Part 71

251 17 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*



By:ZahraArkel!




P1️⃣0️⃣5️⃣
A b'angaren su Iyyah ita abun sai yazo mata banbarakwai don ita bata tab'a kebewa da wani namiji baligi ba saidai Ansaar shiko wannan bama ta d'aukar sa a jerin maza idan tana tare dashi d'ane a gareta don haka gabad'aya ta kasa sakewa.

Shima Abbuhn wannan shine karon sa na farko da ya kasance da wata mace ba Asma'u Mommahn triplet ba don haka dukkan su abun a wani iri yazo musu amma dake shi namiji ne dole haka ya daure ya shiga janta da hira hakan ko ya taimaka sosai ta d'an saki jiki zuwa shad'aya yace suje su kwanta.

Haka suka kwanta kowannen su na edge na gado sun bada mugun fili tsakanin su,shi yana ji bazai iya kasancewa da kowacce mace ba Asmyn sa ba ita kuwa muguwar fad'uwar gaba da fargaba ta hana ta sakewa sosai.

A haka suka kwana babu wani wanda yayi cikaken bacci a cikin su kowannen su da abinda yake saqawa a ransa game da d'an uwansa.

*** *** ***
Ga Mommah kam daurewa tayi ta cije ta zama jaruma jajirtatta don haka ta dinga maimaitawa kanta a fili "Aminatu ce er uwar mijin ki,Mariqiyar d'anki wadda ta shiga tasku da baqincikin rayuwa saboda shi ba kishiyar ki bace abokiyar zaman kice er uwar ki,bazata cutar dake ba don tana son d'anki."

Wannan abin da ta dinga maimaitawa shine ya sassauto da zuciyar ta daga zafin da ta dinga yi har ta daina kukan kuma hakanan ta tsinci kanta cikin farin ciki a washegari.

Kwana biyu suka tattara suka koma kano gabad'ayan su ana komawa kuma akaje aka yiwa su Ansaar da Iyyah passports d'insu cikin sati kuwa ya fito nan da nan ala fara processing visa d'in su ta honeymoon wanda zasu halarci qasashe biyar na duniya Saudi Arabia,UAE,Paris,USA sai su yada zango a Uk inda nan ne kuma Iyyah zata cigaba da karatun ta tundaga secondary har jami'a.

Abinda Iyyah ko Ansaar basu tab'a mafarki ba kuka sosai Iyyah tayi na jin dadi da murnar wannan cigaban.

Cikin abinda bai wuce sati biyu ba komai ya kammala suka d'aga zuwa qasa mai tsarki harda Ansaar wanda shi sati zaiyi ya wuce Uk inda zai tadda su Mommah acan don suma rana d'aya suka tashi dasu saidai su Uk suka nufa.

Sunyi ibada sosai sun zaga kuma ziyara duk inda ya kamata cikin sati guda dole ne ma ka kalli su Ansaar ka qara don har sun canza musamman Iyyah abun sai ya baka mamaki yanda ta koma d'anya sharaf sai ka rantse da Allah wannan baiwar Allah da qyar idan ta rufe ashirin cif balle talatin shi kansa Abbuh tsayawa yake yana kallon ta musamman ma idan tana bacci ya tabbatar baza ta kama shi ba ai ko cikin abinda bai wuce satin ba sonta da qaunarta suka dinga shigar sa a hankali a hankali kafin ya ankara sonta yayi masa yawa a zuci.

Ansaar ya barsu ya wuce uk inda zasu fara zuwa makaranta washegari su ukun su Mommah an sake kai kace nan suke da rayuwar su don gida guda suka sake samu wannan karon ma babba daya fi wancen girma don suna sa ran su zauna sosai tunda da Iyyah kenan.

Washegari suka soma zuwa makaranta abin su kowa da course d'insa kowa da inda zai nufa kenan amma saida suka kai Ansaar har ajinsa sannan suka raba hanya kowa ya tafi nasa ajin.

Da aka tashi ma suka kuma zuwa suka d'auko shi suka shiga nuna masa makarantar da wurare da ke mai fahimta nan da nan ya gane kan komai ya d'auke shi aka.

Mommah bata da matsala dasu Salmah ce kawai suke tare da ita a gida idan sun gaji da zaman gidan sai kawai su fito suma su zaga gari saboda haka wannan hutun kafin su Abbuh su zo ba qaramin dad'i yayi wa dukkan su ba.

