Part 66

276 19 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!




P1️⃣0️⃣0️⃣
Hinde cikin kukan take cewa "Iyyah nasha hasashen bazaki aikata abinda ake danganta ki dashi ba zuciyata tasha musa haka haka zalika kullum sai na cewa baban su Hadiza ni wallahi ban yarda ba amma sai yace abinda tun kafin a haife ni ake fad'an sa ya zan musa alhali bansan sanda akayi ba a kullum nakan ce masa kamar mutum halinsa ashe d gaske ne hasashe na gaskiya ne meyasa kika zauna kika qunshi wannan baqin cikin na fiye da shekaru ashirin Iyyah akan abinda baki aikata ba?meyasa kika bari sharrin Rammah ya dinga bibiyar ki haka Haba Iyyah?"

Iyyah Aminatu tace "Kamar yanda Rammah ta fad'a ne idan da a lokacin na fito na qaryata babu wanda zai yarda tunda babu ma muhallin da zan qaryata d'in don haka shiru na shine mafi alkhairi yanzu ba gashi ba kowa yasan gaskiya kuma yaji ta yanzu waya kunyata."

Duk suka juya suna kallon Iya Rammah da Megari yasa wasu dogaran sa su kama su tafi da ita kafin a zauna ayi tunanin hukuncin daya dace da ita,da sauri Iyyah ta tafi wajen tana share kwallar ta sannan ta dake sosai tana kallon Iya Rammah tace "Baba Megari ku sake ta ku qyale ta ta tafi duk hukuncin da mu mutane zamu yanke mata bazai kai wanda ubangijin mu ya tanadar mata ba don haka kawai ku sake ta taje duniya ta ishe ta."

Megari cike da mamaki yace "To ai ba ke kad'ai ta zalinta ba bake kad'ai taiwa abubuwa ba don haka dole mu hukunta ta."

Sama'ila da tun fara wannan maganganun bai tofa ba saboda yanda gabad'aya yaji bama shida kuzarin tofawar ya matso kusa yana kallon Iya Rammah da Megari yace "Nima ina goyon bayan maganar er uwata duk hukuncin da zamuyi mata baza muji mun gamsu ba amma mu barta da Allah kawai ya hukuntata daidai da abinda tayi mana."

Ya juya ga Iya Rammah dake razgar kuka yace "Kanki kika cuta bani ba na sake ki saki d'aya biyu uku ki tafi babu sauran aure tsakanin mu sannan ban yarda ki koma gidana da sunan koma meye ba sannan idan a cikin yaran da kika haifa kinsan akwai wanda ba nawa ba ki d'auke shi ku tafi tare dashi na sallame ku."

Daga haka yaja hannun Aminatu yana jan na Ansaar yace "Kuzo mu tafi."

Duk jiki a salub'e duk suka bar wajen dasu Mommah dake bin Iya Rammah da wani irin kallo na tsana tsantsa suka barta a wajen Megari ma daya ga sun tafi kawai sai ya miqe yace ya sallami kowa ya shiga gida,ai kamar jira suke ya shige sai ruwan duwatsu Iya Rammah ta fara ji ana kiran mu jefe shedaniya mu jefe shedaniya su Lado kenan da da alamu abinda ya faru yafi kowa jin takaicin sa kamar akan sa ne abun ya faru,gudu ta fara yi amma da yake qafarta ba lafiyayya bace bata wani gudu mai kyau sannan ita dai a iya tsammanin ta gudun da tayi ya isa ace takai titi ma amma kamar wadda ke tafiya waje d'aya sam bata matsawa sai tayi wajen taku hamsin don haka kafin kace wani abu sun had'a mata jini da majina da qyar suka qyaleta suka tafi,wasu kuwa duk da hakan saida suka gaggaura mata mari saboda haushi sannan suka yi tafiyar su.

A jigace take don suma tayi amma ba wanda ya kula hatta yaranta sai Auwalu da yafi kowa jin ciwon abinda aka yiwa uwar sa duk da yaga laifin ta.

Sai cikin dare da qafa ta d'auke ya fito da abinci da ruwa yazo inda take kwance tana makyarkyata ta sanyi ya bata abinci da magani tasha yayi niyyar d'auke ta zuwa cikin gida koda da asuba ne ya fidda ta amma kamar wadda qasa ta riqe sukayi sukayi taqi koda motsawa dolen sa ya haqura yaje ya kawo mata bargo shina yayi shimfid'a ya kwanta a wajen saidai a wannan daren saida ya gwammaci bai taya ta kwana ba saboda bala'in daya gani.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now