Part 53

274 24 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel

P7️⃣6️⃣-7️⃣7️⃣
Tun tana iya jin abinda ke faruwa a fad'in duniya har ganinta,jinta da fahimtar ta suka d'auke mata d'if ta daina gane komai.

Bata tashi farkawa ba sai asuba sanyin asuba ya kad'a ta ta bud'e idon ta a zaton ta zata ganta a d'akin ta amma maimakon sa saita ganta a qofar gidan Lami,cikin razana ta dinga kuka tana waige waige gaba d'aya ta rasa inda zata cusa kanta taji dad'i kuka kawai take gashi ta rasa bakin magana balle ta samu ta bawa duk ma mai yi mata hakan haquri.

Tun tana sa ran kukan ta zai bada tausayi a sake ta ta tafi harta saddaqar ma babu abinda zaiyi mata.

Haka taita fama har rana ta sake qwalle mata aka abun kamar almara kuma abun mamaki tana iya ganin duk wanda zai wuce hartai qoqarin tab'a shi amma su basa ganin ta,koda ta fahimci hakan saita fara tantamar kasancewar ta mutum ita kanta don inda ita mutum ce da me zai hana su ganta.

Tsakar rana sannan aka sakar mata qafafu aka tankad'a ta gaba tayi talau ta kife bisa fuskar ta sai ga hanci ya fashe haqoranta biyu na gaba sun b'antare ta qarfin tsiya.

"Hahahahahaha." Taji an kwashe da wata mahaukaciyar dariya a karo na farko tun fara yi mata izaya tsahon lokaci ana yi sannan akayi d'if.

Ta dade a zaune a wajen fuskar ta gaba d'aya ta d'aure zogi take mata da masifa taji ance "Zaki tashi ki bar nan ko sai mun qara riqe ki."

Da qyar ta iya miqewa tana gani dishi dishi amma hakan bai hana ta zabura ba tayi hanyar gida tana addu'ar Allah yasa kada su qarawa hanyar nisa kamar yanda sukayi mata jiya,saidai adduar ta bata karb'u ba don saida takai la'asar a hanya sannan ta isa gida a jigace duk ta fita hayyacin ta ko gani da kyau bata iyawa a haka ta fad'a gidan tayi d'akinta a wahalce tana numfarfashi ta zube saman gadon ta.

************
Wata d'aya tsakani Ansaar ya samu admission a bayero university kano(Buk) zai karanta Business administration nan da nan kuwa Alh.Sa'idu yayi masa komai na makaranta ya soma zuwa abun kamar almara don bai tab'a tsammanin zai iya samun cigaba haka ba balle ya samu ya shiga babbar makaranta shikam shigowar sa binni kam sai hamdala don ya shigo ta da qafar dama Allah ya had'a shi da mutanen arziqi.

Course d'in ma Alh.Saidu ne ya sashi ya cike tunda ba wani wayewa yayi da sanin courses ba shi kuma yayi haka ne don yana ji a ransa yaron zai amfane shi nan gaba gara ya karanta abinda zai amfane shin sosai yasan kasuwanci da kyau.

Karatun sa yake cikin kwanciyar hankali gefe guda kuma suna karb'a karb'a a wajen tuqin Alhajin da wanda aka sake samowa Sani driver,duk randa baida lectures shine ke hidimar kai Alhaji ko ina harda Hajiya Abashiya in kuma yana da Lectures Sani ne saidai shi fa Alhaji yafi son Ansaar don dai ba yanda ya iya ne.

Yau lahadi ce babu makaranta tana harabar gidan tare da Da'u mai wanki wanki yake taya shi suna hira Da'u yace "Oh Dafa lelen hajiya na nan wankin nan daya ci uban wannan sau goma kamar jaririya kullum inajin kaya kala biyar take sawa."

Da mamaki Ansaar yace "Waye lelen hajiya kuma?"

Dariya yayi yace "Er Alhaji mana."

Cikin wani mamakin yace "Aa daman yana da yara Alhaji?"

Yana d'auraya yace "Yana da ita wai ita Lubna ita d'aya ce jal kamar rai."

Ansaar yace "Amma tana ina?"

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now