*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 29&30
__________📲Hajiya Naila na gama fad'ar haka ta kashe wayarta, Mustapha ya shiga tashin hankali sosai, bin kiran nata yayi wayar na ta ringing amma tak'i d'aga wa, samu yayi ya bar wajen batare da Abida ko Annur sun kula ba.
Sake kiran number yayi sau ba adadi amma tak'i ta dauka, yasan ko sun kub'uta daga hannun ta yanzu akwai babbar matsalar da za su fuskan ta a gidan.
Hajiya Naila ce zaune a falon k'asa ta d'ora k'afa akan center table dake gaban ta wayar ma na kan table d'in sai Shan k'amshi take tana ji kiran Mustapha yana shigowa amma bata da niyyar d'auka.
Anty Hadiza ce ta shigo falon, wajen dinning ta nufa d'auke da warmers a hannunta,
Hajiya tace mata "Idan kin ajje ki zo" "To hajiya" Abinda ta fad'a kenan ta k'ara sa wajen dining d'in cikin sauri ta ajje warmers d'in ta dawo gaban Hajiya tace "gani".
Cikin shan k'amshi da ya zama halinta ta nuna mata wayar da Kira ya sake shigowa tace "d'aga wannan kiran Sai ki saka min ita a handsfree" .
Anty Hadiza ta yi yanda Hajiyar ta umarce ta, daga cikin wayar sai faman magana ake " Hello hajiya don Allah ki saurara ki ji bayanin da zan miki".
Anty Hadiza ta gane Mustapha ne ke magana duk da a waya ne.
Hajiya tace ki ajje min wayar a hannun kujera kusa dani, ki d'auke wannan plate da cups d'in ki maida kitchen.Anty Hadiza "To" tace sannan tayi yanda Hajiyar ta Umarce ta.
"Ina jinka" abinda hajiya Naila ta fad'a kenan kamar ba ita tayi maganar ba, ta maida Idanunta kan tv dake ta faman aiki.Mustapha yace "Hajiya Idan ki ka duba wayarki nayi miki missed call ya kai guda hud'u naga baki d'aga ba Sai nayi miki message in kika duba zaki gani".
Abokin Annur ne tun na primary, yake a k'asar waje shine yanzu ya shigo Nigeria kuma ya Kira Annur yace shi yake so ya zo d'aukar sa sun dad'e basu had'u ba.
Hajiya ki daina sa shakka akai na kaf gidan nan kece me tabbas, babu Wanda zan yi wa aiki sai ke gamawa da Annur ba wani abu bane a waje na lokaci dai muke jira.
Plate da cups d'in dake hannun Anty Hadiza ta saki koi na a jikinta rawa yake saboda tsananin rudewa, da tayi kuma ta tabbatar da muryar Mustapha ce taji a wayar Hajiya.
*************
Salim na fitowa ya sauke ajiyar zuciya tare da d'aga hannu sama yace "Ya Allah ka shiryar da mahaifiya ta, Allah ka bata ikon gane gaskiya da aiki da ita", lifan d'in sa ya d'auka ya fita daga gidan."Ki nutsu Humaira shine wa?" cewar minista da shima ya tashi tsaye, Humaira ta sake cewa shine wanda zuciya ta ke so dad ka taimaka min"
Umar dake tsaye cike da mamakin nuna sa da Humaira tayi Kuma bai fahimci komai ba, yace "wai me ke faruwa ne", malam ne yayi gyaran murya yace"ku zauna Sai ayi maganar a nutse".
Ba musu duk suka zauna, Malam ne ya kalli Humaira yace "Idan na fahimce ki wannan shine yaron da kike so ba tare da kin San shi ba"
Humaira tace "eh shine rayuwa ta malam" cewar Humaira, zunbur Umar ya mik'e yace " Aiko Sai dai ki mutu don ni Rayuwar wata ce, ba zai tab'a faruwa ba nima Abida ce Rayuwa ta tun wuri ki chanja tsari"