58

237 17 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel





P8️⃣6️⃣-8️⃣7️⃣
Washegari ya dawo gidan yana ji a ransa lalai dole ne ya nemawa kansa mafita cikin gaggawa idan ba haka ba Lubna zata rusa masa lissafi harda rayuwarsa gabadaya da karatunsa daya shekara hud'u yana fama da fad'i tashi.

Yana shigowa suna fita a mota da Sani a ransa yace "Gantalalliya ni me zai sa na auri macen da bazan iya sata ko na hana ta ba."

Taga shigowar sa kamar ta cewa Sani ya tsaya sai kuma ta basar ta qyale shi suka wuce tana ta tunani kala kala a ranta.

Cikin gidan ya shiga Hajiya Abashiya bata falon sai Hanne dake aiki ya gaishe ta ya tambaye ta ina Hajiyar take tace "Yau dai banga saukowar ta ba kasan kuma da yake Alhaji yana nan baza ta sauko yanzu ba abincin safe ma sai saman aka kai musu saidai da yamma."

Kai ya kad'a yace "Ba damuwa inta sauko kafin na dawo kya sanar da ita na shigo."

Da to ta amsa ya juya ya fice ta bishi da kallon sha'awar halayyar sa ta sanyi da sanin ciwon kai.

Lubna kuwa gidan su wata qawarta Na'ila taje don yanzu akan Ansaar data lura Hidaya itafa ta fad'awa Ansaar b'oyewa kawai take tana nuna kamar babu komai don ma shi ba mai saki bane ta tabbatar da tuni ta riga ta sanar masa abinda ke ranta.

Na'ila itama qawar suce saidai ba kamar Hidaya ba da take childhood friend dinta ita iya degree sukayi tare saidai sun shaqu sosai don halayyar su da yanayin su iri d'aya ne da yawa ma daga course mates d'insu suna zaton yaya da qanwa ne.

Maman Na'ila ta tarar a falon ta gaishe ta ta amsa cike da fara'a sannan tace "Na'ilan na d'akinta jeki."

Lubna ta miqe ta shige d'akin nata tana kwance tana fama da laptop da alamu da akwai abinda take son yi yaqi yiwuwa duk ranta a jagule yake.

Tana jin sallamar ta ta miqe da ihun ta tana fad'in "Ga bae ga bae."

Dariya tayi suka zauna kan gadon Na'ila tace "Bae ashe ashe dai."

Dariya Lubna tayi tace "Ashe me?"

Na'ila ta danna wata waya dake kusa da ita irin landline d'innan na da tana cewa "Bari na sa a kawo miki abinci tukunna sai mu zauna."

Lubna ta cire yalolon mayafin data yafa saman doguwar rigar ta sea green ta zauna sosai tana fuskantar Na'ila ta soma magana "Kafin a kawo bari na soma kora miki nawa labarin."

Lubna ta gyara zama tana kallon ta tace "Hala anyi new catch ne."

Dariya tayi sannan ta soma bata labarin abinda ya faru tun daga sanda ta soma ganin Ansaar har zuwa fad'a masa tana sonsa da tayi da amsar da ya bata.

Na'ila tayi shiru lokacin da me aikin su ta shigo da tray da abinci akai shinkafa da miya da peppered chicken da hadin salad ga juice me sanyi a gefe.

D'ayan tray d'in kuma aka zubo snacks dangin su samosa da spring rolls dasu cake gadai sunan MashaAllah nida ke gefe sai hadiye yawu nake ina leqe.

Kallon abincin tayi tace "Sauko muci sai mu yanke shawarar abinda zai iya biyo baya."

Ba musu Lubna ta sauka suka soma cin abincin tana bata labarin nata saurayin da abinda ya faru bayan ya gama cin moriyar ganga sai kawai ya nemi yada koranta ta qarashe da "Ni kuma nace wallahi be isa ba yanzu jiyan nan nida mama mukaje wajen maman shi na gaya mata yanzu haka ma cikin sane a jikina aiko maman nasa ta d'auki zafi kinsan dangin sarauta ne shi ta dinga fad'a tana cewa wai zai ja musu abin fad'a a gari aiko dole ya aure ni zancen da nake miki har baban sa ya kira Abba yace zasu turo cikin satin nan."

Dariya Lubna tayi tace "Amma baki da kyau bae wallahi yanzu da cikin zaki auren?"

