page 17

414 36 0
                                    

1⃣7⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

*Sakon gaisuwa gareku masoyana 😘😘😘*


Labarin abinda ya faru ha ya kai gidan Alhaji Tanko , abinka ga kauye yara ha sunje sun fadi albarkacin bakin su kowa na fadin Alhaji tanko neman aure yake dan yaga yarinya ta fito daga birni,
Lokacin da matan shi sukaji abinda ya faru uwar gidan tsaka saida ta rangada buda ayyyyyyyyiririiiiii tana cewa
"Allah ya kara , ai ni naso su bashi yarinyar tazo nan gidan ta dandana abinda muke ji ,"
Sai amaria tace
"ai ni tin jiya naso in tafi inga wanene ake ta yiwa hidima ,haka, Alhaji hada cewa in na fita a bakin aure na , ashe yaga yarinya ya kyasa, shiyasa kukaga ban fita ba"
Uwar gida tace
"ku bari ya dawo muji mi za'a dafawa yaw a kai ma baki"
Aiko sai naga amaria tace Ahayye huuuu suka tabe da uwar gidan tsaka , ita kuma uwar gida murmushi kawai tayi , daga nan sukayi ta maida zancen har lokacin da kawu Akhaji tanko ya iso 😂😂

Tinda Alhaji Tanko ya baro gidan kawu sanusi , yana tafe saman hanya kamar yayi kuka, shi wlh dan yaji ance soji ne zata aura da sai ta tafi ya masu asiri, sun aura masu ita, amma yanzu yana tsoron a aura mashi ita sojoji ba imani ne da su ba, suzo su ci shi tara a amshe mashi kudin( sai son kudi tsiya) dan haka bari yayi hakuri gobe da safe ya tura a amso mashi kudin zabin shi, yana tafe kowa sai kallon shi akeyi saman hanya har ya iso gida , yana zuwa da sallama ciki ciki kamar hadin baki, suka amsa kusan a tare , sai can uwar dayake itace da girki tace
"wai Alhaji ina ka shiga ina ta cigiyar ka kazo ka bada kudin sanwa ayi ma bakin ka girki, kaga yanzu har an kusa magriba ba'ayi masu ba komi ba, ko dai yaw balangu za'a saye masu ne"
Ta ida maganar tana kallon sauran mata da kifta masu ido👀
Shi kuma Alhaji tanko tinda ta fara maganar yaji zuciyar shi tana zafi 🔥🔥🔥, tana tafarfasa ji yake kamar yaje ya dauke uwar gida da mari( bafa ita ta kai zomon ba, ko taraya ba'a bata ba) , dan bata san asara da yayi ne ba zuwan bakinan garin , amma bari dai yayi mata sannun dan kar su fahimce shi, sai yace
"ai yanzu na bara su , suna shirin komawa ma, dama wai ita wannan yarinyar ce zata aure shine suka zo fada masu zancen auren, kuma wai uwar ta , ta rasa mijin da zata zabar ma y'ar ta sai soji, ai ni wlh tabani ma haushi"(🙆🙆🙆 )
Amaria tace
"yo kai Alhaji ina ruwanka da su ai inda ba'a mata miji ba da sai ke nema lawali auren ta" (sunan d'an Alhaji ne lawali)
A zuciyar shi , wane lawali kuma bayan ni ai ni badan sun mata miji ai saidai kawai kuji ana ayyyyiri an kawo amaria, mtssss ya ja tsaki sannan yace
"ke ni bani a buta in tafi masalaci, raba ni da zancen su"
Uwar gida tana boye dariarta taje ta zubo mashi ruwa a buta yayi alwala sannan yayi ficewarsa masalaci su kuma suka zauna suna ta mashi daria ( hummm mata an samu abinda ake so, ),

A can kuwa bangaren su inna bayan sun gama gaisawa da gwaggo suke cemata ai ko gobe ma zasu koma birni kasancewar matan da suke aiki gidan ta watan tane na haihuwa kuma batada yan uwa kusa, inna tayi mata karya kasancewar bata son gwaggon su taji labarin abinda ya faru , tana tsoron tayi ta bata hakuri ha suzo su tsaya kuma azo a hada diyan ta da wani a mata auren dole, wannan kenan

Gwaggo tayi masu bankwana sannan ta nufin bangaren iya tayi mata bankwana itama sannan tayi gida,
Suma su inna bayan sunyi sallah isha'ai suka haw gyaran kayan su basu dai fada ma kowa samako zasuyi ba gobe amma sunyi shiru da bakin su, daga nan sukayi shirin bacci( asuba ta gari inna suwaiba momyn samira)

Washegari tinda safe su inna sukayi wanka suka shiryawasu tsaf sannan suka shiga bangaren iya suka ce mata tafya zasuyi gida kuma sai watarana in Allah ya maido su

Iya ta kalle su sama da kasa sannan tace
"zaku tafya yaw amma shine tin jiya ba zaku fada mani ba , dan ba ni na haifi Dahiru , shikenan Allah ya kiyaye hanya"
A zuci tace gwara ku tafi in huta da kallon fuskar wancan aljanar yarinyar me kama da indo, dun tafi jikoki na kyaw , sai shegen kyaw tsiya, mtssssss, ta ja tsaki ,

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt