𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
https://my.w.tt/2G68wXrRabb
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮Bismillah Rahmani Raheem.
#Alhini
0️⃣8️⃣Bude wasikar Alhaji Ma'aruf yayi cike da bakin ciki zai karanta Alhaji Ahmed ya kwace wasikar a hannun shi.
"Kayi hakuri!"
"Ahmad! Allah Ya Shirya mana Zuri'ar mu, Amma kasan Aamil ya tozartani!""Ka gama kome! Tunda ka nima mishi shirya, Allah ya tsare shi duk inda yake Allah ya duba Alamarin shi"
"Ni ya tozarta! Insha Allah aure babu fashi bazan zarga mata igiyar shi ba, amma tabbas dashi za a daura auren nan duk ranar da ya dawo. Mutumin banza mara kirki."Bai kuma magana ba ya fita, ya d'ago kan tare da cewa.
"Ahmad me zancewa Haliru? .me zan gayawa yan uwana, da wani fuska zan fuskance su? Yaron nan ya kunyata ni saura kwana uku bikin ya tsalleke yayi tafiyar shi kaji yadda nake ji kuwa?""Kayi hakuri! Yayi laifi amma ka bishi da du'a'i, Allah ya shirya mana shi" inji Alhaji Abubakar, gyada kai yayi cikin jin tausayin kan shi, domin duk inda ake niman mara kirki Aamil ya kai.
Kallon Garzali yayi driven shi yace mishi.
"Kai ni gida!"
Cikin tsananin tausayin, Abokan shi suka yi sallama dashi, ya nufi gida. Tun a hanya yake rike da kirjin shi. Kwalla na zuba daga idanun shi. Ba kuka yakewa Aamil ba tausayin Maraicin Sidrah yake, ya kuma san gidan shi ba zai yiwu ya dauko ta ba. Domin Idan Hajiya Uwani bata nan zata zama abin tausayi.Har suka isa gidan shi da yake bayan gidan gwamna, ya fita a hankali, ya shiga cikin gidan. Ya samu mata anata hidimar suyar cincin, kallo daya Hajiya Uwani tayi mishi ta fahimci yana cikin tashin hankali, dan haka yana shiga dakin shi ta bishi.
Zama yayi, ta juya tare da dauko ruwa ta zuba mishi a glass cup, yasha sannan ya kalleta da idanun shi da suka cika da kwalla yace.
"Aamil ya tafi! Ban san me zanyiwa Yaron nan ba, ya fahimci gatar da na mishi, ya tafi ya bar ni da kunyar mutane, meye na rage shi da shi?"Cikin nutsuwa sannan tace mishi.
"Ka dauki haka matsayin kaddarar mu, Allah yana sane dashi da kuma mu, muyi mishi Addu'a a duk inda yake, kar mu watsar da Al'amarin shi. In yaso sai a dakatar da auren shi kafin nan yarinyar ta kuma girma, Yanzun ba zamu daukota ba, sai nan da wani lokaci.Domin idan muka daukota zai zamana zata yi ta walagigi a cikin gidan nan, dan haka ka barta Insha Allah zai dawo kuma zai amshi tayin da ka mishi da hannu bibbiyu. "
"Toh ya zanyi? Me zan faɗa musu a fahimce ne, dan kowa zai ga kamar na barwa Aamil daman yayi abinda yake so ne!" Ya faɗa a raunane,
"Duk wanda ya zargeka, bai san me ake kira tarbiyya bane, domin ai kayi ƙoƙari, Insha Allah Ubangiji zai dube ka da idanun rahama ya duba Alamarin ka."Sosai take gaya mishi magana masu taushi da dad'i, har ya sata ta kira sauran matan ya gaya musu, auren babu Aamil an d'aga nashi. Sun sha jinin jikin su. Suka yi ta kame kame, ko zasu ji me ya faru amma basu ji ba.
Ya kuma je dakin Mahaifiyarshi ya gaya mata an fasa auren Aamil dan haka ta sake guɗa. Tare fadi,
"Ga irin ta nan, ka haifi d'an da ya juya maka baya, tirr da ni ne na haife shi sai na tsine mishi albarka""Hajiya ba zan iya tsine mishi ba, tunda ke da kika haife ni baki tsine min ba, akan me zan tsine mishi.!" Numfasawa yayi cikin damuwa sannan ya cigaba da cewa.
"Hajiya lalacewar da Aamil yayi bai kai na wasu yaran ba, amma kuma a haka iyayen su suke jingina kome su rungume su.
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
RomanceThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...