0⃣4⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 ina kike kawata ta kai na , aminiyata, yar uwata , my Fati wanan page taki ce ke kadai kiyi yadda kike so da ita🤓 ,
Habib ne zaune a palour shi yana jiran Iman da muslim su gama shirin su na makaranta ya biya ya ajiye su da yake wani lokaci in Hafsat bata zuwa aiki da safe shi ke kaisu makaranta se ga Hafsat ta fito tareda su, da gudu sukayi wajen baban su suna cewa
"baba mun shirya"
Habib yace da su
"ok kuzo muje "Yaran sukace da mama su "mama mun tafi école( school)
Hafsat ta shafa kan su tace "Allah ya kiyaye hanya y'ay'a na ayi karatu da kyaw banda wasa kunji mes enfants (my kids)"
Sukace " toh mama au revoir (bye) !!"
Habib yace da Hafsat " mon amour ( my love) mun tafi kasuwa kuma se Allah ya dawo da mu"
Hafsat tace " ok mon coeur ( my heart) Allah Ya kiyaye nima bari inje in kimtsa saboda karfe 9 ne nima zani tafya wajen aiki"
Habib yace "Ameen mon amour ( my love) " yana me yin gaba
Fitowar Habib daga palour tayi dai dai da shigowar Samira harabar gidan, Samira ji tayi kamar ta koma waje dayake bata son kallon nan da Habib yake yi mata a duk lokacin da ya ganta amma haka ta dake ta taho cikin gidan, a bangaren Habib kuwa wani dadi ne ya lullube shi ganin yar yarinyar da yake fatan kasancewa tareda da ita a matsayin mata ta biyu ( tirkashi😳)
Samira tana kawowa wajen shi tace da shi "Ina wini Alhaji"
Habib yace da ita "an wini lfy yan mata ya innar ki da jiki"
Ta amsa da " da sauki " tana me yin gaba zuwa ciki palour
Shi kuma gogan ya bi ta da kallo , kafin daga bisani yayi gaba zuwa parking space , yana zuwa ya shiga mota shi da yaran shi sukayi gaba. (Allah ya kiyaye hanya )
Tafe yake yana tuki yana tunanin Samira , shi dai yana son matar shi amma kuma Allah ya jarabce shi da son yarinya karama , gaskiya ya kamata ya fada mata sirrin dake zuciyar shi ya huta da abinda ke damun shi ( soyaya kenan )
___________________
Samira na shiga palour ta fara aikin da ta saba , bayan ta gama gyara palourn sannan ta shiga kitchen ta fara wanke wanke , tana tsaka da wanke wanke matar gidan ta leko kitchen in , Samira ta gaida ta, Hafsat ta amsa ba yabo ba fallasa ta kara da cewa "amshi kudi kiyi sauri ki tafi kasuwa ki sayo zogale daffafa me kyaw in kin dawo se ki aza mani dambun , kar ki sayo mani zogale me daci kinji na fada maki"
Samira tace " toh anty " ta amshi kudin ita kuma ta kama gaban ta se wajen aikin ta .
Bayan ta gama wanke wanken ne ta rufe palour ta fito waje bata sha wahalar samun adedeta sahu ba kasancewar kasuwar da zata tafyar ba kusa ne ba shiyasa ta haw adedeta sahu
Ana kawo ta kasuwar ta biya me adedeta sahun kudin shi ita kuma tazo layin masu saida zogale , seda ta zabi me kyaw gudun fadan uwar dakin ta sannan ta saye aka sanya mata a leda ta sake shiga adedeta sahu tayo gida .
yanzu aka fara wasa🤸🏻♀,
Muje zuwasakon gaisuwa gareku masoyana❤❤❤ ina gaida ku kywata 👌🏻
KAMU SEDANG MEMBACA
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomansaSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...