page 20

494 33 0
                                    

2⃣0⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

*_Wannan page tawa ce ni kadai 💞Nana Aicha💞_*





Habib ne yake neman a mashi iso cikin gidan , aiko yana shigowa samira ta tashi tayi daki tana mai zubda hawaye , ya bita da kallo cike da tausayawa ko ba'a fada ba yasan inna ta fada mata yana sonta saboda a yanayin da ya ganta,

Cike da da girmamawa Habib ya gaida inna kamar yadda ya saba, bayan sun gaisa ne yake tambayar ta miyasa Samira zata bar zuwa aiki,

Inna ta kalle shi cike da natsuwa tana cewa
"malan baba ne yace ta bar zuwa aikin kuma nima na diba na ga dacewar haka saboda kar matar ka ta gane abinda ke ran ka game da ita azo a samu matsala gwara tin wiri ta dauke kafa daga gidan ka"

Habib yace
"hakane inna , nagode sosai"

Inna tace
"tinda ka mani gami da malan a shikenan amma gaskiya sai na sanya tayi istihira sanan kaima sai kayi taka saboda neman zabin Allah,"

Habib yace
" hakane inna inshah Allah zanyi cikin satin nan "
inna tace
"Da kyaw  a gaida gida"

Habib yayi ta zabgawa inna godiya ya tashi ya tafi yana cewa zai dawo bayan kwana biyu, ya shigo da damuwa ya fita da fara'a a fuskar shi , yana fita ya biya wajen mai balangu ya saye tareda yagourt yayi gida abun shi .

Bayan Habib ya fita inna ta kira samira tayi mata nasiha mai ratsa jiki ,ta kara da cewa
"yanzu abinda za'ayi gobe kiyi istihira, kinji duk abinda ya kwanta maki a rai sai ki fada mani kinji diyata, Allah ya maki albarka"
A sayyaye Samira ta amsa da amin

daga nan sukayi shirin su na bacci kamar yadda suka saba ,
washe gari sukuku samira ta tashi daga bacci,  inna ta koya ma Samira yadda zatayin istihira aiko ba bata lokaci tayi ta rannan , itama inna ta dage da adu'a ba dare ba rana🙏.

___¥_¥_¥_¥_¥_¥_¥_¥_¥__

Habib yaji shiru har yanzu iyayen shi basu tuntube shi ba tin randa akace ya dawo shine yace yaw ko in ya tafi sai yayi maganar samira.

su kuma a bangaren iyayen Habib sunyi shiru da maganar ne saboda suna tausayin Hafsat ga ciki an kusa haihuwa kuma suna tsoron a fito da maganar a fili wani yaji ya fada mata azo ta samu matsala ko kuma abun cikin ta ya samu matsala (surukan kwarai kenan👍🏻👍🏻) , shiyasa sukace daga ta haihu sai suje nema mashi auren ta, shi kuma ya gaji da jira shine yace yaw in ya tafi gaida su sai yayi maganar.

bayan sun gaisa da baba da Hajiyar su ne yay shiru yana jiran ko sun ce mashi wani abu , su kuma duka sun gane abinda ke tafe sa shi amma sai babu wanda ya mash zancen, ganin babu wanda keda niyar mashi maganar cikin su sai yace da su
"dama game da maganar da na maku kwanaki ne"

hajiya tace
"ai fah dad'a ka fara , haka kayi lokacin da zaka auran Hafsat saida aka kai kudi sannan muka huta , yanzu ma in ba kudin aka kai ba bamuda zaman lfy"
murmushi Alhaji yayi yace da shi
"sai bayan matar ka ta haihu zamu kai kudi mun rigada mun gama magana da maman ku"

godiya yayi masu sannan yayi masu sallama ya tafi gida yana mai jin dadin yadda iyayen shi suka karrama matar , gaskiya dun kurin ta da jiji da kai in ta tanq girmama iyayen shi , matsalar ta guda raggaci da komi sai an mata , amma kuma ai dama ko ba ragguwa ce ba dama zan kara aure tinda inada ra'ayin yin mace sama da guda , a fili ya furta
"na kusa fara zuwa zance ashe "

_______¥¥¥¥¥¥¥¥_______

Tin randa Samira  tabar zuwa aikatau inna ta sanyata a islamiyar dake unguwar su , tana zuwa da safe da yamma,  kuma inna kayan miya take saidawa cikin gida ba laifi ana samun cikini , da shi sukaci suke sha yanzu , kuma Habib da yazo hira ya kawo masu buhun shinkafa.

