Part 72

263 18 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!



P1️⃣0️⃣6️⃣
Zaman su a paris sai ya sha banban da na saudiyya don wannan karon janta yake sosai a jiki kuma daya lura ita mutum ce me son tarihi sai ya biye mata duk inda yasan akwai abubuwan tarihi na qasar saida ya kaita.

Sosai ta sake dashi fiye da farko wanda ita kanta mamaki take don yanda take jinsa yanzu ya wuce yanda take jin sa da farkon auren su yanzun kam ta saba dashi sosai kuma sosai suke hira da komai saidai in an zo kwanciya bacci ne kowa ke kama gabansa don dukan su a qarshen gado suke kwanciya.

Yau sunje bakin ruwa ne sun jima a wajen sosai suna ta wasa da ruwan kawai bata ankara ba taji an watso mata shi da yawa ga snyi.

D'an qara tayi na tsoratar da tayi tayi saurin miqewa tana kallon sa.

Dariya yake sosai yana nufota d sauri ta gudu daga bakin ruwan don tsakani da Allah bata son ruwa ko misqala zarratin musamman ma na sanyi wanda ita daman can duk zafi bata iya wanka da ruwan sanyi balle idan sanyi yayi sanyi ai ko wanke wanke saita dumama ruwa takeyi.

Ganin ta bar wajen ya bita yana dariya ta qara azama sosai tayi nisa da ruwan sannan ta tsaya tana haki,yana qarasowa ya janyo ta yana cewa "Matsoraciya."

Dariya tayi tana kwanciya a jikinsa tace "Ni bana son ruwan sanyi ne,ko a gangare da sanyi ma komai zanyi da ruwan dumi nakeyi."

Jinjina kai yayi yana murmushi yana shafa bayanta yace "Sorry bansani ba ni kam sanyi baya damuna."

Gyad'a kai tayi tace "Ai to baza ka had'a muba tunda kai ka saba zuwa qasashe irin wad'annan masu d'an karen sanyi."

Dariya yayi yace "Zaki je kuma inda ake qanqara ya za'ayi kenan?"

Zaro manyan idanuwan ta tayi tana kallon sa da mamaki sosai tace "Qanqara??"

Yanda tayi ya ba shi dariya yace "Eh mana,yanda ruwa ke zuba daga sama haka itama take zubowa wata rana ma idan tayi yawa takai minus a garin har hana fita ake saboda kada mutum ya daskare."

Hantar cikin tace taji ta kad'a a ranta ta dinga ji kamar tace ta fasa zaman Uk tace zata bisu su koma nigeria amma sai ta dake bata fad'a din ba tayi shiru kawai.

Shiko sai nazarinta yake yana kallon ta da yanayin data shiga ya fahimci dole akwai damuwa amma ba yanda za ayi ai tunda makarantar su ma sunyi hutu ne nan da sati biyar zasu koma don haka ma suke da sauran lokaci har zasu yi sati a Uk kafin su koma.

Shirun da tayi ya sa yace mata suje su sha ice cream sai su wuce gida.

Dan turo baki tayi tace "Nifa sanyin nan ban cika son sa ba."

Yana murmushi yana jan hannun ta yace "Sai zafi kike so?in ma shi ne saikin gaji ba Uk zaki ba."

Dariya tayi ta fahimci abin nasa harda tsokana don haka ta dake tace "Bakomai ai zafi yafi sanyi tunda shi baya illa."

Dariya yayi ya jata suka tafi,wani Cafè suka je suka sha coffee sannan suka koma hotel d'in su saidai basu shiga ciki ba sai suka tsaya a harabar suna ta kallon mutane nata zurga zirgar su kowa da abinda yake yi abin sa abun gwanin ban sha'awa ba ruwan wani da wani.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now