https://my.w.tt/Yv5BKGNphbb
𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮Bismillah Rahmani Raheem
*Wancan posting din da nayi bani bace Khadijah Candy ce aka ce wai ta rasu, ita ta manta bata saka sunan ta ba, Nima kuma ban yi azancin saka mata ba da fatan zaku fahimta🙏🏼*
#Ƙullaliya1️⃣5️⃣
Shiru tayi tana kallon shi, cikin yanayin damuwa ta taka har gaban shi,ta rungume shi ta baya shi tare da kifa kanta a gadon bayan shi. Lumshe idanunshi yayi cikin nutsuwa, sannan ya janye ta daga jikin shi yana kallon yadda take jin ba dad'i sabida shi.
"Ba wai bana son faranta mata ba ne, kawai ta bani damar na fita na rayu kamar kowa, haka zai sanya ni jin nima ina da yanci amma a tarani a guri guda babu adalcin a cikin shi. Zata fahimci haka domin itama tana cikin kaɗaice."
Yana kai aya yabar mata falon......
"Wannan wani irin abu ne? Kana nufin Allison shi ya aikata duk laifin da yake faruwa? A'a akwai wani Inuwa a bayan D'ana akwai wani wanda yake bibiyar shi.Akwai wanda yake bin sawun shi, haka kawai Allison ba zai aikata abin.."
"Mss William! Ina son ku biyo ni asibitin dashi, domin akwai wasu da suka tabbatar da cewa,Allison shine." Inji Anthony General na yan sandan.
Mik'ewa tayi zuwa sama inda yake ta sami Emily a zaune ta zuba tagumi tare da kurawa dakin da ya shiga idanu, cikin damuwa ta shiga ta sami yana zaune akan laptop yana zanen a ciki. Yana zane wata matashiya. Yadda yake amfanin da Black paint ya sata fahimtar baka ce. Daga kafadar shi, tare da kallon fuskar zanen.
"Wacece ita?" Murmushi yayi sannan yace mata.
"Kawai zuciyata ce ta sani zana ta! Ina ji a jikina kamar dama can akwai ta a duniyar, tayi min yanayin da na zanata tana kuka!"Murmushi tayi sannan ta shafa kan shi, tare da sake wurga mishi tambaya.
"Jiya da dare ka fita ne? Ina kaje?"
"Ni kuma! Mom ai rabona da na fita yau kwana uku, ki duba dakin Tsaro mana." Ya fada mata haka kai tsaye.
"Toh taso muje! Akwai matsala domin Anthony General na yan sandan yazo tafiya da kai."
Kura mata ido yayi sannan ya rufe laptop din shi, ya biyo bayanta, suka sauka kasa kallon Lauyan su yayi, aka shiga tattaunawa kafin suka fita tare, Office din Yan sanda suka isa aka kai Allison har asibitin suka tabbatar shine. Bincike da yayi bincike aka Fahimci a daren bai fita ko ina ba, dan suna da cigaba .Sosai, akwai camera a kowani ɓangare na unguwa da kuma titi, da wannan Allah ya kwace shi ya dawo gida,
Amma kuma tabbas Mahaifiyarshi ta hana shi fita ko ina. Gudun b'acin sunanta.---
"Ka tabbatar Jerry! Allison yana tare da kai? Domin kuwa zan so na kashe shi da hannuna yadda mahaifiyar shi zata dawamma a cikin bakin ciki na har abada."Gyara zama Jerry yayi sannan ya kalli Chris yace mishi..
"Ba zan maka aikin banza ba, amma tabbas yana tare damu, idan dare yayi baya zama a gidan da yaƙe,komawa Mansion din su yake.Sannan kuma asuba yana yi zai dawo, Breth da su Max sun dauka da gaske ba shi bane ni kuma nasan shine, dan baya cika barin fuskar shi a gani, idan kuma ya bari toh tabbas zai maka dukar da sai ka manta da i da kake. Ni dai idan zaka kashe shi karka sanya ni a cikin mutanen da zasu maka aiki dan ya yarda dani, sama da kowa."

YOU ARE READING
RUWA BIYU.....
Любовные романыThey were born in one day! one Womb! one person! but their destiny has divided their world, One Muslim and evil! one person Christianity person The Lord's case is under control! So He arose and created them as one! They were born once! They were bor...