1⃣9⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
Wannan page taki ce kawata Flower🌹🌹, ina yinki sosai
*_Sakon gaisuwa gare ku masoyana😘😘😘😘, masu sharhi ina gaida ku kyawta👌🏻👌🏻👌🏻👌🏻 ina yin ku irin sosai in nan_*
Da yamma bayan sallah isha'i gidan kaka samira na wajen uwa iyayen inna suwaiba kenan , akayi ma malan sallama yayi baki wai suna son magana da shi, shi dai abun ya bashi mamaki kuma ance wai cikin mota suke , yace dai ayi masu iso cikin zaune,
Suna shiga cikin gida bayan sun zaune sai na ga wai ashe Habib ne da Abdulahi suka zo (ko ya fada masu hanyar gidan🤷♀ )
Bayan sun gaggaisa ne malan yace da su bai shaida su ba
Murmushi sukayi sannan Abdulahi ya zayyane mashi abinda ke tafe da su kuma ya kara de cewa
"wlh malan babu yadda banyi da inna ba taki yarda , dan Allah ku sanya baki a maganar nan shiyasa ma nace ma Abokina mu zo nan nasan ku zaku amince da maganar mu"Malan ya kalle su da kyaw yana cewa
"naji abinda ke tafe da ku , kuma inshah Allah nayi ma ita suwaibar magana, ai shi lamarin aure ba haka yake ba , bakasan abinda zai kasance ba, amma kuma tayi gaskiya da tace diaywa zasu ce taci amanar matar ka, amma abu daya zance maka shine kaje kayi istihira , itama zan sa ta tayi ko kuma ita samira tayi da kan ta"
Abdulahi yace
"mun gode malan , Allah ya kara nisan kwana"Malan yace
"amin amin, inshah Allah zan sa ayi mani kiran ita suwaiba dan mu tattauna da ita , dan haka ku kara hakuri , zuwa bayan sati sai ku dawo sannan na gana da ita "Suka amsa da inshh Allahou sannan suka aje mashi jikka goma( 6k) yace sam ba zai amsa ba, da kyar suka samu ya amsa bayan sun sha fama da shi, sukayi mashi sallama suka tafi suna mai yabawa da karamci irin na malan .
Washe gari da yamma baban inna suwaiba ya aika ayo amshi kiranta kasancewar basuda waya balle ya kira ta ( wa zaya sai masu waya ☎ fans )
Saida gaban inna ya fadi lokacin da dan aike ya zo , ha tana cewa yanzu zata tafya saida d'an aiken yace mata kowa lfy sannan ta yarda tace inshah Allah washegari samako zatayi ,aiko bata fata lokaci ba wajen zuwa kiran malan saboda washegari tare suka fita da samira ita tayi gidan aiki ita kuma inna tayi malan dan jin kiran da ake mata
Tafe suke cikin adedeta sahu tanayi tunanin ko lfy malan yake mata kira , ko dai wani ya rasu, ko kuma wani a baida lfy, gayanan dai tunani kala kala inna keyi ha dan adedeta ya kaita gida, a sauke ta , taga malan kofar gida sannan ta sauke ajiyar zuciya ,tana zuwa ta gaida malan, sannan tayi cikin gida , tana nan zaune malan ya shigo cikin gida suka kara gaisawa har yana tambayar ta yana cewa
"yo suwaiba ya banga amaria ta ba, ai naso ace tare kuka zo da ita dan kusan kiran ma na tane "
Inna suwaiba tace
"kiran ta baba , lfy kuwa"Saida tsoho malam ya murmusa sannan yace
"lfy klw sai alkairi , wani ne yazo nan neman auren ta na yaba dan hankalin shi kuma da nutsuwar shi , shiyasa nace bari ayi mani kiran ki dan in shaida maki "Inna tace
"wani kuma malan , wanene shi"malan yace
"wanda ya tafi gidan ki neman auren ta kika hana shi , shine yaji ba zai iya hakura da ita ba yazo nan gidan"saida gaban inna ya fadi , a zuci tace Habib miyasa kayi mani haka , ai ko nasan tinda ka zo wajen malan dole in yarda da kudirin ka tinda in na ki yarda malan cewa zaiyi na nuna mashi ba ni na haife ta ba , gaskiya *_ban zaci haka ba_* (littafin anty Nasseeba Isma'il uba), ni suwaiba , *ya zanyi*? (naseeba isma'il uba)
malan ne yace mata
" kina jina ko , yanzu abinda za'ayi kije kiyi ma Samira bayani , ki kwantar mata da hankali , kuma kice tayi istihira duk abinda ya kwanta mata a rai sai ta fada maki "inna tace
"to malan na gode Allah kara girma"Malan ya amsa da
"ameen" ya kara da cewa "kuma ya zama dole Samira tabar zuwa aiki a gidan "
inna tace ai inshah Allah tabar ma zuwa daga yaw da yamma in ta tafi dama wata ya kai karshe jiya aka mata albashi"malan yace