Harara ta galla mata tace "Wanne irin ciki ana zaune qalau?wallahi ba abinda ke tare da ni ke kinsanni bazan taba yadda wannan gangancin ya same ni ba ban tab'a ba sai kace wata farin shiga."

Dariya ta sake yi tana cin spring roll d'aya tace "Oh qarya kikaje kikai masa kenan idan suka gane fa.?"

Na'ila ta tab'e baki tace "Baza su gane ba hajiya don har medical result muka kai musu."

Lubna ta gyad'a kai tana hawa saman gadon tace "Nasan halin ki baki da sauqi akan abinda kike so amma ban tab'a zaton zaki yiwa Sulaiman haka bafa."

Murmushi tayi itama tana dawowa kusa da ita da tray d'in snacks d'in a hannun ta tace "Ke ma gashi nan kin fad'a cewar in ina son abu,kema kinsani a duk harka ta ban tab'a haduwa da wanda naso kamar shi ba don haka kam dole ya haqura ya karb'e ni ko baya so."

Lubna tace "Balle ma zai so shi din banza saidai bai shiga hannun kiba."

Dariya suka yi harda shewa sannan Lubna taci serious tace "Ni fa ban gano ta inda zan tallafo abinda nake so ba nima."

Na'ila tayi baya ta kwanta tace "Abu mai sauqi ne kema sai ki riqa abu kamar baki zauna dani ba?"

Dariya tayi tace "Ban gane ba,fad'a min."

Janyo ta tayi tana cewa "zo kiji."

Banji meta rad'a mata ba sai ihun su da har ya so firgita ni na yarda birona saboda qarar Lubna da d'ora da birgima saman gadon tana wani irin abu na alamun tsantsar farin ciki. (nNidai ina gefe mamaki ya ishe ni ina kuma jiran ganin Lubna ta aiwatar da shawarar qawarta.)

Sun jima sosai suna hira don har yamma ta kai sannan ta kira sani tace yazo su tafi.

Suna komawa kuwa ta shiga d'akin mahaifin ta kai tsaye yana zaune kan kujera a falon sa yana karatun wata magazine ta kasuwanci ta zauna tana cewa "Wash Daddy na gaji."

Murmushi yayi yana kallon ta yace "kije ki wanka mana ki d'an huta ko."

Har ta miqe ta koma ta zauna tana cewa "Daddy baza ka fita ba yau?"

Ya sake d'agowa yana dubanta da kulawa kafin yace "Ina zani ai yamma tayi Princess."

Murmushi tayi ta juya tace "To bari naje na dawo bana jin bacci."

Ta soma tafiya yace "Da labari kenan."

Dariya tayi ta juyo tana kallon sa tana gyad'a kai.

Shima dariyar yayi yace "To sai kin dawo."

Bata amsa ba ta juya ta fita tawuce d'akin ta,wanka ta fara yi ta zura wata doguwar riga baqa armless ta tufke gashin kanta ta nad'e shi tayi clipping d'in sa da wani clipper,sai ta fito sak baturiya tayi kyau sosai.

Ta juya gaban madubi bayan ta gama fesa turaren ta mai sanyi da dad'i tana murmushi ita kad'ai.

Ta fito harta doshi hanyar qasa ta fasa ta koma ta shiga d'akin mahaifinta.

❣️❣️❣️
Ansaar tunda ya dawo yake babu dadi haka nan,ya rasa abun yi ya kuma d'auki litattafan amma karatun yaqi yuwuwa haka nan ya shiga gyaran kayan sa yana ninke su yana jera su cikin jakar sa daya siya qatuwa ta zuba kaya.

Litattafan ma dake yana da jakar da yake amfani da ita wajen adana su sai kawai ya tattare su da handouts d'insa duk ya zuba su ciki kamar wani mai shirin tafiya gabad'aya don bai bar komai nasa a qasa ba dama shi gwanin tsafta da ita killace komai nasa sam bai iya baza shirgi ko kayan sa ko'ina ba.

Har bayan magriba yana abu d'aya saida ya katse ma yaje yayi sallah ya dawo sannan ya samu ya gama yana gamawa ya kwanta bakin katifa tana jin qirjin sa na bugawa da yawan fad'uwa da gaban sa keyi ya rasa kuma dalilin hakan.


Na baku gari guess me zai faru nan gaba.

Ayi manage da wannan am kinda busy today.

ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now