayi yana cewa a gigice "Saratu menene?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now