0⃣5⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
Tana shiga gidan ko hutawa batayi ba ta shiga kitchen ta fara aikin ta kamar yadda ta saba , a nitse ta aza dambun ta na shinkafa tanayi tana gyara zogalen ta har ta gama sannan ta gyara kitchen in , ta dan samu waje ta huta saboda muguwar gajiyar da tayi tana nan zaune se ga matar gidan ta dawo daga aiki , ta zuba mata abincin tayi gaba sai gida da alama yaw dai mutumniyar ta gaji dan na ga da fita ko an makaranta dake wucewa bata tsaya kallo ba , tana zuwa gida ta shiga da sallam tana me yin kwance saman tabarmar da innar ta ke zaune
innar ta ta amsa sallamar y'ar ta cike da kulawa
inna suwaiba tace "diyata an gaji ko"
samira tace "wlh inna kamar kin sani yaw nagaji bari inje in watsa ruwa saboda in fidda gajiyar nan"
inna tace " to ayi lfy y'ar albarka Allah baki y'ay'a na gari suka abunda kike mani"
Samira tayi murmushi tana me yin gaba
__________________
*Bari muje wacece Hafsat ?*
Hafsat y'a ce ga prof Alhaji Haladu malamin jami'a ne dake koyarwa a jami'ar maradi wato UDDM (Universite dan Dicko dan koulodo de Maradi), yayi aiki a jami'ar yamai, da can suke da zama tinda duka can sukayi karatu , daga baya ne aiki ya maido shi maradi garin dangin shi , sunan mama ta Hajiya Zainab itama tana ma'aikaciyar gwamnati ce tana aiki a Hospital babba ta cikin garin maradi , suna zaune a unguwar gawo dake cikin garin maradi , yan asalin garin maradi ne suma, inda Alhaji Haladu yake bagobiri na cikin tsibiri ita kuma Hajiya zainab bakatsina ce gaba da da baya , iyayen su yan boko ne sosai shiyasa Hafsat ta taso da rashin son aiki kasancewar ko a gida batayin komi sai dai masu aiki ne sukeyi masu, su biyar ne iyayen su suka haifa itace ta uku tanada yaya biyu Lawali da Ibrahim , da kannen ta biyu Fati da Abubakar , dukkansu sunyi aure se auta Abubakar da yake karatun medecine in shi a jami'a yamai wato UAM (Universite Abdou Moumouni de Niamey) ,
Hafsat tayi karatun ta na primary da secondry a wata private school dake cikin garin garin yamai , tin da suka fara makaranta akwai me koya masu karatu a gida lesson teacher kenan , tana zuwa islamiya tayi karatu bakin gwargwado
Bayan ta gama secondry school ne ta samu gurbin karatu a wata institut me suna INJS dake garin Yamai , a can tayi degree a fannin science, tana level 2 anyi wani hutu tazo maradi lokacin ana auren aminiyarta suka hadu da Habib koda ya aza ido a kan ta yaji ta birge shi sai da yayi abinda ya samu number ta daga nan soyaya ta kullu tsakanin su saboda itama a nata bangaren ya birge ta kasancewar shi dan gayu ne ya iya daukar wanka ( amma fah be kai honey ba😍🙈 ) kuma gashi CFA ta zauna a aljihun shi lokacin yana ji da kurciya shi saboda duka 28 years ne gareshi ita kuma tana cikin ta 22years , bayan ta gama degree iyayen su suka shiga a maganar auren su aka kawo kudin aure da lefe na gani na fada, bayan an sha biki amaria ta tare da gidan ta dake unguwar Ali dan tsofo , iyayen ta sun gyara mata dakin ta sosai an mata kayan daki masu kyaw da tsada , suna zaman su cikin aminci da girmama juna da soyaya sai dai matsalar Hafsat ragguwa ce batada kokari ta saba a gida komi se an mata shiyasa ta roki mijin ta a kan daukar mata yar aiki da kyar ya amince ya daukar mata ita sai dai tana yawan samun matsala da su wasu ai tace way basuda tsafta wasu kuma sabani suke samu se su bar aiki , tayi yan aiki diyawa har Allah ya kawo mata inna suwaiba wadda itace ta jima tana masu aiki a duk cikin masu aikin ta babu wace tayi jimawar ta .Hafsat tanada y'ay'a biyu Iman 6years da Muslim 4 years, bayan Hafsat ta haifi Iman taso suje asibiti ayi mata planning amma Habib ya nuna mata shi fah y'ay'a yake so in bata so toh gaskia sai dai ya auro wacce zata haife mashi yara abinda yasa ta hakura kenan batayi planning ba shiyasa diyanta basuda wata tazara tsakanin su
A bangaren aikin ta kuma bayan sunyi aure ya murza ma idon shi toka akan lalle ita bazatayi aiki ba saboda bayason matar shi tana zuwa aiki , saida aka kai ruwa rana sanan ya amince mata , yanzu haka malamar makaranta ce tana koyarwa a wata a CEG Ali dan tsofo dake can wajen unervesity akan abinda ya shafi science .