*Bayan sati uku*

Samira maganar Habib ta kwanta mata a rai kuma ta fada ma inna ita ma ta fada ma malan baba yace to yanzu iyayen Habib kawai suke jira su kawo sadaki , kuma malan baba yace dole sai can wajen dangin uban ta za'a kai kudin aure tinda sune masu bada auren ta

kuma a wannan lokacin ne cikin Hafsat ya shiga wata tara cif haihuwa yaw ko gobe.

Habib ya fara zuwa zance wajen Samira
duk da har yanzu bata fara sakewa da shi ba, gani take ta ci amanar Hafsat na auren mijin ta, duk da maganar arziki bata taba hada su ba amma ai babu dadi ta auri mijin ta alhali tayi zama y'ar aikin ta , amma duk da haka tana jin son auren a ran ta .
tin randa ya fara zuwa zance ya kawo mata waya android  mai kyaw kirar Tecno L8 Lite , ya koya ta mata yadda ake anfani da ita dayake tayi school ha ta iya

_____¥_¥_¥_¥_____

*Gidan Alhaji Habib Alhaji Isufu*

Misalin karfe 9 na dare su Iman suna can tareda  Nafisa suna karatu , su kuma masu gidan suna palour zaune saman kujera mai zaman mutum 3 , suna hira ita shi duk da maganar ma wahala takeyi mata kasancewar yaw batajin dadin jikin ta tin safe kawai karfin hali ne takeyi , Habib ya lura batajin dadi amma sai tace mashi ba nakuda takeyi ba kawai dan dai watan haihuwa ne shiyasa yake mata haka , ita kuma bata son zuwa asibiti su jima in nan tafi son har abun yazo ya kusa tinda tayi haihuwa biyu tasan ya haihuwa take, kawai wannan cikin ne dai da yayi mata girma sosai.

Habib ne yace da ita
"my love ki tashi mu tafi asibiti please, ko so kike ki haihu gida"

da kyar dai ta yarda suka shiga mota sai asibiti .
aiko nakuda kamar kamar jira take suzo asibiti, suna zuwa ta taso mata gadan gadan sai labour room akayi da ita, basu fi awa guda da zuwa ba Allah ya sauke ta lfy ta haifo yan biyu mace da namiji.
bayan an kimtsa ta ne aka kaita dakin hutu , aka sanya mata karin ruwa aiko take sai baccin gajiya ya kwashe ta,

Aiko Habib kamar yayi tsalle haka yakeji ,take ya lalibi wayar shi ya kira mutanan arziki ya shaida masu haihuwar mata shi , mamar Hafsa ko ana kiran ta sai gasu tafe cikin daren itada wata mata wadda ban san ko wacece ba , lokacin da sukazo hafsat bata tashi daga bacci ba , sun dan jima zaune sannan ta tashi ,

lokacin da Habib ya kira Samira cikin daren saida gaban ta ya fadi kasancewar basuyin wayar dare da ita saboda yana girmama matar shi , ba zai so ba dan zaya kara aure ba ya wulankanta ta ba shiyasa daga ya shigo gida to babu waya sai in dai fita waje zaiyi ya kira ta .

Shiyasa yanzu da taji kiran shi cikin dare tace ko lfy , tana dauka bayan ta gaida shi yake fada mata Hafsat ta haihu kuma yan biyu ne aka samu ,aiko samira ta nuna farincikin ta , taan mai son yan biyu sosai kamar tayi tsuntsuwa taje ta ga yaran,  tayi mashi barka sannan sukayi sallama , inna da itama karar wayar ya tada ta daga bacci samira ta fada mata an ma Habib haihuwar yan biyu mace da namiji.
Inna tayi masu adu'a Allah ya raya kan sunna ta kara da cewa
" in an sako su daga asibiti sai mu tafi mu ga yara ko"
Samira tace
" ni gaskiya inna kunya nakeji"

Inna tace
"tafya kam dole muje tare da ke gobe goben"

ita dai samira shiru tayi daga nan suka koma baccin su

Washegari da safe aka sallamo Hafsat daga asibiti saboda batada wata matsala , aiko suna zuwa gida sai ga yan barka , wasu na shiga wasu na fita kunsan dama yan biyu da farin jini ,



_*dama nace in banji sharhi ba dan mitsitsi zanyi , kuma da rana banjin sharhi ba shiyasa nayi kadan, yanzu in naji sharhi inshah Allah gobe sai na maku page mai tsawo*_

*GOOD NIGHT AND SWEET DREAM*
*BONNE NUIT ET DOUX REVES*


_*INA SONKU MASOYANA A DUK INDA KUKE, MASU SHARHI NA GAIDA KU KYAWTA*_

Mu hadu a gobe idan Allah ya kaimu

*💞Nan Aicha💞 ce*

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang