Leniency 2️⃣0️⃣

485 62 2
                                    

𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...

Mai_Dambu

Bismillah Rahmani Raheem

🤣🤣🤦🏼‍♀️🤔🤭 Jama'a ina niman Uwar Tankwali 😂

#Sassauci
2️⃣0️⃣

Haka aka raba su dan dole, bawai dan sun so haka ba, sai dai fahimtar indai suna tare Toh zasu yi ta faɗa ne kamar wasu zakarun tsare. Ran Allison ya gama b'aci musamman idan ya tuna da ce mishi da Aamil yayi dan daudu. Sake shafa bottom fi shi yayi tare da cewa.

"Banza jahili, Ni zai kira Gays!"
Can kuma idanun shi suka cika da kwalla, yana kallon P.A, bakin shi yana rawa yace mishi.
"Wai da gaske ni lusari ne? Sannan ni dan daudu ne? Don Allah ka fitar dani duhu mana"

Shigar da shi mota yayi tare da mika mishi wines, ya kurba. Tari ya fara, yana buga kanshi kafin wani lokaci ya shanye tare da niman kari, ko kafin su isa gida ya bugu sosai.

Dakyar aka fidda shi motar bayan sun isa gidan, kwantar dashi suka yi a dakin ƙasa, tare da lullaba mishi duvet,suka fito. Hawaye ke zuba mishi dan. Babu wanda ya tab'a cin zarafin shi haka, wai shine ɗan daudu. Shafa Manhood din shi yayi, yaji ta gim. Lumshe idanun shi yayi tare da budewa. Take giya ta fara mishi huɗubar tsiya. Sabida lokaci guda, My Baby tazo mishi, tare da jan hannun shi. Fincikota yayi ta fado kan shi. Yana kallon fuskarta, kurawa juna ido suka yi yana kallon cikin eye Ball ɗinta wanda yake da wani color na musamman. Wani sabon kasala ce ta dauko mishi bai san lokacin da ya matseta a kirjin shi yana faɗin.
"Ki kasance dani, har abada"

Jan kumatun shi tayi sannan ta bashi light kiss a bakin shi, kafin ta janye daga jikin shi, zata sauka.
"Ina zaki?"

Murmushi tayi tare da mik'ewa, dake giya ta gama gaya mishi gaskiya,hangota yayi tana tashi samar,tare da mika mishi hannu. Yana son bin ta, amma gabaki daya ya rasa kuzarin shi.

Lumshe idanun shi ya cigaba da yi har barci yayi gaba dashi. A gurin cike da mafarkan baby, a cikin wasu lambu masu kyau, sai zagaye shi take, tana dariya, tare da hayewa jikin shi. Tun yana biye mata suna dariya karshe suka zube a gurin sai bar numfashi suke ajiyewa, shafa fuskarta yayi, a hankali ya kai bakin shi goshinta, zai sumbata yaga tayi mishi nisa, sake murmushi yayi tare da riko ta yaga kamar ana janta, a hankali ya kai hannun shi. Gani yayi wannan me kama dashin ya shiga tsakanin su.

Tana mika mishi hannu, shima yana mika mata, amma wannan me kama dashi ya hana, kome. Dake zuciyarshi ta gama rike dan daudun take kuwa Aamil ya juya tare da gargad'in shi yana fad'in.

_Kai da kake ɗan daudu, me zaka yi da mace irin wannan! Tawa ce ita din_

Daga fadar haka yaja hannun my Baby ya tafi da ita, yana son bin su ya kasa, itama my Baby. Tirjiya take tare da mika mishi hannu, karshe ta juya ta gantsara mishi cizo, kawai ya sake ta, ta dawo gurin Allison da gudu.

Bude mata hannun yayi ta shige jikin shi, duk yadda yaso ya amsheta kin zuwa tayi tare da rungume Allison sosai, tana kuka.
A zahiran kuwa, shida Emily ce tana rungume a kirjin shi, sai cewa yake.
'Karka raba ni da ita, itace burina karka shiga tsakanin mu"

Kallon shi Emily tayi haushi yana kamata, bata san lokacin da ta kai mishi maka a cinya ba, tare da cewa.
"Dalla bude ido, ka kuma sake ni. Daga ranka ya b'aci kake shan giya. Ko waye ya b'ata maka rai Oho kazo kana shirmen mafarkai marasa dad'i."

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now