=Contention5️⃣

546 86 9
                                    

𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

     ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
      
        ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮

Bismillah Rahmani Raheem
 
https://chat.whatsapp.com/GIIFqCembtoD3Bp6yWve7C

Don Allah idan kana Groups dina karka shiga wannan na masu bukatar Free Pages ne! Please karku shiga 🙏🏼

     *Masu tambaya akan Sunan Labarin! Kusan zan fada muku cewa aya ce ta Alqur'ani kamar Yadda Allah madaukakin sarki yace. He released the two seas, meeting {Side by side} between them a barrier [so] either of them, transgresses 55:19:20! Da fatan zaku fahimta, and indai ruwa biyun zasu zauna a guri guda daya ba zai shiga daya ba, sannan koda ya shiga zai fita! Toh taya haka zai faru? Labari ne akan Halayyar mutane biyu! Duk wanda ya karanta PROLOGUE zai fahimci ainihin kan labarin! Halayyar mai kyau da Mara Kyau! Shine Ma'anar Ka sayi daya ka samu daya kyauta Shine ruwa biyu! Daya me dad'i daya me gishiri! Taya zamu banbance su koda kuwa sun kasance a kofi biyu! Sai ku tayani duba su*
#Taƙaddama
0️⃣5️⃣

"Wai lafiyarki? Ki tafi ki basu abinci mana, kin wani kasa kin tsare, tare da addabar mu da tsida yawu, sai kace wata farin shigar ciki." Inji Ya Hindatu, cike da jin kunya me hade da jin haushi ta mike, ranta bai so ba, ba dan kome ba sai dan gulmarta da tayi imanin zasu yi.

          Tana mik'ewa Ya Hindatu ta tab'e baki tana faɗin.
"Algunguma, kin iya ta wasa baki son ayi taki, dani kike zancen sakarya."

"Hmm! Ita nan mai wayo sai da Jamilah suka je shagon kafin ta aka ganta gurin wai ta kama kame kame, ita gata nan mara gaskiya biris nayi da ita na zubawa gudu ruwanta ido, naga iyakatar."

    "Assalamun Alaikum!" Inji Hajiya Uwani. "Wa'alaikimun Salam, Uwar biyu kyautar Allah, Barka da zuwa, ya aiki? ". Murmushi tayi sannan tace masu.
"Alhamdulillahi ya gida!" 
"Lafiya lau,"
"Toh sannunku da aiko!"
"Yawwa sannu da dawowa.".
"Yawwa sannunku da gida, "
Tana wuccewa suka bita da zunɗe, tare da nuna bayanta, da baki.

Wato gidan Alhaji Ma'aruf, babban gida ne,  domin a sauran jikin gidan ya fidda wasu shashi kusan tara, idan ka cire na Aamil wanda yake ciki. Sauran duk suna wajen gidan ne, amma akwai hanya ta cikin gida.

     Kowani shashin na wajen gidan flat ne na zaman mutane biyu, Ali da Ghali. Flat din su biyu, kowa da shashin sa..
Faruq da  Mujaheed, shashin su suma ɗaya. Kuma dukkan su kusan ginin su irin na Aamil ne.

Sulaiman da Ismail suma gidan su daya Mahmoud da  Saleh suma haka Bala da Isah. Duk suna zama anyi musu...... Dakin Hajiya Surayyah, yara biyar zata aurar. Ali da Ghali, Jamila Safiya, harirah. Wadannan sune za ayi auren su nan da wata uku.

       ----
Bayan sallah azhar ya shigo gidan, ya samu ana dambe akan abinci,
"Wani wani irin rashin mutunci ne? Dan Ubanku." Sake kwanon suka yi tare da kamewa guri guda, suna rawan sanyin tsoro.

        Tsaki yayi sannan ya wuce dakin Hajiya Uwani, yana shiga ya zube a kujera, ya kalli Aseed, cikin damuwa yace.
"Bani ruwan sanyi!"
"Kai wuce kitchen ka dauko mishi ruwa mara sanyi a gora, Son zanga ranar da zaka bar shan ruwan sanyi babu amfani a jikin d'an adam balle ka samu abin yi kullum."

         Zuba mata rinannun idanun shi yayi cikin damuwa, yace mata.
"Wallahi idan ban sha ba, toh ba makawa zan zuki wiwi! Dan ina jin kaina kamar zata yi bindiga, Ummi wai meye yasa sai ni ne zaku hada da wancan halittar?

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now