page 8&9

634 40 0
                                    

0⃣8⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*






Sakon gaisuwa gareku
*YAR AIKIN GIDANA NOVELS*
Nagode sosai da addu'ar ku gareni

Anty ta, ta kaina Anty Naseeba Gao kema na gaida ki kyawta
My Harira kema ina gaida ki
Masu sharki kumu ina yin ku irin so in nan , i love you so much 💗💗💗


Bayan kwana biyu da maganar su Habib sai ko gasu gidan su Samira shida aminin shi sun kai ma inna ziyara hada bata kyawtar 10000 FCFA (dubu 6 kenan) , way su biya mai haya , inna tayi ta zabga mashi godia har lokacin da zaya tafia saboda yana masu kirki tin lokacin da itace take aiki a gidan shi,  bama shine karo na farko ba da yake zuwa gidan ta duba lfyr ta amma tinda ta ji dan dama yana dan jimawa bai zo ba ,  shiyasa yanzu da ya mata kyawtar kudi bata kawo komai a ran ta ba, a lokacin Samira tana can gidan shi wajen aiki , sai bayan ta dawo ne innar ta ke fada mata yazo tareda nuna mata kyawtar da yayi mata , tace
"Allah ya biya shi"
Inna ta amsa da ameen

Daga nan inna tayi shirin sallah magariba dayake lokacin sallar yayi., ita kuma samira har yanzu ana hutu🙈🙈🙈

Bayan inna ta gama sallah suna zaune suna hira sai innar ta tace da ita

"Samira tinda kinga mun samu kudi kuma ga na albashin ki da aka baki sai mu gama mu tafi garin baban ku , kinga mun samu kudin mota ko"

Samira tace " hakane inna, to yawshe kuke gani zamuyi tafyar nan dan ina son shaida masu kenan su samu masu taya su aiki "

Inna tace " gobe inshah Allah in kin tafi ki fada masu zamuyi tafya kuma zamuyi ko sati ne in mun tafi saboda ina so kiga dangin ki duk da sun zubda ki dan ba uwar su guda da baban ki ba,  muje ki gan su saboda watarana kuna iya haduwa da mutum baka san shi ba "

Samira tace " hakane innata wlh kinga duk diyan su ban san su ba sai uwaye masu dan zuwa nan lokacin da baba na da rai" ta karashe maganar a sanyaye

Innar ta tace
" hakane kam Allah ya jikan malan "

Samira tace " ameen innata , Allah bar min ke"

Inna tace " ameen diyar Albarka , Allah ya nuna mani auren ki , nima in ga jika na "

Samira ta sunne kai kasa tana murmushi

inna tace
" yar nema baki amsawa"

Samira ta kara murmushi ta amsa da ameen cikin zuciyar ta ( ni ko nace yaw innar ce ake jin kunya)

Suna nan zaune suna hira ha aka kira sallah isha'i , inna ta tashi ta dabatar da sallah , tana gamawa suka zuba abincin su suka ci abun su , bayan sun gama ci suka kuma komawa hirar su irin ta da y'a da uwa ,


_________¥¥¥¥¥¥________

Washegari bayan Samira ta tafi gidan aikin ta , ta shaida ma matar gidan cewa zasuyi tafya zuwa kauyen tawa wajen dangin baban su ,

Saida Hafsat ta dan ja fasali kafin tace

"yawshe ne tafyar "

Samira tace
"nan da kwana uku inshah Allah"

Ok kawai Hafsat tace , inaga bata son tafyar ne da Samira zatayi shiyasa , tunatin ma yanzu nan da kwana uku ina zata samun y'ar aikin da ta iya sanwa kamar Samira, batada amsar tambayar da take cikin zuciyar ta shiyasa tayi bedroom abunta ta huta da yake tana ta fama da da kan ta cos cikin ta yayi girma kamar yanzu ne zata haihuwa kuma alhali duka wata bakwai ne gare shi,

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Where stories live. Discover now