Part 41

278 23 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel





P5️⃣4️⃣-5️⃣5️⃣
Ga Hansai kam tsawon kwanaki ta d'auka tana zantawa da zuciyar ta so take ta yardarwa kanta tabbas ba wani aibu a auren er ta da Ansaar so take dole ta gamsar da zuciyar ta yarinyar ta ta samu mijin da daya dace da ita wanda hankalin ta zai kwanta.

Wannan zaman ga Saratu kamar a kurkuku take don bata saba ba mahaifiyar ta na sonta matuqa kusan tafi sonta akan duk sauran yaranta wannan yasa tafi jan ta a jiki tafi hira da ita fiye da sauran sunfi zama indai ba talla ko makaranta ta tafi ba duk zamanta a gida suna tare da juna don haka wannan abun ke matuqar qona mata zuciya da rai wannan kuma shiya figar da ita ya ramar da ita fiye da tunanin mai tunani a wannan kwanakin.

Shikam M Ladan ya zuba mata ido ne ya bata lokaci don yaga iya lokacin da zata d'auka ya lura tabbas tayi matuqar sanyi saidai baiga tana da niyyar neman inda Saro take ba har aka kwashe sati da maganar,wannan yasa yaje ya sake samun ta daren da yake d'akin ta bayan ta sallami yara ta dawo tana ninkin kayan yaran da da Saratu ke yinsa ya kalle ta cikin taushi da sauqaqa murya yace "Wanne hukunci kika yanke ne akan Saratu?"

D'an shiru tayi tana tuna hukuncin da ta gama yankewa kanta a d'azun nan da yamma tana tsakar gidan qawar Karime tazo sun gama hirar su sun fito zata raka ta ta kalle ta tace "Ashe kuma haka abu ya fru to Allah shi kyauta don surkunta da shege ai jafa'i ne saidai ka tubarwa Allah don wataqila kayi wani babban zunubin ne...."

Ai kafin ma ta qarasa Hansai ta miqe tana huci ta soma qunduma mata ashar wanda sam matar bata zace shiba don yanda Karime ta bata labarin haukan da tayi tayi zaton har yanzu tana nan kan tsini ne yanda zasu qaddamar da shirin su na rabata da gidan M Ladan don ta lura ya zuciya sosai da abinda tayi qila in suka tunzura ta tayi wannan karon ya sake ta amma sai suka ga akasin haka ta zage su tas ta cigaba da harkar gaban ta ta barsu da kunyar juna don ba qananan goruka taja musu ba.

Wannan tunanin ya jata lokaci mai tsaho kafin ta amsa masa har ya fidda ran zata yi magana yana niyyar sake yi mata magana tace "Na amince kuma na sawa wannan auren albarka Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba."

Wani irin farinciki ne ya ziyarce shi irin wanda ya jima bai jishi ba ya tashi da sauri ya qarasa gaban ta yana dariya ya shiga shi mata albarka da nuna mata tsantsar farin cikinsa.

Cikin murmushi tace "Gaskiya tun yamma naso samun ka da maganar saidai kunya ta hanani da nauyin abubuwan da nayi don Allah kayi haquri ka dawo min da Saro in sha Allahu baza kaga abun kaico ba."

Dariya yayi yace "Gobe kuwa yanzu ma badon dare yayi ba da tuni na je na d'auko ta."

Nan da nan ta bada kai suka shiga shirya yanda auren zai kasance dama ranar da aka saka da irin abubuwan da za'ayi duk da yace mata baya son bidi'a amma daya ga ta gane kuma yasan tayi namijin qoqari sai ya qyale ta kawai ya tayata lissafi.

✨✨✨
Iya Rammah duk da bata da qafa amma duk abinda ake akan idon ta akan kunnenta ta shiga matuqar tashin hankalin da bata taba shiga ba kuma abun mamaki qafar kamar daman jiran dawowar su Ansaar take nan da nan ta soma warkewa tana kamewa cikin abinda bai wuce kwana shida ba aka kwance d'aurin da akayi mata alamun sauqi ya samu kenan sosai tana takawa da sanda ko'ina.

Koda taga yanda ake gini kuma harda d'anta Auwalu wanda mahaifinsa ya tilasta masa yi badon yaso ba ta kuma shiga tashin hankali sosai da gayya ta kwalla masa kira tace yazo zata aike shi.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now