"haka yafi ma , kinga amshi jikka biyar cikin cikin goma da suka bani ce, sai ki ja jari kafin mu ga yadda zata kasance"Inna ta amsa tayi godiya daga nan suka dan tafa hira da ita zuwa karfe 12 tayi masu sallama ta tafi gida gudun kar samira ta dawo hankalin ta ya tashi amma da sai ta yini gidan su
Bata ko jima da dawowa ba saiga samira ta dawo daga gidan Alhaji habib wajen aikatau kamar kullum yaw ma da abincin ta , bayan sun gama cin abincin ne inna take cemata da yamma in kin tafi kice masu kin bar aiki
Samira tace da inna
"saboda me inna"Inna tace
"na gama magana da malan da naje can dazu , in kin dawo da yamma zan maki bayani"
Samira ta amsa da tohHakan kuwa akayi da yamma bayan Samira ta gama aikin ta ,tace ma uwar dakin ta ta bar aiki ,
Hafsat ta tambaye ta dalili ita kuma tace sana'a zaku rikayi tareda inna ,
Hafsat ta sallame ta, ita kuma tayi masu bankwana tareda fatan Allah ya sauke ta lfy, Hafsat bata wani damu ba tinda ga Nafisa ta rika yi masu girki tinda yanzu babu laifi ta iya tinda Habib ya gargadeta kullum tareda ita suke girki shiyasa ha ta iya, yanzu ma shiyasa da Samira tace mata tabar aiki bata wani nuna damuwar ta ba tinda ga Nafisa amma dai tayi neman wata y'ar aikin tinda ko yaw aka janye strike Nafisa zata koma school kenan itace zatayi aikin gida, tace bari Habib ya dawo muji yadda za'ayi.
______¥_¥_¥_¥_¥________
Da dare zaune suke a dinning zasu fara cin abinci , kafin a zuba masu ne Hafsat take fada ma mijin ta cewa samira tace barin aiki zatayi a gidan su wai har ma tayi masu bankwana bazata kara dawowa ba , take gaban Habib ya bada rassss rassss
Da sauri yace
"soboda mi, ko wani laifi akayi mata"Hafsat ta yamutsa fuska 🙁 irin bata son maganar nan tace
"laifin mi za'ayi mata kuma , kawai dai cewa tayi wai sana'a zasu farawa ita da uwar ta , taje suyi ta sana'ar su , suka sani" ta ida maganar tana saving in su abinci
Shi kuwa gogan na ku yana can ya fada duniyar tunani, take maganar da Abdulahi yace mashi inna tace ta fado mashi a rai ,
_in kuka cigaba da tada maganar nan samira zata bar aiki a gidan_
Kenan inna bazata bashi samira ba, ya zama dole in sun gama cin abinci ya tafi gidan inna dan jin ba'asin barin aikin SamiraMon coeur (my heart) tunanin mi kakeyi haka ina ta maka magana bakaji na
Maganar Hafsat ta daki dodon kunnen shi tana cewa
"tin dazu inata magana kana ta tunani"
Habib yace da ita
"babu komi wani abu ne na tuna"
Hafsat tace
"ok bismillah"
Daga nan suka fara cin abinci, shi fah Habib yaw taunar abinci ne yakeyi yaw ko dadin shi bayaji (abincin samira ne ba dadi🙆)Bayan sun gama cin abinci Habib yace ma Hafsat
" mon amour (my love) bari in dan fita nan in dawo "
Hafsat tace mon coeur(my heart) ina zaka cikin daren nan karfe 9 fah tayi"yace da ita
"kar kiji komi matata yanzu nan zan dawo ba wani jimawa zaniyi ba"Ba dan ran ta ya so ba ta amsa da
"Allah ya kiyaye hanya, please kar ka dawo "
shi kuma yayi mata sallam ya fita ,
Aiko bai tsaya ko ina sai gidan inna suwaiba._____¥_¥_¥_¥_¥_¥_¥____
Acan kuwa gidan inna suwaiba bayan Sallah isha'i ne inna ke fada mata dalilin tana cewa ta bar zuwa aiki , saida Samira ta zabura tace
"Haba inna yanzu kema kina goyan baya in auri Alhaji "inna tace
"ba haka bane diyata kin san babu mai ja da ikon Allah, tin satin biyu da suka wuce lokacin sukazo nan shida abokin shi maganar ce ta kawo su , na nuna mashi ban amince amma sai ya kewaye gidan malan ya fada mashi bukatar shi, shine malan yace kin bar zuwa aiki gidan shi , sannan kuma kiyi istihira"kafin samira tace wani abu sai mukaji sallamar yaro a bangaren mu
*mu hadu da dare in Allah ya kaimu*
_*Ina alfahari da ku masoyana ,Hauwa J, ummu shafa'at, Dr ummiey boko, mmn bodo , Hafsat Ahmad, Hadiza Idi, Mom Kaleed*_
*GOOD AFTER NOON ALL*
*BON APRÈS MIDI A TOUS**💞NANA AISHA💞* ce
YOU ARE READING
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomanceSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...