*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 23&24
__________📲Yana fad'in haka yayi tafiyar sa, baki bud'e take bin sa da kallo cikin mamaki, ta d'au lokaci a haka sannan hankalin ta ya dawo gareta, gani tayi teacher Ahmad baya wajen.Hangoshi tayi har ya kusa gate, da sauri tabi bayansa tana kiransa.
Annur dake tsaye a balcony har lokacin yana kallon duk abinda ke faruwa kuma yanayin nayi masa dad'i murmushi yake ta saki wanda shi kansa bai San dalili ba.
Teacher Ahmad tsayawa yayi a Dai-dai gate ganin Abidar ta biyo shi, tambayar shi tayi dalilin tafiyar sa ba tare da sunyi sallama ba hasali ma basu gama magana ba.
Teacher Ahmad ne ya sauke Ajiyar zuciya sannan yace "Ni musulmi ne nasan haramcin nema akan nema, sannan ina ta miki magana don inji k'arin bayani daga gareki sai naga sam hankalin ki baya tare dani"
Dan Allah kayi hak'uri mamaki ne ya cika ni, shi ma aiki yake a gidannan, direba ne kuma tunda muke tare da shi cikin gidan nan bai tab'a cewa yana so na ba,sannan bai tab'a zuwa gidan mu ba dan haka abinda ya fad'a d'azu ban san da shi ba.
Teacher Ahmad nutsuwa yayi yana kallonta na d'an lokaci sannan yayi murmushi tare da fad'in "Kenan ni mai sa'a ne, daga zuwa na har na samu karb'uwa"
Abida tace "Ba haka nake nufi ba na fad'a maka ne kar kayi tunanin da maganar wani akai na nake kula ka"
"To ni yanzu mene ra'ayin ki a kaina?"cewar teacher Ahmad, "Zanyi tunani akai" " Zuwa yaushe?" "Jibi ma idan Allah ya kaimu" teacher Ahmad yace "Ta yimin nisa, sai dai ko zuwa gobe" "To ba damuwa Allah ya kaimu goben" cewar "Amin" ya fad'a tare da mik'a mata wayar shi, "Amshi ki samin number ki" "bani da waya" ta fad'a kai tsaye " "Ba damuwa gobe Insha Allah zan dawo misalin k'arfe hud'u na yamma ki koma ciki kar a nemeki" godiya tayi masa suka yi sallama ya tafi cikin takunta na nutsuwa ta yi hanyar cikin gida.
Tunani ya cika ta akan abinda Mustapha yayi mata, ta sa a ranta gobe da Annur ya gama jarrabawa sun dawo gida zata tsare shi ya fad'a mata dalili.
Har ta kusa zuwa main entrance na falon gidan ta dag'a kai ta kalli balkony Dai-dai saitin d'akin Annur.
Ganinshi tayi ya kafe ta da Idanu da gani ransa a b'ace yake da sauri ta shige falon, direct stairs ta soma hawa cikin sauri tana so taje ta ji ko me ke damunsa ta ganshi a wannan yanayin ta San ba k'aramin abu ne zai b'ata masa rai har haka.
Tura k'ofar tayi ta shiga d'auke da sallama a bakin ta, shiru d'akin ba kowa, hanyar balcony ta nufa kai tsaye dan ta san yana wajen.
Kafin ta k'arasa suka had'u a hanya wuce ta yayi tabi bayansa suka koma dakin.
Study area ya nufa sai da ya zauna ya kafe ta da idanunsa na d'an lokaci sannan yace "lafiya".
Wani al'amari da bai tab'a samunta ba shine ya ziyarce ta, take taji yayi mata kwarjini, cikin sarkewar magana tace "Ba komai na zo ne inji ko kana buk'atar wani abun".
Bana buk'atar komai har ta tafi taji yace "Ninah baku dace da juna ba, ki gaggawar fad'a masa ke Matar wani ce"
Bata san lokacin da tace "Dan Allah na tambaye ka, bata bari yayi magana ba ta cigaba da cewa ni d'in da wa na dace"