Kayan aure6️⃣

497 83 20
                                    

https://my.w.tt/JAgNlnN98ab

𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

     ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
      
        ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮

Bismillah Rahmani Raheem

#Kayan aure
0️⃣6️⃣
"Alhamdulillah! Ya zanyi? Na kasa fahimtar kome akan Hauwa, duk abinda zanyi dan ita nayi amma sabida son kai tayi tafiyarta, shi yasa ban bi bayanta ba. Ba wai!"   Katse mishi magana Alhaji Ahmed yayi cikin nutsuwa yace mishi.

" Baka da wani excuse! Domin kuwa da saka hannunka kome ya faru, kai da kanka ka gaya min kasha dukarta, amma haka bai sanya ta bar ka ba,karka manta tunda ka saka hannu a jikinta kimarka ta fara raguwa, a hankali tana hakuri da kai baka fahimci tsawon lokacin da ta dauka tana share kwalla ba.

    Ni da kai Mahaifinta yaƙe gaya mana cewa. Ba zaka iya rike ta ba, dan ya rene ta da SOYAYYA ce,ya rene ta, ta yadda babu abinda ta nima ta rasa, haba Ma'aruf. Wai yaushe ka zama mara kirki ne? A ranar da abin zai faru, kake gaya min baka san tana ajiye da dukiyarta ba, sai da kazo zaka fita niman aiki.

   Ta ciro ta mika maka, sannan ta kuma ce maka bata jin dadi, kai kanka kayi imanin ba zata iya tafiya ba a rana, yarinyar da muka zo da kayanta sama da kwati bakwai sai da aka wayi gari , rigar da take sawa babu maraban shi da ta almajirai, sannan kace ta gudu ne dan tana da dukiya a hannunta, kai a  tunanin ka da tana son guduwa ai da ta tafi, tuntuni amma sabida soyayyar da take maka yasa ta tsayawa. Kayanta da ta dauka ta baka, sannan ta ta tashi gudun da kake fada bata tafi da kome na ta ba,sai wannan duwatsun Haba Ma'aruf idan mai magana wawa ne, ai majiyin shi ba wawa bane. Kayi nazari da kyau shi yaron da ake son yabi ra'ayin ka,. Ka tab'a tambayar shi meke damun shi? Baka tab'a ba, da zaran an gaya maka yayi kaza ranka a b'ace zaka hukunta shi. Sabida zunzurutun son kai.

     ... Toh wallahi matukar ka ɗore a haka Tabbas akwai matsala, domin kuwa za a wayi gari yana adawa da duk wani abun cigaba da zaka kawo mishi kayi nazari da magabata, kayi dubi da abinda na gaya maka. Matsalar Aamil daga cikin gidan ka aka faro shi. Ba wai daga ko ina bane laifin uwar shi ya shafe shi.    A wannan duniya kowa son ka shi yake kowa na shi yake so.

    Kai kuwa kayi watsi da naka, lokacin da ake bukatar ka more shi ya juya maka baya, sannan maganar gaskiya indai yadda ya kawo korafin Yarinyar bata mishi ba, mishi ba  hakura da auren nan haka."
                 "Ba zai yiwu ba! Yarinyar zai aura, naji nayi laifi batun auren Sidrah ko Aamil yana mutuwa ya dawo sai ya aureta. Balle kuma babu abinda zai faru, aure ne sai yayi shi. Indai Ni na haife shi." Duk wannan musayar  yawun da suke, Alhaji Abubakar yana jin su. Gyara zama yayi bayan ya kalli Alhaji Ma'aruf, ya sauke numfashi sannan yace musu.

"Wato wani kuskuren da muke aikatawa, bamu sani ba, shine hada iyayen mu mata da matan auren mu, ba dan kome ba sai dan babu wata uwar da zata jure ganin wata ta juya Mata D'anta, musamman iyayen mu da suke da duhun kai! Gani suke sun gama wahalar su, lokaci guda kinzo kin juya mata hankalin D'anta, sannan suma matan mu, basu iya hakuri ganin an juya musu akalar mazajen su. Sabida ai su, suka fi dacewa da juya mazajen su ba iyayen mazan ba.

   Kaga irin wannan al'amarin. Ya sani raba gidana biyu, mahaifina tana can bayan layin mu, har da yan aikinta da duk wani abun da take bukata na tura mata, har mota nata na kanta, na saya mata. Da driven ta, gudana kuwa nayi kokarin tsayawa namijin duniya, babu macen da zata rena min uwa, kuma naki yarda na dauki damuwata da Matana na kai na gayawa Mahaifiyata.

    Badan kome ba, sai dan kawai na tsira da kwanciyar hankali na, ka nutsu da kyau, taya za ayi a ce da kome sai Mahaifiyar ka ta sani, wannan shine dalilin da ya rabaka da matar ka! Shine dalilin da ya rabaka da Yaronka. Babu wani wanda zai gaya maka gaskiyar da muka gaya maka.

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now