Page 30

504 23 2
                                    

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

*_wannan page kyawta ce ga duk wanda suka bani goyan baya a fara rubuta novels, ina godia sosai, Allah kara hada kan mu,_*

Alhamdulillahi bini'imatihi tatimussalihati,



A bangaren Hafsat kuwa itama yaw shiri takeyi sosai, na tarban mijin ta, so take mijin ta ya linka son da yake mata , shiyasa tace itama zata ajiye raggaci a gefe ta fara mashi duk abinda yake so,
yaw tinda safe aka gyara palour , aka sanya turaren wuta, daki sai kanshi ke tashi,
Da yamma kuwa tin bayan fitar Habib daga gidan ta fara kiciniyar aza girki, aka shiga akayi wanki wanke dukda batada wasu kwanoni masu kazanta sosai saboda sati1 batayi aiki ba , haka dai aka sake wanke su, tana tsaka da wanki wanke Samira ta sake shigowa da sallama a bakin ta, taga su uneisa su kadai a palour tareda yarinyar da ke rainon su, ta dauki uneisa ta bar mata sudais a hannun ta, sai ta tafi da ita bangaren ta ko banzan zata rage mata tunani, sunyi wasar su itada shi ,
Hafsat na jin lokacin da ta dauki ta sai tayi kwafa tace yarinya ba fah zaki taba birgeni ba , tinda har kika auri mijina , ina ganin ta sumi sumi ashe munafuka ce(inji Hafsat bani ba) , tayi kwafa

tuwon shinkafa ne tayi da miyar kub'ewa, ta sha naman ta ragajab sai kanshi ke tashi, ba laifi Hafsat ta fara iya girki , ban sani ba ko nan gaba zata cin ma Samira a bangaren girki saboda gaskiya ta zarce ta sosai, aiko kafin magrib har ta gama , ta kwashe a kula ta aza saman dining , ta tafi ta tsala wanka, tayi sallah , tayi kwalliyar ta cikin wasu kaya mini skirt ne wata yar riga mara hannuwa, kamar ba ita ta haifi su iman ba, dama ko can Hafsat y'ar gayu ce, balle yanzu da ake son ta dawo da hankalin mijin ta gareta, tayi wankan turare tana jiran isowar mijin ta, bayan yazo , yayi wanka za'a fara cin abinci ya leka bangaren samira, ita kuma Hafsat sai ta koma dakin ta ta aza after dres saman kayan jikin ta , saboda bata so samira ta ganta da su kar itama tayi sha'awar yiwa Habib kwalliya da irin su.

Bayan Habib ya kira Samira sannan Hafsat tayi saving in su, suka fara cin abinci, koda suka gama aka dawo palour wajen zaman Samira sai tayi masu saida safe tana cewa da Iman ta taso su kwanta tare. Hafsat tana son hanata bin Samira amma sai Habib yace Iman tashi ku kwanta keda antyn ki, Muslim ma yace yana zuwa sai suka tafi tare aka bar mata twins kawai, sai Habib yace da Hafsat

"my love bari inyi mata saida safe"
to kawai tace sannan shi kuma ya fita sai bangaren ta , bayan yayi mata saida safe ne yace da ita, kar su mance basu rufe palour ba. Samira ta amsa da toh tana binshi da kallon kauna, har ta fara kewar shi,

Ita kuma Hafsat Habib yana fita taje toilet tayi brush, sannan ta fidda after dress inda ta sanya ta kara bulbula ma jikin ta turare,  saboda fah Hafsat a hannu take saboda an sha tsumi kuma ko banza sati 1 rabon ta da shi abinda bata saba ba, saboda Habib ba daga kafa saman bed🤭 , aiko yana dawowa daga bangaren Samira koda ya ganta haka take ya kwance layi ,sun dagargaji juna ita da shi yaw .

A can kuwa bangaren samira bayan Habib ya fita, sukayi kallo, koda su Iman sukace sunajin bacci, sai suka kashe kallon suka rufe palour, sannan sukaje daki suka kwanta,  koda ta kwanta sai taji gadon ya mata fadi, juyi takeyi tana tunanin moment in su itada Habib na tsawon sati daya, yadda ya koya mata zama saman jikin shi, yadda yake mata shagwaba, da y'an tabe taben da yake mata🙈, kewa ce ta isheta, tunanin mijin ta fal ran ta, ta kalli su Iman da tuni sunyi jima da yin bacci, ta juya nan ta juya can a fili ta furta
"Ina kewar ka mijina" sai ta tashi tsam tayi alwala tayi nafila tareda adu'a Allah ya raba ta da mugun kishi, kuma ya hada kan su itada Hafsat saboda taga har yanzu bata dauke ta a matsayin abokiyar zama ba, tayi ma mijin ta adu'a Allah ya kara mashi budi , sannan tayiwa dukan masu bakuta adu'a,
bayan ta shafa adu'ar ne ta kara hawa saman gado, sannn ta dauko wayar ta, tana kallon hotunan da sukayi ita shi, tana kallon har taji rabin kewar da takeji ta ragu, tana cikin kallon hotunan bacci yayi awon gaba da ita , ba ita ta farka ba saida taji wayar ta na ringing , Habib ne ke kiran ta saboda ko yayi bugun kofa bazataji ba, tana dagawa yace ta tashi lokcin sallah yayi,  tana tashi saida ta bude palour sannan ta tada Iman  , suka tafi sukayi alwala , tayi raka'tul fajar, koda taji an tada sallah sai ta kabbarta sallah ta .

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Where stories live. Discover now