https://my.w.tt/UenPpAMydbb
𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮Bismillah Rahmani Raheem
#Hali zanen dutse
1️⃣1️⃣Sosai jikin Lantana yayi sanyi, dan idan zata nutsu nasiha ce Sabuwa take mata, a fakaice har sabuwa ta gama zata bar gidan Sidrah da take makale a bango tana shashekar kuka, bata fasa ba. Riko hannunta Sabuwa tayi sannan tace mata.
"Kiyi hakuri! Zaki ga amfanin haka domin shi Mahakurci mawadaci. Ance karyanka ta kare amma gaskiyar ka da hakurinka ba sa karewa, sai da akasin haka. Kowa yace zai iya sai kabarshi da iyawar shi. Insha Allah zaki kasance wacce zata ribanci hakuri a duk inda ta taso miki. Lantana na barki lafiya."
..... Kamar ance Sidrah ta kalli, Lantana ta zuba mata jajjayen Idanun, tana na nazarin yadda zata ci uban Sidrah a nutse, yadda babu wanda zai fahimci abinda take aikatawa sai ta gama, dan haka ta yayi gyalenta sai gidan kawarta Aminiyarta, kuma kawar cin mushenta, tun daga soron gidan take kwad'a sallama.
"Lale maraba, Lantana shigo mana. Ai gidan ne nan. Karki ji kome" dake a fusace take tana shiga ta nemi guri ta zauna tana huci. Ruwa ta kawo mata daga randan sanyi, sannan ta kurb'a.
"Mai dan wake! Kinji yadda nake jin bakin ciki kamar zai karni lahira! Kinji yadda kirjina take wata irin bugawa!
Wai Nice za acima mutunci a cikin gidana"
"Kamar ya? Meke faruwa, ince kome ya wuce akan wancan yar rikon ku?" Mai dan wake ta tambayeta,
Cikin tsannanin b'acin rai tace mata.
"Hmm! Akanta ne, kuma wallahi sai na dauki mataki akanta." Lantana ta faɗa tana hura hanci,"Dadi na dake baki da hakuri, me ya faru kin barin a duhu?"
Nan ta gyara zamanta ta shiga mata bayani, wani dogon tsaki taja sannan tace mata.
"Amma wallahi babu sakarya lamba daya. Akan yar da kika haifa zaki zauna kika ihu. Toh bari ki ji, toh bari na gaya miki, babu duka babu zagi, wai ma Lantana duka duka nawa Sidira take da ake baki tsoro akanta?Yarinyar da ke kanki kin san ba kome bace a gurin ki da gurin sauran mutane, dan banten Ubanta daura mata talla, idan bata sayar ba, a bakin abincin ta, dole ta fara karuwanci naga yadda za a dauke ta abawa Bature ita bayan ta zama karamar karuwa."
Zaro idanu Lantana tayi tare da cewa..
"Ke ruwa min asiri wasitira wa alaika z rabani da abinda ya turewa buzu nadi, ke kina tsammani zasu bar ni je dangin Ubanta, bayan basu daurawa yaran su talla, ai zasu cinye ni d'anye. Ke dai Zan iya zabtar da ita sai ta rasa inda yake mata dad'i."...."ji sakarci! Haka shine mafita" inji mai danwake,
"Bafa zai yiwu bane! Domin na tab'a kuskuren hakan malam ya kusan sake ni, da girmana gotai gotai, ban zauna a d'akina ba. Nace sani zawarci gida ai babu tsari, kawai zan a zabtar da ita dai amma talla kan akan aurena ne dan duk yaran gidan basa talla."Shiru suka yi suna niman idea, kansu ya kwance,
"Toh kawai ki cigaba da a zabtar da ita domin na lura mutane basu san cewa kina kokari ba, ki a zabtar da ita a boye a gaban mutane ki sota yadda babu wanda zai fahimci ainihin abinda kike mata!"Shiru suka yi kafin suka kuma fashewa da dariya, ana kuma cigaba da hada rigima sosai.
***
Jigawa dutse.Aiki suke na karyawa masu wanke wanke suna aikin shi. Latifah ta kalli. Hajiya Uwani tace mata.
"Ummin mu! Ko zamu saka curry a wancan kwai din, sabida yana karni kuma kin san bawai kan agric bane na kazar gida ce!"
"Saka mana In-law, gran Son baya son karni ko? Jiya ma miyar kukar dare an saka curry sabida karni, girkin rana ma, curry. Za a haifa min yellow miji ko yellow kishiya"
![](https://img.wattpad.com/cover/242711842-288-k359149.jpg)
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
عاطفيةThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...