Part 62

235 18 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!




P9️⃣4️⃣-9️⃣5️⃣
Suka gaisa a mutunce yanda suka saba suka dan tab'a hira sannan ya maida hankali sosai yana kallon ta yace "Wata magana ce ta kawo ni fa maman Ansaar."

Ta gyara tsaiwar ta tana murmushi tace "inaji."

Yace "Daman kan maganar aure ne."

Yanda yayi maganar saida taji gabanta ya fad'i,tana tuna yaushe rabon da ayi mata maganr wani abu waishi aure a rayuwar ta idon ta ya ciko da qwallah tana roqon Allah yasa ba shine zai ce yana sonta zai aure taba don da matsala...

Ya katse mata tunani da fad'in "Baki magana ba?"

Da qyar ta had'iye hawayen ta tace "Uhm ina jin ka meya faru da auren?"

Ya sake yin murmushi yace "Yaya nane Allah yayiwa matarsa rasuwa wanda na fad'a miki rasuwar ai."

Ta jinjina kai qirjinta na cigaba da bugawa,ya sake gyara tsaiwa yace "Na fad'a miki mu biyu ne Allah yaba iyayen mu kuma mahaifiyar mu ta jima da rasuwa shine nake neman alfarma a wajen ki."

Kad'a kai kawai take ta kasa magana ya cigaba "Don Allah ba don ni ba ki taimaka ki mana alfarma ki aure shi don wallahi na tabbatr ke da shi zakuyi alfahari da samun juna."

Runtse ido tayi tana ji a ranta M Marwaan ya d'aure ta tamau da jijiyoyin jikinta ita kam baza ta iya masa musu kan d'an wannan abun ba saidai ita sam aure baya gabanta bata jin zata iya auren sa ba tare da burin data sa a gabanta ya cika ba.

Ya lura da yanayinta don haka yace "Kije kiyi tunani kiyi shawara kuma bazan takura ki ba koda ace bayan shawarar abinda kika yanke bazai min dad'in ji ba ni farin cikin ki ya fiye min komai a duniya don ni kallon qanwa uwa d'aya uba d'aya nake miki don haka kije ki tunani."

Kasa magana tayi,don M Marwaan yafi qarfin komai a duniyar ta don shine mutumin da ya fi 'yan uwan ta na jini jin ciwon ta da sanin darajarta ba tare da dogon nazari ba tace "Mallam ni ai banda zab'i koda kuwa yau cewa kayi ga miji kayi min balle kuma d'an uwan ka wallhi na karb'a."

Dariya yayi sannan yace "Aa ki dai je ki nazarin tukunna karki yanke shawara kai tsaye bari naje."

"Toh." Kawai ta iya cewa don ita har ranta ta aminta da zab'in sa amma baza ta qi shawarar sa ba don haka ta barshi ya tafin.

Ta shiga gidan su Hafsatu da Salame sai Jummai suna qoqarin shigewa da kaya saboda hadari daya gangamo garin nata bugawa ga iska ana yi, Jummai ce tace "Uhm ayi dai mu gani idan iska zata hura wuta."

Salame ta tab'e baki tace "Uhm sanabe iyayi,yo bariki ai ba er amana bace kowa ya gama iya shegen sa inta tashi wullo shi baza tayi masa ta ta dad'i ba."

Murmushi kawai tayi ta wuce abinta don har ranta bata ji komai to baya ma taji maganganun da suka ninka wannan meye zata damu kanta yanzu akan en wad'annan maganganun?

Ansaar na tsakar farfajiyar su Mahmoud na d'akin su nada a falo suka shimfid'a katifar Saratu don ba a tab'a komai ba har lokacin komai na nan inda yake.

Da sallama ta shiga ya amsa mata yana mata kallon mamakin ganin fara'ar kan fuskar ta don yana jin irin baqaqen maganganun da su Salame suka gaya mata.

Hannun sa taja zuwa d'akin ta suka zauna sannan ta soma fad'a masa abinda ya faru tsakanin su da M Marwaan ta qare da "Duk da yanzu babu zancen aure a raina ko a gabana ina son cikawa Mallam muradin sa don ya cancanci komai daga gare mu,shine mutum mafi qima a idona a garin nan."

