35 Qaddara ce sila

311 13 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

Don Allah 'yan uwa ina tsananin buqatar adduar ku akan lamurana don Allah ku sani a addu'ar ku Koda sau daya ne Allah ya yaye min ya sauqaqa min nagode.

By:ZahraArkel!



Page48-49
•••Washegari da safe wajen qarfe goma M.Ladan da maigari wanda M.Marwaan ya taso shi dole sai 'yan sanda mota guda suka shiga laluben su Lado a garin anci nasarar damqe shi Ladon da abokansa biyu wad'anda ba a same suba aka damqe iyayen su aka tafi dasu yayin da gefe guda kuma labarin mutuwar Ansaar ya karad'e qauyen kamar wutar daji.

Bayan an gama kame kamen ne M.Marwaan yace a tafi dasu zai biyo su daga baya tare da iyayen wad'anda aka samu su Lado kenan tunda su ba laifi sukai ba ba a zuba su a motar shiga ba biya fita da Allah ya isa ba.

M.Ladan ya jashi gefe ya tambaye shi ko Ansaar da gaske ya mutun?

Murmushi yayi yace "Yana nan da ransa saidai saran ya shiga naman sa sosai saida aka yi masa d'inki sosai don haka bai farko ba amma ko d'azun ma da safe munje nida mai d'aki na mun kai musu abinci tace kuma ya farka cikin dare amma an sake masa allurar bacci."

Jinjina kai yayi cike da jin dad'i marar misaltuwa yace "Alhamdulillahi mun godewa Allah."

Cike da jin dad'i M.Marwaan shima yace "Shine abun godiya saidai fa yaran nan mun shirya shiga kotu gaskiya don baza mu bari ba tunda baida gata bazai zama kowa kuma ya zuba musu ido ana zalintar su irin haka ba."

Kai ya jinjina cike da jimami yace "Niko banqi ta taka ba amma dai inada shawara."

M.Marwaan ya maida hankalinsa yace "To inaji."

Ya sake gyara tsaiwa yace "Me zai hana Marwaanu tunda maganar nan ta had'a da masu sarautun gargajiya ne muje wajen dagacin gezawa?na tabbatar zaiyi adalci fa."

Shiruuu yayi yana nazari a ransa yana ayyana shima dai don ya dage ne shine kuma mai qwarin gwiwar cewar za'aje kotun amma ko kud'in d'aukar lauya basu dashi kuma idan sun matsa ya zasu yi su sallami lauyan da ya jagoranci nemawa yaron su adalci bayan haka kuma idan aka zo ba ayi nasara bafa da wanne zasu ji wannan kuwa ba shari'ah ce irin ta kotu ba qila ko yaya ne indai ba azzalumi bane zai musu adalci ai don haka yace "Mallam zaiyi mana adalci kuma?"

Kai ya jinjina yace "Inada tabbas akan wannan domin shi ba irin kowanne sarkin gargajiya bane yana da mutunci da girmama mutane da kuma sanin ya kamata."

M. Marwaan yace "Shikenan sai a juya akalar maganar zuwa wajen dagacin bari naje na shirya nima saina biyo tanan mu tafi."

"To to ba laifi nima bari naje wajen liman na sanar dashi halin da ake ciki tunda a shirye nake." Suka yi sallama suka rabu kowanne yayi gidansa.

A tsakar gidan sa ya tadda Hansai ta jawo Saro tana duka da zagi kamar ta samu jaka su Bukar na gefe suna zugata kamar filin dambe da gudun sa ya qarasa ya karbe ta yana kallon Hansai cikin mugun 6acin rai yace "Wallahi wallahi Hafsatu ki kiyayeni bana son shashanci da rashin hankali kinji ko?"

A qufule itama tace "A samu shashashan tsakanin mu da ita kuma naji dadi da ma ya mutu ba sai muga ta qaryar so ba da kukan rashin kunya."

Da Sauri Saro ta dubi mahaifin ta da alamu tambayar sa take da idanu da gaske ne amma bai lura ba cike da takaici yace "Albishirin ki ki kwantar da hankalin ki a yanzun nan da kike ganina wajen su zani Ansaar na nan da ransa bai mutu ba kuma aure a yau zan d'aura shi ki kuma jirayi dawowa ta."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now