0⃣3⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
Wannan page naku ne yan
*RAHAMA FANS NOVELS*
*ASMA BAFFA FANS*Naji dadi yadda kuka bani kwarin gwiyar fara rubutawa ina yin ku irin su in nan 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Wacece Samira ?
Samira y'a ce ga malan Dahiru me wanki da guga dan asalin garin tawa ne neman kudi ne ya kawo shi cikin garin maradi har Allah ya hada shi da suwaiba lokacin zashi kasuwa ita kuma zata islamiya ya gani ya yaba da nutsuwar ta , be mata magana ba dai amma ya yaba seda yaje ya nemi gidan su ya tambayi a mashi izinin zuwa zance wajen ta , seda iyayen ta sukayi bincike a kanshi kafin suka barshi ya fara zuwa, da farko ta ja aji daga baya suka fara fahimtar juna , babu jimawa soyaya ta kullu tsakanin masoyan biyu har ta kai su ga aure , bayan auren su so uku tana haihuwa diyan suna rasuwa tana ta hakuri har Allah ya kara bata wani cikin ya tsaya bayan wata tara ta haifi y'ar ta mace kyakyawa son kowa kin wanda ya rasa rana suna yarinya taci sunan *Samira* an sha shagali a wajen sunan , Samira ta fara wayo iyayen ta suna ji da y'ar su sosai kasancewar ita kadai Allah ya basu dunda haka suna bata tarbiya dai dai gwargwado , lokacin da ta fara wayo malan Dahiru ya sanyata a islamiyar dake layin su , sannu sannu tana zuwa tana fahimtar wani abu da yake tanada kokari bakin gwargwardo , lokacin da ta cika shekara 6 ya sanyata a wata primary school ta gwamnati dake unguwar su, sannu sannu tana zuwa har ta gama primary taci jarabawar fita daga primary school , a wannan lokaci ta bada mamaki sabida duka garin maradi itace ta 3 wajen exam, bayan result ya fito aka shiga hutun karshen shekara su samira ana daukin za'a shiga secondry school a lokacin tanada 12 years , bayan hutu ya kare ta fara zuwa secondry school a kafa take zuwa da yake babu wani nisa sosai itada kawar ta me sunan zainab suke dawowa sai dai kowa daban yake tafiyar shi saboda gudun kar wani yayi latti ya tsaida wani taci gaba da zuwa makarantar ta ha tazo tayi 6e (Js1 kenan ) tana tsaka da 5e (Js2 kenan) a wata ranan Litinin mahaifin ta ya rasu bayan rashin lfy da yayi , mutuwar shi ta girgiza inna suwaiba da ita kanta samira sun sha kuka😭😭😭😭😭(Allah ya jikan mahaifan mu) daga baya suka rungumi kaddara saboda babu me wuce lokacin shi amma inna suwaiba ta sanya a abun a ran ta har ya kaita ga kamuwa da hawan jini sanadiyar tunanin da takeyi na maraicin Samira kuma gata ita gidan su ba wani hali ne garesu ba shiyasa ta nemi aikatau a gidan Alhaji habib tana zuwa kullum safe da yamma da shi suka ci suna sha, tafya tayi tafya han hawa jinin ta ya tsananta shiyasa ta bar zuwa aiki ita kuma Samira taci gaba da zuwa ta maye gurbin uwar ta abinda ya hana ta zuwa school kenan saboda tana mugun son innarta shiyas take tausaya mata wannan dalilin ya sa tabar zuwa school , se dai fah tin lokacin da fara zuwa aiki tana birge me gida Alhaji Habib amma gudun kishin matar sa shiyasa yake takatsatsan amma fah shi ya ga mata ta biyu(😳 in Hafsat ta sani mu dai yan kallo ne)
Sannu sannu ha se ga Samira tayi shekara biyu tana aikin ta a gidan Alhaji Habib, da abincin da ake bata suke ci kullum safe da yamma kuma in wata ya mutu in anyi albashi a basu da shi kuma sukeyin bukatar su na yaw da kullum , Samira yarinya ce kamila nutsatsa abun hannun wani baya birge ta , tanada kokari sosai batada kwiya a fannin aiki se dai tanada fada amma se an janta tana girmama na gaba da ita amma fah ta tsani raini da tozarci dukda basuda hali bata rakon ka iyacikar ta taje aiki ta dawo shima dan babu yadda zatayi ne shiyasa takeyin shi , tana sha'war komawa makarantar boko sai dai ba halin komawa saboda aikatauSamira tanada tsayi ba sosai ba , batada kiba , jikin ta madaidaici ne, tanada kyaw in ta ba sosai ba amma fah ta fini kyaw😂😂 sema in ta samu hutu zakuga yadda zata komawa Yanzu tana cikin 16 years in ta kuma har yanzu ba ta fara soyaya ba ko miye dalili ni dai ban sani ba ( ku fah fans🤓🤓🤓)
cigaban labari
mu hadu a page 0⃣4⃣
ku muje zuwa fans🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀ 💃🏻💃🏻💃🏻
sakon gaisuwa gareku masoyana , ina alfahari da ku a duk inda kuke
comment in ku yana sanya ni nishadi😘😘😘😘
BINABASA MO ANG
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomanceSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...