*MATAR DA ZAN AURA*
BY NAFSAL KZ
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_Visit to Our Page-https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap
Wattpad https://my.w.tt/RXazzM0MY7
Youtube https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ
Page 81&82
Finale episode
K'arshe..........__________📲Hajjo tace "Na gama magana a taron nan ga 'yan mata da samari nan Ina gani kowa a had'a shi da Wanda ya dace".
"Ke Hibbah taso ki maida ni gida tunda na gama abinda zan yi".
"Ni gaskiya sai dai ki jira dan ni ban gama ba" Cewar Hibbah.
Daddy yace "Ai ba a gama ba sannan ko abinci ba a gabatar ba".
Ba yanda Hajjo ta iya dole ta koma ta zauna.
Daddy ya yi musu bayanin kan halin da ake ciki game da case d'in su accountant wanda an dawo dasu kano, Rabi ma anje kauyen su an taho da ita ya sanar dasu cewar an tura su kotu har ma ya sanar da lawyern sa kuma zuwa sati uku masu zuwa zasu shiga Kotu.
Hibbah tace "Daddy please I really want to participate".
Daddy yace "Lawyer na ya riga da ya fara bincike".
Hibbah tace "please Daddy ka had'a ni dashi na tabbata zan masa amfani".
"To ba damuwa gobe zan kirashi gidan nan sai ku had'u". Cewar Daddy
Bayan sun gama cin abinci Daddy ya umarci Mustapha ya maida Hajjo gida don ta samu ta huta, Abban Hibbah ya ba Mustapha address na gidan.
A hanya Hajjo take ce masa bai yi dacen mata ba ya auri marar kunya amma daganin yarinyar da ta had'asu yanzu daga gidan mutunci ta fito.
"Af na manta kira min number Amadu nawa Baban Hibbah nake nufi ba ubanku ba".
"Bani da number sa" cewar Mustapha dake dariya k'asa k'asa.
"To kira min Amadu uban naku".
Wayar sa da ya jona a motar ya d'auka ya kira Annur, bayan ya d'aga yace "Kai wa Daddy wayar".
Daddy ya mik'awa wayar, yanayin sallama daga can b'angaren Mustapha ya mik'awa Hajjo wayar.
"Amadu wannan d'iyar da tazo kar ku sake ku bari ta tafi ba tare da kun san iyayenta ba na fad'a muku" bata jira amsar shi ba ta mik'awa Mustapha wayar.
Daddy yayi dariya ya kalli Abban Hibbah yace "Babar ka ta cika rigima".
Shima dariyar yayi yace "A haka zamu lallab'a ta mu rabu lafiya".
Bayan an gama cin abincin 'yan matan suka hau gyaran gida da wanke kwanuka yayin da iyaye maza tare da 'yayan suka koma d'aya falon.
Governor yace "Tunda mun samu keb'ewa kowa yazo ya fad'a min buk'atar sa"
Annur yace "Ni so nake a shiga tsakanina da wannan tsohuwar ina son matata kuma ba zan iya had'a mata biyu ba gaskiya".
Daddy yace "Mahaifiyar tawa kake irin wannan batun akan ta, to ka sani maganar ta kamar yankan w'uka ne, dole ce".
Abban Hibbah yace"Kar ka damu babu wanda za'a wa dole, na san yanda zan shawo kan uwata".
Murmushi Mustapha yayi yace "Alhamdulillah".
Daddy yace" Wato so kuke ku bad'a mana k'asa a Ido kenan".
Saif yace "Daddy ni ina son Hibbah".