***🥰***
Sati suka qara a saudiyya suka baro ta zuwa paris wadda ta ita suka fara,tunda suka sauka airport Iyyah abun ya fa d'aure mata kai a ranta tace "Sai kace ba a duniya muke ba irin wannan had'uwa haka?"

Ya lura da yanda ta sake baki tana ta kalle kalle zai ma iya tafiya ya barta,yayi murmushi ya kamo hannunta,da sauri ta juya tana kallon sa tsigar jikinta na tashi kamar kodayaushe idan ya tab'a ta.

Girgiza kai yayi ya tsayar musu da taxi yace ta shiga,ta ko shigan shima ya shiga yanda yaga tana kalle kalle kawai sai yace "Let me give little tour kafin mu fito sosai."

Murmushi tayi duk da bata fahimci me yace ba.

Ya matso ya matse ta sosai harda wani janyo ta kafin ya soma nuna mata wuraren da suke wucewa a hanya yana gaya mata inane wadanda yasan tarihin su ya fad'a mata wad'anda iya suna ya sani ya fad'a mata har suka isa wani qaton hotel wanda 5star ne a paris.

Tsawon sa da girman sa shiya ba Iyyah mamaki da tsoro lokaci guda,ta bud'e baki cikin mamaki bata ma san tace "Yanzu nan gidane Abbuh?"

Dariya ce taso sub'uce masa ya ja hannun ta ta dawo baya sannan ya lakuce hancin ta yace cikin wasa "Wannan amarya tawa er qauye ce hotel ake ce masa shima dai kamar gida ne amma na saukar baqi ko kuwa masu hutawa na cikin qasar."

Kunya ta kamata ta rufe fuskar ta tana murmushi tace "Kai Abbuh."

Dariya shima yayi yace yana wucewa da loggages d'insu "Muje mu huta na gaji."

Da mamaki tabi bayan sa tana maimaita kalmar gajiya a ranta don ita bata ga abun gajiya ba,daga mota sai jirgi sai mota amma yace ya gaji ko me yayi na gaji a cikin nan oho.

Haka ta bishi har reception ya karb'i key d'in d'akin su don tun yana saudiyya da 1 day ya kama musu don kada yazo sai yabi wani long process yana son hutawa.

"Subhanallahi." Shine abinda ta fara furtawa sanda suka shiga d'akin hotel d'in saboda tsabar tsaruwar falon full set na kujeru,gefe dinning area ne,sai can wani gefen wani d'aki ne daban,ta juya gefen ta shima wani d'akin ne wanda alamu nan ne bedroom don nan taga yayi da kayan su.

Murmushi kawai yake yana jin wani nishad'i sosai,wanka yake son shiga don haka ya soma cire kayan sa ita kuma ta sa kai zata shiga d'akin ta ganshi da gudu ta koma qirjin ta na fat fat fat,tayi saurin dafe shi tana mamakin sa ta lura tun a saudiyyan ma baya jin nauyi ko kunya kamar kwanakin su na farko ko tana zaune zai cire kayan shi abun sa.

Ta jima a zaune sannan ta miqe a sanyaye don tana son d'aukar jakarta ta d'aki abu idan badon haka ba da bazata shiga bama har sai ta tabbatar daya hama komai.

Yana fitowa yace taje tayi itama,haka sum sum ta d'auki kaya da zata canza ta shiga ya bita da kallo yana mamakin ta wato mata duk shekarun su halin su d'aya ne baya canzawa indai aka ce mace ce to macecen kawai babu wani shekaru dake banbanta su sai yayi murmushi kawai yana saqa wani abu a ransa wanda shi kad'ai yasan me yake tattaunawa da zuciyar sa harda cije gefe lips d'insa.

Haka suka zauna yayi musu ordern abinci aka kawo musu suka ci suka qoshi suna gamawa ta fara hamma yayi dariya yace "Bacci ko."

Kai ta gyad'a masa yace "To ki kwanta zan kwanta nima yanzu."

To kawai tace ta miqe ta nufi lumtsimemen gadon dake d'akin ta kwanta ko minti biyu batai ba bacci ya d'auke ta,ya zo ya zauna gefenta yana kallonta tayi wani irin fresh sai glowing take aiko kamar mai magnet a jikinta ji yayi kamar tana fizgar sa gare ta,a hankali ya kwanta tare da jawo ta jikinsa ya qwaqume ta shima baccin ya d'auke shi.

Sorry banda lafiya 2days ga abubuwa sunyi yawa ayi manage da wannan luv y'all so much and plz i need ur prayers ko yaya ne thanks.


ZahraArkel ce!

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now