*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
2⃣3⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
Suna zuwa kofar gidan suka tarda su kawu zaune kofar gida kamar kullum , koda sukaga mutane sun tsaya kofar gidan su tareda Inna suwaiba sai suka kara daure fuska irin wannan 😎😎 , saboda sunji haushi sosai kwanaki da suka tafi, sun so kafin su koma su yiwa samira auren dole da ko dan ga ruwa ne ,
Gaishe su sukayi sannan inna suwaiba ta gabatarda baban ta wajen su sannan tace tare suke da baki, magana mai mahimanci ce ta kawo su , sannan tayi cikin gida kawu ya mara mata baya domin dauko tabarma da za'a ba baki duk da bai san mike tafe da su ba.
Tana shiga cikin gida ta gaida yan gidan , ta leka ta gaida iya anyi ma sa'a gwaggo tazo gidan daga nan suka zauna suna hira bayan rabuwa, har take shaida mata ai neman samira ne suka zo , kuma bayan sallah ne auren , fatan alkairi tayi mata sannan tace inshah Allah zasu zo ,
Inna tace
"ga ma number samira tace a kawo maku, kuma tace ku bata taku" tayi maganar tana bata takarda dake dauke da number samiraGwaggo tace "aiko dai in na tafi na kira ta salular yayan ta "
Iya dai tana zaune tana sauraren su amma tanajin haushin yadda gwaggo take sakewa suwaiba sai kace ba y'ar ta ba😏.Acan kuwa bayan kawu ya shinfida masu tabarma suka sake gaisawa sannan suka fada masu abinda ke tafe da su ,
Kawun Habib yace
" sun daidaita da yaron shine mukace dole sai mun zo wajen dangin baban ta , da fatan zaku bamu auren y'ar ku"Wani kwarjini ne malan tsoho ya yiwa kawu sanusi , kuma sai yaga ai ba wasu masu hali ne ba, tinda bai gan su da sutura mai kyaw ba kuma ga wannan tsohon kakan na ta da ya kura mashi ido yana jiran amsar shi "
Da kyar Kawu Sanusi yace
"mi zai hana tinda har sun daidaita ai ko yanzu kuke so sai a daura masu aure"Malan tsoho yace
"a a ba'ayi haka ba, wata uku dai za'a sanyawa kenan bayan sallah karama"
Suka bada kudin aure jikka dari(dubu 60 kenan) da akwatin da suka zo dashi , kawu aka ba kudin ya rike su ga hannu shi , sannan ya shiga cikin gida tareda d'an uwan shi , suka kuma ya bar su kofar gida zaune .
Bayan sun shiga cikin gida suka nunawa yan gidan kayan da aka kawo da kudin sannan kawu yace
"yanzu nawa za'a ba ma yan uwa kudin da ake rabo "
iya tayi caraf tace"ai kaine uban ta kaine zaka yanke abinda za'a basu"
Kawu yace
"hakane iya, jikka 20 zamu dauka sai ta tafi da jikka 80 ta saye mata matala da su ko ? , abinda muka samu daga baya sai mu kai masu in aure ya tashi"
Iya tace
"hakan yayi dai dai"Ita dai inna suwaiba tana zaune batace komi ba suka gama rabon kudin su sannan suka bata saura , akwati ya jawo zai budawa saboda yaga abinda ke ciki, buda akwatin sukayi suna kallon sannan iya tace
"ai ko mu da kauye mun fi karfin wannan kaya balle wanda ke birni "
babu wanda ya tanka mata cikin su , sannan aka rufe akwatin aka ajiye shi sabida da shi inna zata komawa .Basu fi awa 2 a garin ba sukayi masu bankwana suka tafi sai maradi.
*Abinda ya sanya sukayi masu basaja sukayi shigar talakawa*
Habib ne fadawa iyayen shi abinda ya faru a lokacin da Alhaji Tanko ya nemi auran Samira suka hana mashi saboda yana mai kudi shiyasa da zasu tafya kauye suka fadama malan tsoho yadda ya kamata suyi, shine ya bada shawarar su kawo kayan gidan shi , shi yasan yadda zaya tsara abun, kuma yace kar su sanya kaya masu tsada suyi shigar talakawa shine suka sanya kayan da basuda wani tsada.
A lokacin da zasu tafya suka biya gidan malan tsoho suka kai kudin aure jikka 500 da akwatin 5 , shine malan yace tinda basu san ta auri mai kudi kuma bamu san zuciyar su ba , sai ya bada shawarar su debi kayan kadan cikin wanda aka kawo su sanya cikin wata akwati daban kuma su dauki jikka 100 su tafi da su sannan sai su bar sauran gida , dukan su sunyi na'am da haka sannan suka dauki malan tsoho da inna gidan kasancewar samakon zuwa gidan tayi , sannan sukayi kauye ....._____¥_¥_¥_¥_¥____
*Gidan Alhaji Habib*
zaune suke suna cin abincin rana Hafsat sai wani daddaure fuska takeyi yaw fah ita da kan ta , ta shiga kitchen yin girki duk da ba wani iyawa tayi ba sosai amma yaw saida tayi duk ta jigata , ga yan biyu ga gidan ba kowa duk suna can gidan su Habib basu dawo ba ,
Habib ne yace da ita
"my love ashe har yanzu baki hakura ba tinda an ki sakar mani fuska sai fade fuska akeyi"Hummmm kawai Hafsat tace ,
_*Amincin Allah ya tabbata a gareku my fans, kuna lfy, cewa nayi in kuna son in maku al'adar garin mu in za'a auren samira kamar events haka, in kuma baku so a sanya events kawai sai a barshi kenan an ragewa book in tsawo, naga yawancin fans in yan 9ja ne , ni kuma bansan yake events ba a 9ja ko nan cikin wanga page in yadda akeyi garin mu ne nayi , ina jin amsar ku saman number ta, ta private , sai naji amsar ku sannan tin daga yanzu har zuwa gobe inshah Allah , ina yinku irin sosai in nan*_💕💞
*GOOD NIGHT & SWEET DREAM*
*BONNE NUIT &DOUX REVES*Je vous aime tous ❣❣
love you all my fans💕 *NANA AICHA* 💕ce
DU LIEST GERADE
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomantikSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...