page 73&74

12 0 0
                                    

*MATAR DA ZAN AURA*
    BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

     Page 73&74

__________📲Bayanta Fadila ta bi suna shiga cikin falo ta nemi waje ta zauna.

Cike da b'acin rai Fadila tace "Malama kina hauka  ne zaki shigo gidan mutane kai tsaye ba tare da izini ba.

"Ki gyara kalaman ki, Barrister Hibbah sunana, sannan ba wajen ki na zo ba kin gane" Hibbah ta k'arasa maganar ta cike da isa.

Fadila zata sake magana ta ji maganar Annur a bayanta.

"Bak'uwa ta ce" abinda ya fad'a kenan ya k'araso cikin falon duk da shima sosai yake mamakin yanda akai ta san gidan.

"Barkanki da zuwa Barrister" wani irin dad'i da farin ciki ne suka ziyar  ci Hibbah sam bata yi tunanin samun tar ba ba.

Fari tayi da Idanunta irin na cikakkun 'yan boko wayayyu sannan tace "Na sameka lafiya".

Abida dake tsaye Ido fal da hawaye ya kalla hankalinsa ya tashi amma ya shanye yace "lafiya".

"Am dama girki nayi maka na ce bari na zo na kawo maka" cewar Hibbah.

"Naji dad'i sosai, nagode"  cewar Annur.

Cike da mamaki Abida da Fadila ke kallonshi yayin da Hibbah ma Mamakinshi take.

"Tell me you are not using me, ni barrister ce ina fahimtar mutane" Hibbah ta fad'a cike da rauni a muryarta.

"Why will I, da muka had'u ban fahimce ki bane amma yanzu na fahimce ki" Annur ya fad'a cikin juriya don ya san  yau sai Allah ya b'ata ran Ninarsa.

"Sweet Ina ne kitchen zan d'auko plate na zuba maka na fi son kaci da zafinsa" Cewar Hibbah.

Fadila ta waro Idanu cike da mamaki tana jiran taji me Annur zai ce, Abida ko tuni hawaye sun zubo mata ta goge wasu sun sake tahowa.

Hankalin Annur a tashe yake sosai ita ko Hibbah basa gabanta bata san ma abinda ke faruwa ba.

"Tashi muje park sai mu ci abincin a can" cewar Annur.

"Ok sweet hakan ma ya fi saboda  privacy" tashi tayi ta d'auki basket d'in abincin.

Annur yace "d'auki jakar ki a motar ki zamu tafi".

"Wow naji dad'i  zaka hau tuk'ina" Cewar Hibbah cike da farin ciki.

Abida d'akin su ta nufa da saurin ta, Fadila ma tab'e baki tayi ta bi bayan Abida.

Annur bin su yayi da kallo cike da fargabar rigimar da zata biyo baya.

"Sweet wannan k'annan naka basu da mutunci naga ma kamar basu sona anya ko su d'in blood ne ko dai cousins d'inka ne" Hibbah ta k'arasa maganar tana kallon Annur.

"Idan mun je can zan fad'a miki komai.

Hibbah na fita gate Annur yayi tsaye jikin gate yace "Allah ya tsare hanya idan nace ki tafi ba zaki tafi ba shine dalilin da yasa sa nayi hakan.

Biyun nan da kike gani d'aya matata ce d'ayar Kuma sister ta ce dan Allah ki daina zuwa kar ki had'a min fitina a cikin gida".

Rufe k'ofar yayi ya bar ta a tsaye.

"Wallahi Annur baka Isa ba dole ne ka so ni ba abinda ya dame ni da wata matarka" tana surutu tana goge hawaye har ta k'arasa bakin motar ta.

Tana shiga gida ta fad'a kan cinyar kakar ta ta fashe da kuka.

MATAR DA ZAN AURAWhere stories live. Discover now