Part 55

262 22 2
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel

*MuhammadKademi my fan from wattpad am so proud of u and I appreciate every single comment and like from you thank you so much I really really appreciate it this page is dedicated to you Allah's khair always.*

P8️⃣0️⃣-8️⃣1️⃣
Karatu sukayi sosai saboda sunsan semester d'insu ce ta qarshe ga project babu wasa dolen su su maida hankali in ba haka ayi babu su.

Sai gab da magriba suka fito Isma'il ya ajiye shi a gida shima ya wuce nasu gidan.

Yana shiga harabar gida yaci karo da Sani driver, Sani yace "Kai ina ka shiga ne wai?"

Ya d'anyi murmushi yace "Naje karatu ne."

Tab'e baki yayi yace "To madam ce take ta neman ka tun yamma."

Qaramin tsaki yaja wanda iya shi kad'ai yaaji abin sa sannan yace "Lafiya iceko?"

Sani yana barin wajen yace "Ni ta ina zan sani ko lafiyar ko aa kaje kaji mana."

Kai tsaye ko littafan da yayo aro a libraryn bai ajiye ba yayi falon,yana zuwa ya tadda su da hajiya zaune suna hira da kallo ya shiga da sallama ya tsugunna ya gaida Hajiyan da fara'a tace "Sarkin karatu hala daga can kake."

Murmushi yayi yace "Eh jibi zamu koma ne shiyasa."

Hajiya tace "Da kyau,ya akayi ne."

Ansaar yayi qasa da kai yace "Sani ne yace Hajiya qarama na nema na tun yamma shine nazo."

"Hajiya qarama?" Ta maimaita a fili wanda saida duk suka juya suna kallon ta.

A daqile tace "Sunana Lubna plz."

Murmushinsa yayi mai kyau sannan yace "Gani."

A ranta tace "Wannan gayen ya cika rainin wayo wato gyaran ne bazai yi ba kenan..."

"Kin tsayar dashi bakice masa komai ba." Maganar Hajiyar ta ta dawo da ita.

Da d'an in'ina tace "Am daman dazu ne zan d'an aike shi to kuma na ma riga na samu shikenan."

Ansaar ya miqe yana cewa Hajiya "Saida safe Hajiya idan da buqatar wani abu kuma to ina d'aki."

Hajiyan tace "To Ansaar saida safe."

Daga haka ya fice ita kuma Lubna ta kwanta sosai jikin kujerar da take kai tare da lumshe ido kawai cute fuskar sa ke mata yawo cikin duhun daya ratsa ganin ta tana sonshi da yawa kuma bata jin zata iya jurewa har tsahon wani lokaci zata soma bayyana masa irin son da take masa idan bai gane ba zata fito fili ta furta masa kawai ta huta.

Da wannan shawarar ta miqe ta haye sama,Hajiya ta bita da kallo tana sane da ita tana kuma nazarinta tunranda ta fara ganin Ansaar ta lura da yanda take abubuwa hatta da kayan da ta bashi akan idon tane ta nuna bata gani bane saboda itama Lubnan bata so ta sani ba,kuma taji matuqar dad'in yanda Ansaar d'in ya nuna mata shi wannan baya gabansa haka nan taji ita kanta ya burge ta yaro mai tsayawa daidai matsayin sa ba irin matasan yanxu ba masu kai kansu inda Allah bai kai suba.

Ansaar kam komawa d'aki yayi ya d'an watsa ruwa sannan ya fita masallacin qofar gidan su suka zauna dasu Sale me gadi suna ta hira har goman dare sannan ya dawo cikin gidan.

D'aki ya wuce kai tsaye ya kwanta don ya samu ya tashi da wuri washegari.

✨✨✨
Qarfe biyu na dare ne Iya Rammah dake kwance ta baje tana shaqar barci kamar wadda bata da wata damuwa a duniya taji ana tab'ata da alamun tashin ta ake.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now