27 Qaddara ce sila

312 18 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!


Page 3⃣6⃣-3⃣7⃣
•••Yanda ya saba gaishe ta da girmamawa ya gaida ta sannan ya zauna suka shiga hira sosai don jinta yake kamar yayar sa haka nan ita kanta kallon qani take masa tasha gaya masa tana da qani Muttaqa kansu d'aya kuma kusan shekarun su ma zasu yi d'aya tana ta son had'a su Allah baiyi shi Muttaqan yazo ba ko a yanzun ma da suke hirar Ansaar na wasa da su Muhsin saida tace "Kaga kuwa wancen satin da mukaje gida nake sake gayawa maman mu da Muttaqa labarin ka shine maman tace da anyi hutu insha Allahu zaizo mana koda sati ne kuga juna tunda na dage saina had'a abotar nan."

Yana dariya yace "Wallahi Aunty Halimatu nima na matsu naga Muttaqan don kinsan ina son nayi aboki ban ta6a yin abokai ba."

Cike da tausayawa yanayin da ya tashi da son basarwa tace "To ai ka godewa Allah Ansaar ba duk aboki ne na gari ba wasu abokan ba abinda sukeyi sai 6ata abokan su kar ma kayi fatan yin abokai ko nan gaba barkatai."

Guntun murmushi yayi yace "Ni Aunty a garin nan waye zai yi aboki dani har da zan yi su barkatai nidai ina son Muttaqa ya zama abokina saidai ina gudun kada a zuga shi a garin nan." Ya qarasa da mutuwar jiki.

Halimatu sarkin tausayi idon ta har ya ciko da qwalla tace "Babu mai zuga shi tunda ma dai shi ba d'an garin nan bane waye zai sanshi balle ya zuga shi kuma kaima baka ganin baban su Muhsin ne waye ya zuga shi ya d'auka."

Cikin jin dad'in maganganun ta yace "Hakane babu mai zuga shi kam Allah yasa kar Muttaqa yayi abokai irin su Lado."

Sarai ta gane yaron da yake fad'i don haka tace "Amin." Tana goge guntuwar qwallar ta.

A hankali cikin salo ta dinga juyar da akalar hirar tasu ta koma kan Iyyar sa nan kuma ya gaya mata halin da suke ciki da tsahon lokacin da suka d'auka a cikinsa.

Jinjina kai tayi tace "Inaga Iyya duk yanda akayi an yi mata sihiri ne don haka zan baka addu'o'i ka riqa mata tana sha tana wanka dasu in sha Allah zata dawo dai dai."

Cike da jin dad'i ya amsa ta da to,nan ta fad'a masa addu'o'in da yanda zaiyi mata dasu dama dabarun da zaibi ta riqa amfani dasu da kanta batare da ya wahala ba.

Haka akayi yana dawowa ya karanta addu'o'in cikin ruwa da ganyen magarya ya had'a mata ya tace don kar ta gane ya zuba cikin abinda suke zuba ruwan shan su sannan na wankan ma tunda shine yake had'a mata ruwan wankanta sai ya dinga d'an zubawa kad'an a cikin ruwan wankan nata don bai san ya zaiyi mata ba duk da ayoyin qur'ani ne amma sai ya dinga mata dabarar wankan a kewayen da band'akinsu yake da sunan zaiyi aikin band'akin ya gyara inda ya 6urma cikin satin.

Haka ta yadda amma a hankali ita kanta ta soma jin wani irin chanji a jikinta wanda ta mance yaushe rabon da taji irin wannan yanayin.

Kafin cikar sati da soma mata maganin tuni duk wani abu dake qudure ta ya nisanceta saidai lokaci lokaci takan ji qunci shima sosai Ansaar ya dage mata da addua a ruwa tana sha kafin kace meye wannan duk wani qullin da Iya Rammah tayi shekara da shekaru tana qullawa ya kwance tas.

Tuni ta dawo hayyacin ta da nutsuwar ta tada wadda ya santa da ita tun yana mitsitsi yayi matuqar farin ciki da murnan hakan.

***********
Aseep na kwance cikin kujera mai cin mutum uku Areep da Hamdiyyah suka shigo falon suna ta er hayaniyar su da suka saba yana jin shigowar su ya miqe ya doshi d'aki yana ta wani fuskewa.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now