Two shadow

492 56 3
                                    

https://my.w.tt/iAhygLXSfbb
𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔
<𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂>

     ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆...
      
        ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮

Bismillah Rahmani Raheem
       
#Inuwa biyu
1️⃣3️⃣
"Babu matar da zata juya mu, dole mu juyata gidan mu ne, ba gidan su ba."
Shiru suka yi, kafin Malam Haliru, ya ce musu zai tafi ya kira mai dauri, amincewa suka yi ya fita, tare da yin shiru. Kowa da abinda yake sakawa a ranshi.

        Bayan mintuna arba'in suka shigo da wani, dattijo yana shigowa ya duba hannun, yace.
"Kashin gefen hannun ne ya karye, Insha Allah zai hade."

Dutse
       Aikin abincin dare Hajiya Surayyah take, ita da Ummita wacce ta shigo taya ta, aikin hankalin su yayi nisa, sosai nan aka Raliyah ta shigo. Tana kallonta. Tare da kura mata ido, dake idan suka yi abincin rana, zuwa yamma sai su shigo cikin gidan hirar maraici.

         "Ummita ya nake jin kamshin turare na a jikinki, kuma yau sati biyu kenan da aka sace?"  Inji Raliyah.

Cikin wani irin tsoro ta kalli Raliyah, sannan tace.
"Wani irin magana ce wannan? Fisabillahi ana zaman lafiya zaki kawo wani irin."

"Kinga dakata! Karki mai dani sakarya, ina kallon ki ne kawai, domin haka kika saka muka tsangwami matar Isah nan kuwa munafuka kece barauniyar, kina shiga dakin mutane ko, toh wallahi baki isa.

      Domin haka kike kwashe kayan mutane ana miki Hakuri Wallahi bazan yi hakuri ba, kiji Dakyau, maza tashi ko na kunyata ki."

"Ke bana ciki da rashin kunya, gidanku ba a koya miki girmama manya bane, da kike wannan rashin kunyar wuce ki bani guri."

     Cikin rashin mutunci, tace mata.
"Hajiya babu inda zani, haka kawai yarinya tana mana sata ace na wuce wallahi sai ta bani turare na ko kuma nayi rashin mutunci a gidan nan"

      "Yanzun don Allah ba zaki tashi a kaina ba, yau naga rashin hankali, ke Ummita kin daukar mata turaren ta ne?" Cikin tsannanin tsoro tace.

"Me zan mata tunda part din mu ba d'aya ba, sannan ga masu ɗaukar abu bata bincike su ba sai ni, dan turaren yayi kamshin turaren ta, sai tace nata ne.  Wallahi ba nata bane!" Ummi ta faɗa tana kuka, kafin kace me gidan ya cika sabida yadda Raliyah take ihu shi ya janyo hankulan mutanen gidan.

       Ga kuma Kukan da Ummita take wanda ya sanya da yawa ganin kamar sharri tayi mata, musamman da uwar mijin Ummita ta amshi rigimar ya zama nata, wannan al'amarin ya masifar b'atawa Raliyah rai.

    Dole Hajiya Uwani ta fito ta kashe rigimar Raliyah tace.
"Wallahi na kyale ki ne..sabida Maman su Abdus Samad, amma na rantse da Allah, sai na baki mamaki. Mara kunya kuma zaki kuma ai ba yau kika fara ba."

Tayi ficewarta, ta bar Ummita tana kuka sosai,sabida tana kiran abinda Raliyah tayi mata da cin fuska..
    ---
"Hmm!" Inji Ya Hindatu, tsabar gulma na cinta, ta kalli waje, a ranta tana jin ciwon sharrin da Aka mata, tab'e baki tayi sanan tace.
"Insha Allah, sai na rama nima, baki yi kuka ba, yar banza muguwa karfi da yaji, kin sani na koma mujiya a cikin gida. Ni dake ne sai na rama."

    Wannan shine abinda take fada tana kuma shan rantsuwa..

**US

       "Rio Lucifa, shine mutum na gaba da ake tsamanin zai zama sakataren na musamman a fadar Whiter house, toh amma matsalar da aka samu. Manyan mutane da yawa suna niman wannan mukamin, a cikin su kuwa akwai shahararriyar attajiran nan Mss William! Dattijuwar kirki mace mai mutunci da kima."

RUWA BIYU.....Where stories live. Discover now