part 17

52 5 0
                                    

moonlight✨

Dishes kalakala wata baturiya tashigo dasu, ajjemusu kowa a gabansa, hade da juice dinsa.

Tananan tinda tagama bayanan Bata sake Magana ba,se wayar ta da ta dauka tana dannawa

Duk abinda take Ashraff na lura da ita,wani irn farinciki ya tsinci kansa,he very proud of her today

Duk wanan bakinciki da aka kunsan masa dazu yamanta dashi,kallan ta ma kadai farinciki take sashi, ba Wanda ya lura da wanan Dan murmushin dayake

Imran ma da yakafe ta da Ido kamar ze cinye,ita kadai ta lura da wanan kallan dayake mata, shiyasa duk tabi tadagu sugama, kowa yakama gaban kansa.

Dagowa tayi suka hada ido dashi wani lafiyayyen murmushi yasakar mata,itama kwakwalo nata murmushin tayi ta mayar Mai,
Duk wanan Abin da Ake akan ido Ashraff, wani kololan bakin ciki ne yaziyarci zuciyar Shi lokaci guda,besan lokacin da yafasa glass cup din, dake hannunsa ba dayasha matsa,

Kowa hankalinsa kanshi yadawo ganin besan abinda yayi bama, dan tin wanan lokacin yarufe Ida nunsu,wani mugun kishi ne yaziyarci zuciyar sa,Gani yayi inbeyi Hakan ba ze iya hada Su duka yamusu mugun duka Har se sun fada mai ma,anar murmushin da sukai.

Hannunsa ne Yake fitar da jini sosai,tsabar kishin dake ibansa besan Ma yaji ciwo ba, kanshin tiraren tane yadaki hancinsa, sundane akansa suna Magana amma besan sunayiba

Harseda yaji wanan kanshin,saboda yasan banda Aisha,deeje kannansa  mutun dayace ta ke sa wanan tiraren Khadijat kenan, a kullin kuwa duk abinda yake yaji wanan kanshin tiraren seya tsaya da abinda ya ke ya rufe idonsa,wani nutsuwa Yake samishi
Baze mantaba,ada kafin Sutafi karatu Russia,bawanda yakai Shi shiri da deeje,ba ashiga tsaka ninsu,kullin tana wajansa, tin haihuwar ta Allah yadaura Masa santa,kwana daya ne tsakaninta da Aysha,tinda aka haifeta Yana gidan Abba har Ammi tagaji tabisa da kayansa,
Bawanda ya Isa tadauke ta,sede duk Wanda yazo yakalleta,tana hannunsa yayi Kane Kane kamar wata babynsa, harfada suke da  hajja kakarsu ta Yola kenan,itama basa shiri shiyasa take cemai mebakin hali,bawai rashin shiri na fadan Nan ba a,ah irin de na jika da Kaka,dan megida na take cemai seran da Yan mugun halin nasa yatashi suke fada
Haka ma Abdul,kullin Yana wajan Aysha, daidai da kwana days inbesata a Ido ba baya iya bacci, sede yayi ya kuka akaishi wajan babynsa.

Ashraff ne yafara sawa khadijat deeje,harsunan yabita,yanakiran ta da deeje ta, tanasan sunnan saboda yayanta ne yasa mata baka Isa kakirata da Khadijat ba,har makaranta deeje akecemata,sede na littafi

Suntaso gwanin sha,awa,kullin tana makale gurinsa,har wanka ma sede tace shi zemata,inyamata wanka tagyara Mata dogon gashin kanta,Har kalaba yake Mata

Hakan Yana yiwa iyayen Dadi yadda Yayan suka taso suna san junan Su.

Abdul ne yace bross bazamu je shopping ba kuwa,inasan insaiwa babyna tirare ne.

Kamar kashiga raina,kwarai wanan shawa ce me kyau,amma Kana ganin Su daddy zasu banmu muje mukadai@ashraff
Zasu banmu amma se sun hadamu da driver@Abdul

A wanan lokacin ashraf Yana da shekara 17 Abdul kuma15, su deeje Kuma 7year

Daddy suka roka akan yabarsu suje shopping da kansu, dakyar yabarsu seda yahadasu da driver,

Wanka suka musu suka shirya Su tsaf cikin wata pink gown me shegen kyau komai iri daya,rebon Din dasuka kama musu Kai Ma iri dayane,🤗gwanin sha,awa kamar wasu Yan biyu

Suma haka matasan, English wear sukasa bakin wando rigar duka iri daya blue colour

Kowanne yarike hannun tashi babyn se cikin mota,
Wani babban store sukashiga.  Kana ganin wanan gurin Kasan se masu Shike Shiga,
Siyayyanta sukai sosai dan sun kwashi kaya kamar na Amutu baynsu kawai suke kwasar wa kaya

moonlight 🌒(Hasken Wata)Where stories live. Discover now