Part 76

284 18 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!


Thanks so much gabad'aya masoyan QCS musamman fans group ina godiya matuqa Allah ya qara had'a kawunan mu kuma a dage da comments plz yana qara qarfin gwiwa.

P1️⃣1️⃣0️⃣
MashaAllah kusan za'ace yanzu babu wata matsala a tsakanin wajen Iyyah da Ansaar da kuma family d'in Muhammad Basheer kowa cikin farin ciki yake.

Ga Hinde sosai ta miqe nan da nan komai ya zame mata jiki ta sake zama wata kyakkyawa fulatancin ta ya bayyana sosai kai sai ka rantse bata tab'a aure ba don ba qaramin kyau tayi da gogewa ba.

A hankali komai ke tafiya tana jin dad'in zama da Iyyah ba kad'an ba.

Akace komai aka sawa lokaci sai ya zo,watanni uku a tsakani su Iyyah harda Hinde suka samu hutun Winter,duk suka tattaro suka dawo gida nigeria inda suka tadda shirye shiryen biki yayi nisa kusan Mommah ta gama komai Iyyah na zuwa itama ta jone suka cigaba da shirye shiryensu.

Abbuh ya had'awa en ukun nasa lefe na gani na fad'a kowannen su saida ya samu akwatuna dozen abin su sauran sati uku aka kai na Lubna washegari aka wuce gangare aka kai na su Fauziyya.

Aifa qauyen nan ya d'auka kai sai ka rantse kantin kwari,sabon gari da rimi aka kaiwa emmatan kowacce uwa sai fatan ko rabi tata er ta samu take ga emmata kuwa abun sai ya zame musu kamar wani koma baya a wajen su don dai babu wadda aka tab'a yiwa irin wannan hamshaqin lefe irin haka yanda aka dinga shiga kallo kuwa saida aka dinga dakatar da mutane don kada ayi sata daga nesa qanwar Hansai ke d'addagawa kowa yana gani en munafunci kuwa tun suna iya irgawa har lissafin ya kufce musu don akwatuna 24 ba wasa bane.

Takanas Ansaar ya sai kayan fitar biki kowacce amarya kala biyar da kansa ya kaiwa Lubna da measurements na su Fauziyya yace don Allah takai wajen d'inki na fashion designers wanda suka iya a d'inko.

Aiko takai wajen wasu fitattu suka tsantsara musu d'inkin zamani yayi matuqar kyau da tsari kuma duk kala d'aya ne saidai na Lubna yafi nasu girma ne kawai.

Tun ranar alhamis aka soma shagali a cikin kano inda angwaye suka kama babban marque aka cancare aka sha shagalin dinner,ranar juma'a akayi kamu,ranar aka ranar asabar kuma aka d'aura aure aka zarce da yinin biki a nan gangare,wadda Lubna a ranar aka kaita gangare d'in tare da en uwan ta da qawayen ta,a ranar suma su Fauziyya aka kaisu ranar lahadi kuma aka wuce gumel nan ma akayi yini sannan washegari litini duk aka watse amare aka wuce dasu kano cikin unguwar rijiyar zaki inda Abbuh yayiwa angwayen manyan gidaje guda uku a had'e kowacce tanada bedrooms hudu kowanne da toilet da faluka biyu da kitchen da store abun sai wanda ya gani.

A daren ranar Ansaar ba qaramin kuka yaci ba tuno da daren su na farko da Saratu da yayi haka nan itama Asiyan gabad'aya ta rikice ta gigice saboda rashin sabo amma ganin ya barta baima je inda take ba sai hankalin ta ya d'an kwanta don ko bakomai dai tasan bazai mata komai ba.

***
Ana gama biki da sati guda Ansaar dasu Mommah suka juya Uk harda Abbuh.

Suna komawa Ansaar yace saidai a sake samun wani gidan tunda gidan da suke ciki d'aki biyu ne ga kuma Abbuh na kawo musu ziyara time to time.

Haka suka yi manage zuwa suka samu wani babban gidan na haya mai dakuna uku suka koma nan da nan kuma ya soma nemawa Asiya makaranta wanda anan ma nigeria Aseep ya nemawa Fauziyya itama nan da wani satin zata fara zuwa.

***
Suna zaune a berroom d'insu Abbuh ya kalle ta yace "Iyyah wai ya har yanzu naji shiru ne??"

Ta kalle shi sannan ta maida hankalin ta kan takardun ta tace "A me kenan?"

"Babies har yanzu naji babu labari."

Kauda kai tayi tana murmushi bata ce komai ba,ya sake cewa "kuma gaskiya kamar lefin kine."

Sai a sannan ta kalle shi sosai tace "Taya ya zama lefi na?"

Ya watsa hannun sa sannan yace "To naga ni ina abinda ya kamata kece dai kunya tasa kike tauye mu kullum gaskiya ni na gaji Babies nake so."

Dariya tayi ta miqe tace "Allah ya kawo masu albarka."

'"Amin." Ya amsa yana miqewa shima ya shige toilet.

Yana fitowa yace "Nikam yau sai nayi ajiya zan haqura fa don haka ki shirya." Ya qarasa yana durfafar ta.

Ganin da gaske yake yasa tace da sauri tana juyawa "Wallahi ka fa riga kayi don Allah kayi haquri ciwon jiki nake."

Ya qarasa inda take yana dariya yace "Da gaske ko da wasa?"

Itama sake girgiza kai tayi a shagwab'e tace "Allah kuwa."

Ya jawo ta yana d'age rigar ta yace "Tun yaushe."

Murya can qasa tace "1month 1week."

Ya d'ago yana zare ido yace "Amma baki sanar dani ba??"

Tayi murmushi tace "Naga kana cikin hidimar biki ne amma Mommah ta sani."

Harara ya balla mata kan yace "Oh k naga alamar Mommahn nan ta fini a wajen ki."

D'an zaro idon ta tayi cikin wani salo sannan tace "Kaii Abbuh kishi kake da Mommahn kuma yau?"

Murgud'a baki yayi yace "Ba wani kishi ya ni da d'ana amma bansan na ajiye ba sai aje a fad'iwa wani ace bazan yi kishi ba."

Dariya tayi don yanda ya murgud'a bakin sannan tace "Uhm to am sorry."

Dariya shima yayi yace "Its Ok thanks Allah ya raba ku lafiya Allah yayi miki albarka."

Cikin murna tace "Amin."

Daga haka kuma naga labarin sha banban don haka na fito ina ta murna wa wannan ahli tare da ja musu qofar.

ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now