page 63&64

10 1 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

      Page 63&64

__________📲Agogon dake d'aure a hannunsa ya duba yaga ya shafe awa d'aya har da mintuna yana neman ta amma shiru, komawa yayi ya bud'e motar sa ya zauna ya jingina da kujera ya rufe idanunsa, in banda ciwo ba abinda kansa ke yi.

K'aramar k'ofar gate d'in Abida tayi knocking mai gadi ya lek'o ya ganta sannan ya bud'e mata.

Direct b'angaren su Anty Hadiza ta nufa, sallama tayi a bakin k'ofa aka amsa mata tare da bata izinin shiga.

Fadila ta tarar a zaune tana danna wayarta, zama tayi a kusa da ita sannan tace "Ina Anty Hadiza".

Fadila tace "Ta shiga makwabtan gidan nan barka".

Abida tace "Dama wajenki na zo" .

Fadila ta juyo tace "Ina sauraren ki Allah ya sa dai lafiya".

"D'azu mun fita da Annur sai  yaje ya saida wayarshi, Kuma na san ba komai bane matsala ce ta abinci da muke fama, to gaskiya bana so yayi asarar wannan wayar shine ba tare da ya sani ba na tafi banki, na kusa awa kafin layi yazo kaina, amma kin san abin takaicin, ana zuwa kaina suka ce dole sai na bada id card, ko katin d'an k'asa ni kuma bani da komai, shine nazo dan Allah ki taimaka ki amso min kud'in, a Bankin"

Fadila tace "Ai sunan ki ne a jiki babu yanda za'ai su bani".

"Aa mama bata sa suna ba, nima ban Sa ba" cewar Abida.

Fadila tace "Annur yana can hankalinsa ya tashi sosai a muryarsa na gane d'azu da ya min waya yana nemanki"

Dan akwatin sark'a Fadila ta d'auko ta mik'awa Abida sannan ta cigaba da maganarta "Ki sauri kije kasuwa ki saida sark'ar nan, ni Kuma zan je bankin yanzu in kin dawo mun had'u".

"Aa Fadila kar ki saida gold din ki mai daraja tunda ga kud'i an samu kawai ki amso mana sai na jira ki" cewar Abida.

"Kar ki min musu nima umarni nake bi Mustapha yace na sayar na ba Annur kud'in, bayan tafiyar shi akai freezing account d'in shi, da ya je can ya samu labarin anyi freezing duka account Wanda ya ba Annur cards shima ba shi da wata mafita don haka ki amsa".

Amsa tayi tare da fad'in "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gare mu".

"Amin ya Allah" cewar Fadila.

Kasuwa taje shagon da ake saida  gold dubu d'ari biyar da saba'in aka saya Bata wani sha wahala ba dalilin receipt da ta basu na gold d'in".

Komawa tayi shagon da suka je da Annur, motar shi ta hango a inda suka yi parking har lokacin tana wajen haka nan ta tsinci kanta da fad'uwar gaba.

Cikin shagon ta shiga, idanunta akan wayar Annur suka sauka.

Ciniki sukayi ta basu har da ribar ta amso wayar ta fito, tsaye tayi a bakin shagon tana fargabar had'uwa da Annur.

           ***************

"Daddy tunda na zo k'asar nan bamu samu chance d'in da zamu gaisa ba".

Daddy yace "Ba komai son Amma ban so zuwanka wajen nan ba akwai had'ari sosai".

"Insha Allah Daddy  tunda har suka yi kuskuren na gano inda kake zaman ka anan ya yanke" cewar Mustapha.

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now