1⃣8⃣
~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)*NANA AICHA* ce
Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*
*Sakon gaisuwa gareku masoyana 😘😘😘*
Wannan page taki ce ke kadai kawata *Maryam Abdoulrahaman* Mamy blew💙 kiyi yadda kike so da ita , ina yin ki irin sosai in nan 💕💕, much love you dear💞💞💞
"Baba so nake kuje ku nema mani aure "
:Aure kuma , mi matarka tayi maka da zaka mata kishiya "
maganar Hajiyar ta daki dodan kunnan shi da shigowar ta kenan sashen baban na su
Alhaji yace da shi
"a ina iyayen yarinyar suke"
Habib yace
"baban ta ya rasu dangin su suna garin tawa ,sai dangin uwar ta ne ke nan cikin garin"
Hajiya tace
"ya ina magana kun kyele ni kai da d'an ka"
Tayi maganar tana zama kusa ga baban su
Alhaji yace
"lokacin da na maki kishiya ke wani laifi kikayi mani, dan d'a na zai kara aure shine zaki cemashi haka, kiyi adu'a Allah baki suruka ta kwarai, kuma kinsan ba tin yaw Habib yake cewa shi sai yayi mata 4 , ko ni da ke baban shi 2 ne nayi amma shi har 4"
Hajiyar su tace to wai a ina ka samu mata ne
Habib ya kara sunkuyarda da kan shi yana cewa
"diyar inna suwaiba Samira, wace tayi mani"
Hajiya tace
"anya kuwa Habib kayi ma Hafsat adalci kuwa ?, ka duba ka gani wajen 2 years da wani abu yarinyar nan take mata aiki amma kuma ka rasa wace zaka mata kishiya da ita sai ita, gaskiya Alhaji ka bar biye mashi a kan wannan lamarin, ko yaje ya sake wata mata ko kuma a fasa auren"
Habib yace
"haba hajiya ta"
Alhaji yace
" tashi ka tafi har muyi shawara da mama ka, ne neme ka"Sum sum Habib ya tashi ya tafi ,yana adu'a Allah ya sa hajiyar sa ta amince
Habib na fita Hajiya ta kalle shi tana cewa
"Baban su ka kalli lamarin nan bai kamata Habib ya auri y'ar aikin shi , baiyi ma Hafsat adalci ba gaskiya , ni dai ban goyi bayan shi"
ta ida maganar tana daure fuska irin wannan ba wasa😎Saida Alhaji ya murmusa sannan yace da ita
"Haba uwar gida na miye na hada fuska kuma, aure ne dai d'an ki yake so yayi , ki mashi adu'a Allah ya tabbatar da alkairi"
Hajiya tace
"shikenan Allah ya kyawta, kuma ya tabbabatar da alkairi"
Alhaji yace
"haka nake so kice madam"
daga nan suka taba hira suna tattaunawa yadda abun zai kasanceA bangaren Habib kuwa yana fita daga dakin baban su saida ya dan jima cikin mota yana tunanin duniya , kar azo hajiyar su ta hana shi auren Samira , kuma ai shi yanada ra'ayin yin mata sama da daya amma kuma yanzu hajiya tana shirin yi mashi haka sai kace auren farko, gaskiya kar hajiya ta kwafsa mani🙆🙆 , ya dan jima yana tunanin shi sannan ya fita daga gidan bai tsaya ko ina ba sai school in su Iman saboda a lokacin har har karfe biyu ta kusa yi,
yana zuwa bai jima ba aka tashe su , suga ganin baban su suka yo wajen shi , suka shiga mota suka yi gida,zaune suke saman dinning suna cin abincin rana , tin a lomar farko Habib ya san samira ta zo wajen aiki yaw tinda yaji girkin yaw daban yake da na kwana biyu 👍🏻👍🏻, yasan Samira ba baya ba wajen iya girki, gudun zargi sai baice komi ba amma yayi shiru😷, can sai Nafisa tace da yayan ta
"Grand frere (big bro) gida zani komawa yaw tinda mai aikin anty ta dawo , "
Yi yayi kamar bai ji ta ba , ita kuma a bangaren ta ta matsu ta koma gida ko ta huta da aikin da takeyi a gidan nan gaskiya, kullum matar gidan sai son jiki, kasancewar ma tanada ciki ne ma ta ma zo gidan amma ba dan haka ba , da ba abinda zai kawo ta gidan , tinda ta jima da sanin halin matar gidan na son jiki,
Habib yace da ita
"to uwar son jiki , dama na jima da sanin cewa baki son aiki, to dan haka babu inda zaki tafya kina gidan nan sai kin koyi sanwa ko kin bar gidan nan sai an koma school daga strike"
YOU ARE READING
YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)
RomanceSamira yarinya ce y'ar shekara 16, tana aiki gidan Alhaji Habib da Hajiya Hafsat, kasacewar Allah yayi Samira da tsafa dukda basu hali amma kullum tana cikin tsafta, kuma ga uwa uba ta iya girki, yaw da gobe har ta kai Alhaji ya fara son Samira...