Part 59

234 20 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!




P8️⃣8️⃣-8️⃣9️⃣
Rana tsaka ne don har sha biyun rana ta gota Iya Rammah ta fito daga d'akin ta tana waga uwar hamma da miqar da babu salati ta nufi madafa don ganin ko akwai wanda ya d'ora musu abincin yau ko kuwa sun yi tsiyar.

Ilai kuwa babu wanda ya d'ora da alamu ma tun da safe ba wanda ya koma wajen don ga tukunyar da akayi d'umame nan ba a tab'a ta ba an barta a wajen.

Ta ja wani mugun tsaki kamar zata tsinke harshen ta sannan ta lailayo wata qatuwar ashar ta narka lokaci guda ta nufi murhun tana cewa "Bari na d'ora mana nida yarana naga shegiyar marar kunyar da zata ce tana jira abinci."

Icce ta d'ebo da karare ta soma jerawa ta gama had'awa ta d'auko makamasai irin ledoji da 'yan robobi ta had'a su tasa d'an kananzir ta qyasta ashana aiko ta kama ganga ganga sosai kamar daga sama kafin ta d'ago taji Lami tace "Kai wallahi kin kyauta nima yunwar nan nakeji sosai yi maza ki gama mana muci."

Tsabar firgitar da tayi bata san yi baya ba sai ji tayi ta gwaru da mutum da qarfi Lami ta tura ta tana cewa "Yau naga iskanci karya ni zaki?"

Bata tashi sauka ba sai cikin wutar da ta had'a aiko ta kama kayan jikinta ta soma ci,dariya sosai Lami ta somayi kai kace saukar aradu ce kuma abun mamaki ihu Iya Rammah take amma babu uban daya leqo kamar babu mai rai saida rigar ta ta atampa roba ta narke a jikinta sannan mutan gidan suka soma fitowa a gigice da alamun yanzu ne suka soma jin ihunta.

Cike da kad'uwa Salame da Hafsatu suka nufe ta suna tambayar ta meya faru haka, Salame takai hannu da niyyar tab'ata sai tsokar wajen ta biyo hannun ta ta Sale gabad'aya wani salati suka saki gabad'aya lokaci guda Lantana tayi waje tana ihun neman agajin maqocinsu sharifi ne yana kamun wuta.

Da dabara suka janye ta daga wajen zuwa d'akinta har ta gaji ta daina ihun tayi shiru sai azaba dake addabarta.

Koda Sharu yazo shi kansa abun ya firgita shi don tun daga fuskarta har wajen cibiyar ta qonuwa ce sai wani irin nishi take abun tausayi haka ya zauna ya kama mata tana ta nishin wahala ya bada magani yace a riqa shafa mata shi ya tafi tana tunanin abinda zai haddasa qonuwa ga babbar mace irin Iya Rammah a ransa kawai dai yace "Tsautsayi ne daga haka ya share zancen a ransa ya cigaba da sabgar sa."

Ko ga matan gidan gutsiri tsomar da suke yi kenan meya faru har ta qone haka?wasu suce tsautsayi wasu kuwa suce da walakin banza ai bata kai zomo kasuwa.

Iyyah na b'angaren ta tana jin duk abinda ke faruwa bata fito ba sai da daddare ta leqa tako kid'ima da ganin yanda Iya Rammah ta qone haka tayi mata sannu bata amsa ba sai kallon tsana take binsu da shi daga ita har Saratu dake biye da ita tana rab'e jikinta ita tsoro ma ta bata don bata tab'a ganin irin wannan abun ba.

💦💦💦
Twins har sunayen su ya fito sune Batch C na masu tafiya camp aka akaisu abeokuta can wani qauye acan zasu yi nasu camp d'in.

Aseep sarkin qulafacin gida dukda shekaru da yayi a waje ya dinga qunci kan wannan tafiyar kamar wanda zai bar qasar.

Areep kam kamar ba ruwan sa don sabgar sa kawai yake yi tafiyar ma bata gabansa sam.

Cikin satin suka gama shirin su suka d'auki hanya harda Abbuh da Hameed suka raka su har camp kafin suka juyo.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now