Part 47

267 20 0
                                    

QADDARA CE SILA!😢
🌍 *HAJOW* 🌍
🌍*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*🌍
_(United we stand,our aim is to educate,entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)_

Facebook:ZahraArkel/Hakuri da juriya online writers.
Wattpad:ZahraArkel.



By:ZahraArkel


P6️⃣4️⃣-6️⃣5️⃣
Da sauri ta d'ago ta tana fad'in "Yanzu Saratu al'ada ce haka ko kuwa 6ari ne na cikin da bamu san da shi ba?"

Cikin kuka ta qanqame ta sosai tana cewa "Nima bansani ba nima bansani...." kukan yayi yawan daya sa ta kasa qarasawa.

Yanda jinin ke fita ta qasan ta shi ya qara tsorata su dukan su da sauri Iyyah tace "Kai Ansaar d'auke ta mu fita ko shaka tafin can mu kaita kar ta mutu."

Da sauri ya d'auke tan suka fito a tsakar gidan suka yi kacibis da Atiku ya haske su da fitila yana cewa "Waye nan."

Ganin su yasa yace "Subhanallahi menene haka?"

Iyyah tace "Jini ne ya b'alle mata zamu kaita ko shaka tafi ne."

Da sauri yace "Aa ga Lanto nan kusa da wajen ta kuka kaita ai in b'ari nekinga zata gane zata san me zatai mata tunda dare yayi."

Kai ta girgiza sannan tace "Aa gara muje wajen wad'anda suka karanta." Daga haka suka fice zuwa shakatafin garin inda basu sa ran samun kowa ba amma dai bahaushe yace motsi yafi la6ewa.

Koda suka je hasashen su ya zama gaskiya babu kowa d'in kuwa cikin sa'a dai sai ga wani Nurse ya mance wayar sa da yayi aiki da ita da safe ya dawo d'auka ai ko suka riqe shi da roqo Iyyah harda kuka don zuwa lokacin ta soma galabaita jinin don kansa ma ya tsaya sai murd'awar ciki kawai take fama dashi.

Da sauri yace ya shimfid'ar da ita ya gani menene nan yai dube duben sa ya tabbatar musu da 6ari ne amma ta zubda jini da yawa duk da Allah ya taimake ta cikin ya zube kuma da alamu babu ragowa amma zai bata taimakon gaggawa zuwa da safe sai su kaita can gezawa a duba ta dakyau.

Da to suka amsa masa suna masa godiya,nan dai yayi mata 'yan abubuwan da zai mata ya bata allura sannan yace su tafi babu komai in sha Allahu.

Haka suka koma suna zuwa Iyyah ta d'ora mata ruwan wanka tana zaune gaban wutar har ya dahu ta had'a mata ta kai mata sannan ta koma ta kamo ta suka je har band'akin sannan ta qyale ta yai wankan tana jiranta har ta gama ta fito da ita ta maida ta d'akin su ta musu saida safe ta fito cike da fargabar abinda har ya tsorata Saratu yasata 6ari.

Shi kansa Ansaar yaji wani irin qunci duk da basu san da cikin ba amma ransa yayi matuqar b'aci da zubewar sa kuma take ya sawa firgitar tata alamar tambaya saidai sam bai mata ba a lokacin yadai qudurce sai ya tambaye tan idan ta samu lafiya sosai a lokacin kam lallab'a ta yayi har tayi bacci sannan shima ya kwanta.

Washegari da sassafe suka fita zuwa Gezawa don samun ganin likita akan lokaci sunko ci sa'a don sune na biyar a layin suna zuwa Ansaar yaje ya yanki kati ya barsu a layin.

Suna zaune layi yazo kansu suka miqe amma Iyyah saita noqe tace suje bakomai.

Suna shiga likitan ya bisu da kallo koda yasan auren wuri irin na qauye kam su wad'annan sai yaga qanqantar su tayi yawa don haka yace tun kafin su zauna "Kai mijin tane ko yayanta?"

Murmushi yayi wanda ya fito da tsantsar kyan sa da kwarjini da wata irin haiba ya gyad'a kai yace "Mijin tane ni yallab'ai."

Jinjina kai kawai yayi yace "To bismillah ku zauna."

Suka zauna ya soma tambayar Saron me ke damunta nan ta fad'a masa ya miqe yace ta kwanta kan gadon dake office d'in ya duddubata yayi murmushi yace "D'aya ya fita d'aya yana nan."

QADDARA CE SILA Where stories live. Discover now