Part 12 of Qaddara ce sila

338 21 2
                                    

*QADDARA CE SILA!*😢

🌍 *HAJOW* 🌍
🌍 *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* 🌍
_{United we stand our aim is to educate and entertain our readers}_
*©️ZahraArkel*

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewar QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai ANA BARIN HALAK..ko don kunya.*

Facebook@ZahraArkel/HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS.

Wattpad@ZahraArkel.

*'Yan uwa mungode matuqa da addu'ar da kuka yiwa abokin mu aminin arziqi Bg Kazaure wanda ya rasu a 'yan kwanakin nan sannan muna qara baran addu'an ku akan rashin Baby da nayi ranar juma'ar nan data gabata Baby Muhammad sani (Nabeel) Allah yaji qansa yasa mai ceton Iyayen sane nagode Fans Allah yabar zumunci.*

                                    _Page 12..._

●●●Tana shiga ta same shi da Hameed da twins suna ta hira gwanin sha'awa abinsu,ta nemi waje ta zauna haka nan Maimunatu ta gaida Baffah ta miqe ta fice daga d'akin da Baby Salmah ta tafi wajen Hajaarah.

Mintuna aka d'iba tsakani sannan Innah Jumah ta shigo d'akin da casbaha a hannun ta ta nemi waje ta zauna.

A hankali aka dinga hirar da ita daga bisani ta gyara zama tace "Nifa zuwa nayi muyi magana."

Shiru duk suka yi suka maida hankalinsu gare ta sannan Baffan Asma yace "Muna jin ki."

Sosai ta maida hankalin ta ta nutsu sannan tace "Da farko haquri zan soma baku bisa ga irin rashin kyautawar dana dinga yi muku bama kamar ke Asma nasan nafi dukkan su quntata miki tun mutuwar Habi kawo yanzu shekara da shekaru don Allah badon ni ba don annabin rahma (saw) ki yafe min wallahi sharrin shaid'an ne."

A hankali kuma jiki a sanyaye Mommah tace "Innah karki damu ke uwace a gareni babu ta yanda za'ayi na guje ki ko naji zafin ki Allah ya yafe mana gabad'aya."

A hankali duk suka amsa da Amin sannan Innah Jumah ta maida hankalin ta kan Baffan Asma tace "Baffah nayi wannan tunanin ne da daddare kuma a yanzu zan sanar daku amma saida yarda da amincewar ku musamman ma shi Hamidu da zancen akan sane." Ta qarasa tana kallon Hameed da qirjinsa ya soma dukan tara tara don baya son matsala ko damuwar da za ace kuma akan sane duk da baisan me zata fad'a ba amma yasani Innah Jumah sunan ta ma matsala a gare su balle maganar ta duk da ta nuna ta tuba yanzu.

Baffah yace "Muna sauraron ki Jumah."

Saida ta gyara zamanta sannan tace "Daman cewa nayi ko Hamidu zai aure Ayaah ne tunda abun duk na gidane kuma ina son ku gane nayi nadama ta gaskiya shiyasa ma zan had'a zuri'a daku."

Da sauri Hameed ya d'aga kansa yana kallon ta cikin wani irin yanayi marar misaltuwa shi baza ka kira shi da baqin ciki ko damuwa ba haka zalika ba farin ciki bane,daga bisani ya maida dubansa ga yayar sa Asma'u wadda murmushi ko kusan dariya ya su6uce mata lokaci guda can qasan maqoshin sa ya furta wanda la66ansa kawai ta kalla ta gane "Yah Sister."

Gira ta d'aga masa tana fad'ad'a fara'ar ta lokaci guda tayi saurin cewa "Ah haba Innah waye Hameed da zai qi jinin ki ai da Hajaarah damu dukka abu guda ne saboda haka mun kar6a da hannu hurhud'u ma Innah Allah ya saka da alkhairi ya qara girma."

Baffah dake ta murmushi yace cikin tsokana "Oh su Asma'u kin bari an tambayi Hajaaran ne da kika jajirce haka."

Cikin dariya tace "Baffah na manta zumud'i da farin ciki yasa na manta ma."

Dariya suka yi gabad'aya sannan ya maida kallonsa wajen Innah Jumah yace "Haqiqa Jumaah nafi kowa farin ciki da jin dadin wannan saukowar taki da kuma wannan gagarumar kyautar da kika yi mana tabbas bamu da bakin gode miki nida yarana koda suke kema yaran kine Allah ya saka miki da alkhairi da mafificiyar Aljannah kuma ya d'orar dake akan wannan d'abi'a."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now