Jinjina kai Ansaar yayi yace "Iyyah wannan shawarar taki mai kyau saidai ina ganin ki istikhara tukunna kada a je ba a rabu da bukar ba a haifi habu ga garba a baya."

D'an b'ata fuska tayi tace "Me kake nufi kana zaton mallam zai cutar damu ne?"

Girgiza kai yayi yace "Sam ba haka nake nufi ba idan da zai cutar damu da tuni yayi mana amma ina fad'a miki ne a harkar aure babu gaggawa yana buqatar nazari da dogon tunani da shawara da addu'a kuma don haka duk muyi hakan musamman da ya kasance matar sace ta rasu ba kece ta farko ba."

Shiru tayi kawai can tace "Bazan qi ta taka ba zanyi istikhara."

Cikin jin dad'i yace "Yawwa Iyyah Allah ya zab'a mafi alkhairi."

"Amin." Ta amsa cike da jin dad'in samun d'a d'aya tamkar dubu.

Daga haka ya juya zancen kan labarin Lubna dama zaman da yake gidan su Mahmoud a yanzu haka duk da taji ba dad'i ta kuma ji dad'in yanda ya samu wani wajen da tama fi wancen kwanciyar hankali amma duk da haka tace "Idan ka samu sukuni ka riqa bullawa can wancen gidan kana gaida su tunda anyi zaman mutunci."

Da to ya amsa mata yace sufa jibi zasu wuce saboda ya gama makaranta zasu yi er dinner da sauran su kuma.

Haka sukai ta hira har Mahmoud ya gama waya ya dawo shima ya zauna suka cigaba da hirar tare.

🦋🦋🦋
Mommah cikin wannan kwanakin duk ta qare ta qara sawa kanta damuwa fiye da da ana magana zata ce ita ba abinda ke damunta amma kowa ya kalle ta yasan da matsala.

Haka yasa suka shirya suka nufi Gumel saboda Abbuh yasan kaf duniya in shi ya kasa to Baffan tane kad'ai zai iya wannan karon dai shima Baffan ya gaza don duk yanda yaso lallashin ta sai ya kasa dole suka zubawa sarautar Allah ido don har wannan lokacin Abbuh bai bar zuwa bakin Bayero university ba ya tsaya wai ko Allah zai sa yaga Ansaar amma babu alamun sa har ma ya fara tantamar wanzuwar sa a makarantar yana tunanin ko ba nan yake yi ba.

Har gizo yake masa cikin d'alibai saidai in yazo sai yaga bashi bane.

✨✨✨
Su Ansaar qarfe biyar na yamma suka bar garin su zuwa kano cikin motar haya abinsu basu da matsala suna ta hirar shirye shiryen dinner d'in da zasu je yau da daddare Isma'il ya kira shi yace yaje gidan su su shirya su tafi.

Har sabon d'inki yayi suna shiga kano kuwa suka raba hanya Mahmoud ya tafi da jakar su yace sai sun had'u wajen dinner d'in don ya gayyace shi,shi kuma ya wuce gidan su Isma'il don su shirya.

Yana zuwa ya tadda ya musu wata dakakkiyar shadda blue getzner sai d'aukan ido take yace yayan sa ne ya sai musu da zaije ma amma aka samu akasi aka kira shi wajen aiki dolen sa ya tafi bazai samu damar halarta ba amma yana so su had'u da Ansaar d'innan.

Ansaar yayi dariya yace "Nima inata so mu had'u fa shekara hud'u."

Isma'il yace "Indai da gaske ne mu dawo ka kwana anan gobe yace zai dawo harda matar sa."

Cikin rashin damuwa yace "Allah ya kaimu goben."

Amin isma'il ya amsa suka fice yaje yayi wa hajiyar su sallama suka fice.

Wajen dinner sunci sun sha abin su anyi harka iya harka anyi nishad'i basu suka tashi ba sai qarfe goma sukayo gida a gajiye tilis suna zuwa suka nemi makwanci suka kwanta don ba qaramin gajiya suka yi shi kansa Ansaar ranar yayi abinda bai tab'a yi ba ya kula wadanda bai tab'a kulawa ba harda exchanging nums ansha ta.




ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now