𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>
https://my.w.tt/U2ZCTqQj4ab
ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...Bismillah Rahmani Raheem
0️⃣2️⃣
"Taya za a ace min na auri ugly girl. Me zanyi da mace munmuna irin Sidrah yarinyar da bata wuce Jaririyar ba. Idan na yarda na shiga Lazza a daure." Ya kuma kaiwa kofar duka, tare da make kanshi. Yana wani haki dan masifa, a fusace ya saka kayan shi ya fito daga dakin.
Tsakar gida ya fito, yana kallon yadda yaran gidan kowa ke shige da fice. Gyara zaman hular kan shi yayi tare da nufar cikin gidan, duk abinda ya gani a gaba shi ball yake dashi. Ba tare da ya damu da koma meye ba, yana isa kofar da zata shiga da shi tsakar gidan su, ya ja tunga ya tsaya. Tare da zabgawa Hasnah wani irin kallon banza, sannan ya kauda kan shi, ya taka a hankali isowa inda Hajiya Surayyah take soyar kosai. Ya gyara zaman facing cap din shi yadda zai kafta rashin mutunci a silale ba tare da ya kalli fuskar kowa ba. Gyaran muryan yayi duk yan kanen shi suka dare, tare da komawa can gefe suna zare ido. Domin sun san shi hukuma ne, bai da mutunci ko na miskala zarratin, bayi da hakuri kamar rina haka yake, fushinsa yafi na mayunwacin zaki, idan yana yinka duk duniya babu wanda ya isa yace baka kai ba, haka idan ba ya yinka babu wanda ya isa yace kayi balle yayi ka, wato Aamil ruwa biyu ne..yana da sassayar hali, kuma yana da baudaddiyar hali, yana iya zama na tsawon watanni bai yiwa kowa magana ba, idan kuma aka kuskura yana gida yara suka cika shi da Hayaniya zai kama yaro yayi ta bashi azaba kamar yadda suka mishi. Mutum ne mai mugun don abu me kyau. Sai gashi ya kasance gidan su bakake ne! Musamman Familyn su.
Shi kuma ya kasance ruwa biyu, Mahaifiyar shi baturiyar Amurka, mahaifin shi bahaushen hadeja. Aamil zai iya juya harshen sa ya dai na magana da kowa cikin harshen Hausa, sai English ba tare da yaji ko dar ba. Sannan yana iya zuwa kofar Church ya zauna, duk bala'in da Christian zasu mishi ba zai tashi ba sai lokacin da yaji a ranshi ya tashi zai tashi.
A duniya ya tsani mutane uku! Baba Mero wacce suke kiranta da Hajiya. Sai Yaya Hindatu, wacce suke kiranta da Goggo hinde, sai Hajiya Surayyah wacce suke kiranta da Hajiyar mu. Dukkan su da sunan su yake kiran su. Sai dai Hajiya Uwani wacce ta kasance matar Alhaji Ma'aruf ta biyu, sai Amarya shi wacce suke kiranta da Hajiya Amarya.
Alhaji Ma'aruf yana da mata uku cif, Hajiya Surayyah uwargida sai Hajiya Uwani wacce take Binta, sai Hajiya amarya wacce take karama, A gidan Sun ware Hajiya Uwani basu yi da ita, gashi itace kusan Alhaji Ma'aruf yake ji da ita, domin itace take jibance da al'amarin Aamil kasancewar ita tayi karatun boko da na addini, sai ya zama na tana kokarin ganin ta karkato da hankalinsa kan karatu. Hajiya Surayyah da Hajiya Amarya wacce sunanta Karimah. Basu da mutunci. Kuma suna tare da Yaya Hindatu da Hajiya. Yanzun haka gidan cike yake da yara Domin wani irin haihuwa ake kirin na gasa. Idan wannan tana da ciki toh Insha Allah ko Shayarwa kike sai taje ta kwaso ciki.
Sabida jahilci, idan ka cire Hajiya Uwani wacce take tsarin iyali. Saboda tana koyarwa a jami'ar jihar Jigawa,kuma tana yawan tafiya course. Dan haka ta cewa Alhaji Ma'aruf.
"Yallabai! Zaka yi hakuri gaskiya, bazan takura kai na da haihuwa akai akai ba, sabida ni ma'aikaciya ce, kuma ina yawan tafiya karo ilimi, kaga ba zan iya tara yara ina barin su a gida babu kulawa ba, dan haka zan iya daukar lokaci zuwa lokaci kafin na haihu."Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya riko hannunta, ya ce mata.
"Babu laifi! Nima da ace wadancan zasu bani hadin da mun samu tazarar Haihuwa, domin Kinga Karimah sai da aka min magana a haihuwar Yusuf, aka ce mahaifar tana bukatar kulawa da hutu. Da kaina na kaita aka bata maganin da zata na sha na wasu watanin, amma kawai wata biyar sai naji wai tana da ciki, wallahi abin ya dame ni, kuma ba kome ya kawo haka ba. Sai kishi tunda taji Surayyah na da ciki shi kenan, magana ya kare."
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
RomanceThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...