𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>
https://my.w.tt/iR709OBtmbb
ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮
Bismillah Rahmani Raheem
#last free page
🤔🤔 Mom Sayeed! Dake da masu goyan bayan Aamil ina mika muku taya murna! Kuma dole a zauna da yar baka mummuna😂😒
2️⃣1️⃣
Hadeja..Iyayen yara kowa sai kokarinta ta fidda yarta kunya, banda Sidrah. Wacce gabaki daya wahala ya kuma mai da ita baya, kana ganinta kaga wacce take ƙoƙarin kare lafiyar ta, kasancewar wasu irin kuraje sun kuma fesowa a jikin ta, ga shi har bakinta da matse matsinta, idan dare yayi bata barci, sosai ya taba mata, idanunta gashi ya hadu da hayaki. Idan tana jin barci idanunta yayi ta zubda kwalla tare da yaji da raɗaɗi.
Kasa barci take, sabida duk jikinta,yayi ta ciwo kenan. Sai goshinta, asuba barci yake daukarta gari na waye. Lantana zata watsa mata ruwan sanyi..haka zata mike jikinta na rawa zata tashi. Shi yasa take ta karewa sabida babu ishashen lafiya.
Dake bikin yazo dab yasanya Lantana fara taimaka mata da gyaran wanke kafarta sabida fason da suka kama kafar, sai ta shiga daura mata lalle, sabida gab kwanakin idan ta taka kafar har kuka take, sabida shiga ruwa da aikin wahala.
Dan kar ace ta nakasa rayuwar yarinyar, shine ya fara kunsa mata lalle, amma a haka bai hanata fahimta tana fama da ciwon kafar ba, sabida bata tafiya normal. Zayi wuya kaga kuka akan fuskar yarinyar idan tana wahala, amma da zaran ta fama ciwon. Tayi ta shashekan kuka.
Bangaren hannunta kuwa, cin ruwa ne suka tsaga tsakanin yatsunta, farcen hannunta kuwa fita suke da karfin tsiya, sabida sanyin da ya shiga jikinta, shi ya haifar mata da rashin girman jiki.
Kuma babu wanda ya damu da yasan halin da take ciki.
Burin su ayi a kai kowacce gidan mijinta, a huta, wannan yanayin yana daga cikin abu mafi muhimmanci da Lantana da sauran matan gidan suka dauka na bikin Yaran su, Takiya itama sun b'arar da cikin, dan haka ana gayawa babanta cikin ya zube yace musu toh ko babu kayan daki ta nufi hanyar gidan Lawali..Dangin Maman Sidrah, sun mata kayan aiki da wasu abubuwan da ake bukata, sabida kare mutuncin Yarinyar, amma lokacin da suka zo suka ganta, sai da jikin su yayi sanyi, dan haka suka ce zasu dauke ta, a gyarata na kwana biyu, Lantana tayi tsalle ta dire, tana fadin.
"Babu inda zata tafi, ai wannan lokacin tsautsayi yana fadawa amare dan haka a barta ta zauna a cikin gidan nan a gama kome, tunda kunyi naku kokarin sai."Ganin zata rena musu hankalin Sabuwa ta dauki Yarinyar da wata Yayar Maman Sidrah me suna, Indoh suka nufi asibiti da ita, a yadda likita ke musu bayani sai da suka zubda kwalla, na banza. Haka ya rubuta musu magani tare da musu bayanin yadda zata yi amfani dashi.
Basu maida ita gida ba,suka riketa, tare da fara duba ta yadda za ayi mata jinyar kanta kafin ranar bikin. Musamman gashin kanshi, sabida kurajen da yayi tare da kuma kwarkwata, ga ciwon sanyin da suka feso mata.
Dan haka suka fesa mata piya piya, tare da bata maganin zazzaɓi, washi gari suka wanke kan, tare da bata magani da ruwan dumi tasha. Kafarta kuwa babu yadda suka iya da ita, amma tabbas yarinyar akwai jinya a jikinta kamar yadda likita ya faɗa musu.
Shi yasa suka yi iya nasu tare da bata maganin ciwon har ta fara murmurewa, sai da tayi kwana goma wanda yayi dai dai da saura kwana hudu kacal, a daura auren. Sanan suka mai da ita, gidan. Bayan an hada mata sabulun wanka na maganin ciwon ta.
YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
RomanceThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...