Forbearance 0️⃣9️⃣

474 63 0
                                    

https://my.w.tt/GbW5hwzNbbb
𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

     ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
      
        ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮

Bismillah Rahmani Raheem

#Juriya
0️⃣9️⃣

      "Meye abun bakin ciki? Cikin dake jikinki? Toh Allah ya kyauta." Ta bar dakin abinta, dan ta lura baki daya jahilci na damun Hajiya Surayyah.

             Washi gari da safe bayan an gama abin karyawa aka kira amare, suka shigo da farko zasu yi rawan kai, ganin yadda take musu bayani, wani abubuwan na girki ma basu sani ba, sai jikin su yayi sanyi, musamman yadda take wurga musu turanci, take duk suka sha jinin jikin su, bayan ta gama sannan tayi musu sallama zata tafi aiki.

         Raba kan su, suka yi wasu suka dauki wani aikin wasu suka dauki wani.
      Sun nutsu suna aikin kawai, zaka dauka wani abun Arziki zasu aikata,
                       "Sannunku amare aiki ake haka?" Inji Hajiya, d'ago kai suka yi tare da zuba mata ido, kafin aka samu Ummita tace mata.
"Eh Hajiya!"
Gyada kai tayi sannan tace musu.
"Hala bata gaya muku ana kaiwa Kasuwa ba? Wannan matar akwai bakin ciki a ranta, dan haka kuyi abinda yayi muku kawai karku dauki tsarinta."
""Toh Hajiya" suka ce mata.

. Hajiya na fita Hindatu na Shigowa, kallon su take kafin tace musu.
"Uwani bata gaya muku muna son yaji ba? Toh ku zuba mana gishiri sosai!". 
"Amma kuma tace mana Abba bai da lafiya bay..."

    "Ke Ummita! Babu ruwanki da wata mata a gidan nan idan ba zaki iya girkin ba, wacce shashin ki!" Inji Surukata Hajiya Surayyah,
                "Toh umma." Dan haka taja bakinta ta shiru, sai ya zamana tsakanin Hajiya da Ya Hindatu anawa juna wani irin kallo. Kafin kowacce ta bar kofar.

             A hankali suka gama aikin aka zuba na shago, tare da zuba na cikin gidan, suka dauki nasu suka watse. 
Bayan wasu mintuna aka dawo da abincin Alhaji Ma'aruf, da kanshi ya kira Hajiya Uwani, yayi fada sosai. Sannan yasata dole ta dawo gida ta mishi abinci yana jira. Hakuri ta bashi daga haka bata kuma cewa kome ba. A hanzarce ta dawo gida, tare da fara aiki babu shiri.

         Matar Ali ce ta shigo gidan ta ji kamshi na tashi, kasa hakuri tayi ta leka kitchen ɗin taga Hajiya Uwani da Aashiq da Aseed tare da Abdus Samad, suna aiki su yaran sun mai da hankalin su kan abinda suke mata, itama ta kuma mai da hankalinta kan girkin ta. Wanke namar kaza Aashiq yayi tare da ajiyewa a choping board, ya shiga yankawa yana zuba mata a cikin kwando, Aseed yana barbada mishi garin flour me mix din kayan kamshi dangin curry da thyme, ingredients da sauran su. Abdus Samad yana yanka Albasa, tare da tomatos. Sun mai da hankalin su sosai. Ita kuma tana fama da hada cus-cus, jollop din shi.

            Dake Yarinyar wayayya ce, shigowa tayi tare da gaisheta tace mata.
"Da wanne za a taimaka miki?"
D'ago kai tayi tare da sake mata murmushi tace mata.
"Huta abinki latifah!"
   "Ai bazai yiwu ba, kawai ki gaya min abinda zan yi, indai har Mazaje zasu shigo aiki meye amfanin mata irina."

   "Da kin barshi wallahi!" Ta faɗa mata cikin lumana,
"Don Allah."
"Shi kenan! Jalil!" Ta kira yan biyu, da gudu ya fito.
"Gani Ummi! Kiyi sauri ana spider man."
"Lallai zan kashe kallon nan, tunda lokacin islamiyya ya kusa..ka je frig ka dauko min fruit maza ka kawo min, kace Jalal ya tayaka dauko min, kayan salat din nan."

      Haka yaran suka yi ta kwaso mata duk abinda take buƙata, sannan tana aiki tana duba agogo, tare da turawa Alhaji Ma'aruf sakon hakuri, dauko wani katon bowl tasa Aashiq yayi ya kawowa Latifah, tana gama wanke ya'yan itacen ta shiga yanka su, Hajiya Uwani tana nuna mata yadda zata jera.

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now