*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
2⃣7⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
Dama sunyi da angaye in sunzo daukar abinci , su biyo da motar da zata kai su wanka amaria, gidan kanwar inna suwaiba ne akeyin shi, tare suka koma da su aka kai su gidan wanka amaria dake unguwar sabon gari, mota biyu ta dauke su saboda yanzu su 8 ne saboda salima ta biyo su ,
Bayan sun isa gidan da za'a wanka amaria suka tarda har an kawo iyaye mata kasancewar can gidan inna ma Habib ya aika motoci su dauko matan da zasu tafya wajen wanka amaria ana la'asar aka dauko su shiyasa suka riga su samira isowa, da suka zo aka zuba masu abinci sukaci sannan aka basu ruwan gumba sunji sugar da kayan kamshi.
Da za'ayin wanka aka tarara ruwan lalle cikin bawon wanka sannan aka kai mata toilet sai aka zuba mata wasu ruwan da zata dauraye jikin ta sannan su gwaggo da kuma wata y'ar uwar inna sukace zasu yi mata wanka , kememe taki yarda sai bar mata sukayi tayi da kanta, bayan ta gama wanka sukayi haramar zuwa gida ,
Dama motocin da suka kawo su basu tafi ba su suka maida su gida,
*A gurgije*
Washegari da safe gidan su zainab akayi kumshi ,yayar ta ce ta dauki kumshi na 2, suma sunyi ma angaye hidima ba laifi , koda aka gama aka kira su suka zo suka dauki abincin su suka ba uwar kumshi kudin ta , sannan suka bada chewing-gum acewar su jiya cikin mota suka mance ta basa basu ba, shine suka basu ita yaw.
Itadai amaria tana can ana mata gyaran jikin ta , sai kankana da rakke take sha, kuma naga maman zainab ta bata wani abu cikin kofi akace ta shanye shi tas, Maman zainab tana ta bata hadi na musaman tana sha, tana gyara ta ba laifi ,
Bayan angaye sun tafi sauran yan mata suka tafi gida ita kuma amaria tareda offial marcy da zainab aka barsu gidan su zainab in tinda gyara jiki ake yiwa samira kumas su saida magriba zasu tahowa gida.washegari tinda safe mai kitso tazo har gida tayi mata shi kanana ne sosai, gaskiya ya kitso kamar wanda za'a sancewa da allura, ana kusa gamawa kuma sai ga mai lalle itama tazo sai bayan la'asar sannan aka gama shi, ta gaji da zama sosai duwawu 🤭duk sunyi mata ciwo kasancewar ta yini zaune,
Ana gamawa kuma sukayi haramar zuwa kauyawa day, duk sunyi shirin su irin na mutanen kauye , riga dan , zani daban, dan kwali daban, fuskar nan an mata kwalliyar duk an sa kwali ko ina, da kunga zanen official marcy kamar zata tsallaka wuta, ita kuma salima abunka da farar mace sai ko kwaliyyar tayi mata kyaw🤭, dayake cikin kwanar layin su ne , da kafa ma suka taka , aiko suna zuwa aka sanya kidar yan kauye , zainab ta shiga sai taka rawa takeyi tana girgiza kugu, itama official ai ta gudu ta fada hili, daga nan sai sauran yan mata sukayi ta shiga suna cashewar su ita dai amaria tana zaune nata ido 👀 ne , ta matsu ma a koma gida ta huta, bayan sun fita daga filin sai naga ana raba rakke , suna sha suna rawa , nace yan matan amaria ba dama , anata daukar selfie , wasu ashe hada tulu suka zo , wasu kuma da kullin kayan cikin zane , ni saida ma suna daukar hoto ne na lura , ana fara kiran sallah suka tsaida kidansu, mashah Allah, Alhamdulillah taro ya tashi lfy,
tin suna can wajen partyn kauyawar su, suke ganin alamar hadari ya kusa tasowa , aiko ana ida sallah magriba sai ga ruwa shaaaaaa , an dan jima haka kamar 30 min anayin su sannan suka dauke, bayan sunyi sallah isha'i Abdulahi ya kira zainab yana shaida mata zasu zo zaman lalle da dare, daga nan sukayi shirin su , wajen karfe tara sai ga angaye tafe gidan su zainab, dayake can za'a daura aure shuiyasa ana sallah suka tafi can , koda su Habib suka zo sai suka biyo da kujerun da za'a zaunawa , suma su zainab da zasu fito sai suka biyo da chewing-gum inda aka kawo masu , zaune suke ko ina ana hira ko ina kujera biyu saurayi da budurwa sun dan rabbabu, shi kuma Habib shida samira shi, nima yaw tsayawa nayi saida nayi hira, sune basu tashi ba sai 12 na dare

ŞİMDİ OKUDUĞUN
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomantizmSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...