Part 42

265 20 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel


P5️⃣6️⃣-5️⃣7️⃣
Qarfe bakwai ta fito da sauri sauri don yau tana da presentation da kuma sauran kwantan assignment da aka basu bata qarasa ba don haka tana son shiga library en biyu ma a d'aki ta barsu don su ranar sai 12 suke da lecture.

Kamar an wullo shi ta qofar library d'in sukayi karo tayi saurin ja baya tana cewa "Hasbinallahu wani'imal wakeel." Lokaci guda ta d'ago tana kallon dawa sukai karo.

A fusace ta nuna shi tace "You again?"

Yana dariya yace "Yeah me again."

Tsaki ta ja ta zagaye shi tana niyyar wucewa yace yana saurin tare hanyar da zata wuce "Nah not too soon durlyn."

Wani kallon banza ta watsa masa tace "Abeg who's your darling?"

Dariya yayi yana kashe mata ido d'aya yace "You ofcourse."

Tsaki ta sake yi tana kallon agogon hannunta tace "Please u r blocking my damn way and am running out of time."

Dariya ya sake yi ya matsa yana kallon ta yace "Ga hanya nan Allah ya bada sa'a."

Ko kallon sa batayi ba ta wuce tana magana can qasa yanda bazai ji taba "Psycho."

Dariya yayi don duk da yanda muryar tata tayi qasa sosai dake yana da lafiyayyen kunne ya jita,ya soma tafiya yana cewa "Am gonna make sure u regret calling me dat."

Ita kam tana shiga da sauri sauri tayi abinda zatayi ta wuce ta koma class takwas da rabi ta cigaba da nazarin abinda zasu yi presentation d'in akai har zuwa qarfe tara sanda mallamin nasu ya iso suka shiga karatu sosai daga qarshe sukayi presentation d'in suka fito.

Tana fitowa ta nufi cafeteria don tayi balain gajiya ga yunwa batayi breakfast ba ta fita,ta gama zuba abincin ta biya tana zama table d'in data zaba shima ya zauna da nasa farantin.

Qamshin da taji ne na turaren sa mai maqalewa a duk inda yake yasa ta saurin d'aga kai tana kallon sa a fusace tace "Kaii ya salamullahi."  Ba kuma tare data sake magana ba ta miqe tana shirin barin gurin.

Yana dariya shi kuma yace "What coincidence,we bumped at each other da safe and we gonna eat on thesame table now what do you think?"

Yayi maganar da d'an rainin hankali,duk da hankalin ta nakan neman empty table bai hana ta sauraren abinda yake cewa ba a fusace ta juyo tana kallon sa tace "Do you really wanna know what i was thinking? Ina tunanin you should leave this table kaje ka ka nemi wani please leave my damn ass alone."

Dariya yayi sosai kafin yace "And inaga tables a nan don d'alibai akayi badon wasu zababbu ba don haka ba inda zani."

Ganin babu table available yasa ta juyawa ta zauna a harzuqe tana tura abincin da sauri don tayi ta gama tabar wajen.

Yanda yake kallon ya sake harzuqa ta amma tayi banza ta gama ta miqe da sauri ta fice ya bita da kallo yana dariya yace "She's cute komai tayi kyau yake mata."

Yana gamawa ya miqe shima ya fice daga cafeteria d'in ya nufi nasu ajin don sunada lecture a lokacin.

**********
Komai aka sawa lokaci akace sai ya iso da kad'an da kad'an kwanaki suka dinga gangarawa har ya rage sauran sati biyu lokacin da aka sa ranar bikin Ansaar yazo.

Su Hamza da M.Marwaan ne suka ququta suka yiwa amarya kayan fitar biki kala uku sai angon shima akayi masa kala biyu Iyyah ma kala biyu,da yake kuma abinci ba matsalar su bace daga Hamzan har Sama'ila Sana'ar su kenan suka kawo abinci na hidimar biki suka kaiwa gidan amarya haka nan suma anan suka bawa gidajen su da kuma ita Iyyar.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now