Sunada 3years da aure ya kaita hajji, a lokacin ne kuma kuri da iyayi ya karu sai aka koma Hajiya Hafsat kuma gashi hada mota gareta kasancewar shi me hali, Hafsat akwai kuri, tana son ace ita wata ce bata harka da kananan mutane ko dan tana diyar professer ce , hajiya Hafsat kenan👌🏻*Bari muji Habib shima wanene shi ?*
Habib Alhaji Isufu shine cikaken sunan shi haifafen garin maradi ne mahaifiyar shi Hajiya maria da mahaifin shi Alhaji Isufu dan canji ne suma yan asalin garin maradi ne katsinawa ne gaba da gaba suna zaune a unguwar burja , sana'ar mahaifin shi canji shiyasa duk yan gidan su suna canji koda kana aikin gwamnati toh kana canji a lokacin da babu aiki se kayi kasuwar ka,
Habib shima yayi karatun boko tinda har jami'a yayi bayan ya gama ne bai samu aikin ba kawai sai ya fada a harkar canji kasancewar tin yana karatu yake zuwa kasuwa yana ganin yadda ake harka ,sannu sannu se ya fara samun nashi na kan shi a lokacin ne kuma Allah ya hada shi da Hafsat sukayi auren su na so da kauna, bayan auren su da shekara guda lokacin an haifi Iman ne ya tafi hajji shima ( Allah Ya kaimu makka mu ma🙏🙏🙏)Habib yana da sha'awar yin mace sama da guda, tin kafin ya auri Hafsat sai dai be taba fada mata gudun abinda zai hada su da uwar gida shi amma yanzu inaga alamar ya kusa fasa kwai tin lokacin da ya ga yar yarinya Samira kenan sweet 16 ya birkice ( tirkashi 😳) mu dai kallon ne namu Habib ka bi dai a sannu.
*cigaban labari*
Samira ce kwance suna hira itada innar ta iren ta uwa da y'a, can se naga Samira ta tashi zaune tace
"wlh inna ina son zuwa garin tawa yawshe rabon da inga yan uwan babana , wlh ina son ganin dangina duk da su basu nema na"
inna suwaiba tace "inshah Allah in na kara jin sauki zan kaiki har garin su "
Samira tace "Allah ya kara lfy inna ta "
Inna suwaiba tace "ameen sha lele na"
daga nan se suka canza hira su.
Washhhhhh nagaji 😔😔😔😔
Masu comment kun fi kowa birge ni , ku karanta ku bani comment ,
kuma fah readers se kunyi hakuri da yadda littafin nan ze tafya amma nasan in an tafi can can can gaba kowa se yaji dadin shi inshah Allah
har yanzu ba'a kawo wajen wasar ba , amma in kuna biye da ni muna nan tafe ya Yardar Allah🙏
se mun hadu a page ta gaba , yawan comment yawan girman page 💃💃💃💃💃💃💃
![](https://img.wattpad.com/cover/201300946-288-k191998.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomansaSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...