Part 61

229 16 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*


By:ZahraArkel!



P9️⃣2️⃣-9️⃣3️⃣
Saida aka dad'e ana mata fifita kafin ta dawo hankalin ta tayi wa Areep dake gabanta quri da ido bako qiftawa so ta ke ta gano banbancin sa da Ansaar babu bata gani ba.

Haka ta koma gaban Aseep saima taga yafi mata kama da shi sosai don shi Areep baida d'aurewa irin na Ansaar da Aseep kawai sai ta fashe da kuka tana fad'in "Na rantse da Allah basu da banbanci wallahi Allah."

Cike da takaici Aseep ya miqe yana cewa "Ke bama son shirme kinji idan gamo kikai da me irin kamar mu saiki gayawa zuciyar ki babu irin mu mu biyu ne mahaifiyar mu ta haifa bata taba bamu labarin muna da wani d'an uwa ba...."

Hamdiyyah ce ta qaraso wajen da sauri tana d'agawa Aseep hannu dole yayi shiru da maganar da yake,ta tsugunna ta dafa kafad'ar Lubna tace "Kina da koda hoton wancen ne?"

Kad'a kai tayi ta soma laluben jakar ta ta zaro wayarta ta kunna hannunta na rawa ta shiga neman gallery d'inta a ciki ta nemo hoton Ansaar duk da baiyi tartar ba don daga nesa tayi zooming ta d'auki hoton ta bawa Hamdiyyah.

Ita kanta hannunta na rawa ta karb'a sosai ta dinga zooming hoton da tsananin mamaki da tunanin waye wannan kuwa,da sauri ta sake d'agowa ta kalli Lubna tace "Ina yake yanzu a ina kika sanshi?"

Cikin kuka tace "ya gudu daga gidan mu saboda nace ina son shi,bansan garin su daman driver ne a gidan mu."

Cikin mamaki Aseep da wayar ke hannun sa yace "To waye shi?menene sunan sa kuma inane garinsu ko gidansu?"

Lubna tace "Sunan sa Ansaar kuma ance d'an qauyen gezawa ne amma ba wanda yasan sunan asalin qauyen nasu."

Areep ya maimaita sunan "ANSAAR?"

Aseep kuma cike da mamaki yace "Gezawa?to meye had'inmu da gezawa meye had'in mu da yaron nan kuma ga dukkan alamu bazai wuce sa'an muba."

Maimuna da tun fara maganar bata ce komai ba saboda mamaki tace "Ku tashi mu tafi gida Mommah ce kad'ai zata iya warware mana wannan al'amarin."

Da sauri Hamdiyyah ta tura hoton ta bata wayarta sannan sukayi sallama da Hajiya mariya babu shiri suka tafi suka barsu da tsananin mamakin abinda ke faruwa don ya d'auke kan kowa.

Suma a mota kowa mamaki ya hana shi magana hatta Areep uban en magana yau gum kake jinsa ya kasa cewa komai.

Suna zuwa gida tun daga qofar falo Hamdiyyah ta dinga kwala kiran Mommah da sauri suka fito da Abbuh dake shirin fita shima don bai dad'e da dawowa daga tafiya ba suna ta shirin komawa abuja inda babban company d'insa na qarafa yake suna shirin fara qera motoci da kansu ne suka kafa a abuja shida Hameed.

Da hanzari Mommah tace "Meye haka Hamdiyyah meyasa bakya girma ne."

Da sauri ta lalubi hannunta ba tare data kula fad'an da take mata ba ta damqa mata wayar tana cewa "Ki kalla Mommah."

Da sauri ta d'aga idonta ya sauka kan screen na wayar sai ganin ta sukai yaraffff ta zube a wajen kamar bata numfashi.

Duk sukayi kanta suna jijjiga ta cikin masifar da bai tab'a mata ba ya dubi Hamdiyyah yace "Me kika nuna mata meye haka wanne irin hauka ne wannan."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now