Part 24 Qaddara ce sila

292 21 1
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.

*RAYUWAR FATIMA da NABEEHA yasa na gane cewa QADDARA CE SILAr data sa mutane ke gane lallai cewa ANA BARIN HALAK....ko don kunya*

By:ZahraArkel!

*Ayi min afuwa saboda jina shiru da akayi na kwana biyu wannan ya faru ne sakamakon rashin lafiyar dana sha fama da ita kuma har yanzun dai sai addu'a ina fatan zaa samu marasa lafiya a addua.*

_Page28-29_
•••Babu tafiya tsakanin qauyen su d Gezawa don haka nan da nan suka isa garin har ko qofar gida mutumin daya d'auke su ya kaisu.

Saida ta sauka tana shirin juyawa mutumin yace "Baiwar Allah."

Ta juyo tana kallon sa ba tare data amsa ba ya cigaba "Ki dage da addua akwai kyakkyawan sakamako ga masu haquri."

Daga haka kawai ya buga babur d'insa ya tafi,cike da mamaki take binsa d kallo har lokacin da su M.Marwaan suka tsaya ya sauka mai babur d'in ya juya don tun a gezawan sukayi ciniki ya biya su shiyasa wancen bai jira shiba.

Ya sauko da kayan hannun sa yana kallon ta ya qaraso inda suke tsaye.

A hankali muryar ta ke fita cikin sassauqan sauti tace "Bani da bakin gode maka saidai nayi maka addu'ar Allah yayi maka sakayya da aljanna mafi girma da d'aukaka idan badon kai ba qila da tuni na mutu nabar yarona cikin mummunan yanayi saidai idan Allah ne ya raya shi."

Kansa ya gyad'a kawai yace "Ya kamata kema ki kawo qarshen wahalar da kuke ciki keda yaron ki."

Cikin mamaki tace "Ta yaya zanyi hakan.?"

D'an shiru yayi na wajen minti guda yana kallon ta kafin yace "Ki sanar dasu mahaifin sa ko kuma ki kaiwa mahaifinsa shi."

Wani busasshen murmushi tayi ta tsaya tana kallon sa tsahon lokacin da shi kansa saida abun ya bashi mamaki don bata taba kallon sa haka ba tace "Idan mutum nason shan tsinkar mangwaro daga bishiyar sa zungurar d'an yake don d'an ya fad'o buqatar sa ta biya amma a fakaice bishiyar yake tab'awa har ma wani sa'in yayi mata asarar ganyayyakin da basu ji basu gani ba wataran mangoron ma d'anye yake fad'owa ya tafi ya barshi ba tare dya d'auka ba." Daga haka ta juya ta bar wajen zuwa cikin gida.

Da ido kawai ya bita yana jujjuya maganar tata ba tare daya gane me take nufi ba ya bawa Ansaar kayan yace ya shigar musu dasu ciki.

Yaron ya d'auki abinda zai iya ya kai ya sake dawowa ya d'auki ragowar ya tafi.

Shima M.Marwaan tafiya yayi kawai yana tunanin wanne irin zance ne take yi na mangwaro shida kawai ya bata shawarar sanarwa da 'yan uwan ta mahaifin yaron ta ko don ta samu sauqi a rayuwar ta da masifar da take ciki harda shi yaron nata.

Tunanin nasa ya yawaita ya kasa gano meye ainihin abinda take nufi don haka kawai ya share zancen da yi musu addu'ar samun sauqin lamarin nasu.

Tana shiga kai tsaye tayi d'akin su tayi kai tsaye wanda an janyo shi amma ba a rufe yanda ta saba rufewa ba ta kuma san Ansaar ne zai janyo d'in.

A yanda taga d'akin anyi bincike sosai saidai babu wani abun arziqi da za a samu don haka tayi d'an guntun murmushi ta kwanta a gadon tare da lumshe idanuwanta.

Ansaar daya shigo da kayan yace "Iyyah mallam yace na kawo miki."

Ta jinjina kanta da qyar tace "Tura su qasan gado zan gani inna huta."

Tas ya tuttura su kamar basu shigo da komai ba harda bread d'in yana gamawa ko zama baiyi ba Iya Rammah ta fad'o d'akin kamar an harbota.

A tsorace Aminatu ta miqe zaune tana kallonta qirjin ta na bugawa da sauri da sauri.

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now